Shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas ya sanar da cewa suna shirye-shiryen shigar da ƙorafi a Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Kasa da Kasa (ICC) game da kisan gillar da sojojin Isra'ila suka yi wa mai fafutuka 'yar kasashen Amurka da Turkiyya Aysenur Ezgi Eygi.
Abbas ya sanar da mahaifin Ezgi, Mehmet Suat Eygi wannan mataki ta wayar tarho a ranar Asabar. Ya kuma mika ta'aziyyarsa ga jama'ar Turkiyya, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Falasdinu, Wafa ya sanar.
Shugaban na Falasdin ya yaba wa Eygi a matsayin "Jarumar 'yar Falasdin da Turkiyya," wadda 'yan kama wuri zauna na Isra'ila suka yi wa "Kisan gilla". Ya kuma bayyana cewa rawar da ta taka ta zama alamar nuna goyon baya tsakanin jama'ar Turkyya da na Falasdin.
A ranar Asabar 6 ga Satumba ne aka harbi Eygi mai shekaru 26 a ka tare da ji mata mummunan rauni a Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye, inda take aikin sa kai da Kungiyar Kasa da Kasa ta ISM, lokacin da suke zanga-zangar lumana don nuna adawa da mamaye yankunan Falasdinawa ba bisa ka'ida ba.
Abbas ya tabbatar da cewa a yanzu haka shugabancin Falasdinawa na hada kai da mahukuntan Amurka da Turkiyya don neman gudanar da bincie na adalci kan kisan Eygi, kuma za a shigar da kara gaba kotun ICC kan "laifin kisan gilla".
Ya kara da cewa matakinsa na "Ba ta kambin Tauraruwar Birnin Kudus ya zama nuna girmamawa ga sadaukarwar da ta yi ga 'yancin kai da mulkin Falasdinawa." kuma ya gayyaci iyalinta don zuwa Falasdin.
Sojan Isra'ila ne ya harbe ta
An haifi Eygi a Antalya a 1998, kuma sun koma Amurka da iyayenta a tun tana jaririya inda a watan Yuni ta kammala digiri daga Jami'ar Washington, inda ta karanci ilimin sanin halayyar dan adam da yaruka da al'adun Gabas ta Tsakiya.
Ta je Yammacin Kogin Jordan kwanaki kadan kafin ranar da aka harbe ta a matsayin 'yar sa kai tare da ISM, don nuna goyon baya ga manoman Falasdinawa. 'Yar fafutukar kare hakkokin dan adam da ba ta da tsoro, kuma ta kudiri goyon bayan manufofin Falasdinawa.
Ofishin jakadancin Turkiyya a Tel Aviv da karamin ofishin jakadancinta da ke Birnin Kudus ne suka shirya dakko gawar Eygi zuwa Turkiyya. Bayan duba gawar a Izmir, an binne ta a garinsu na Didim da ke lardin Aydin na yammacin Turkiyya.
Eygi ta kasance mai fafutuka da ke aikin sa kai tare da ISM don nuna goyon baya ga Falasdinawa ta hanyar zaman lafiya da lumana inda suke adawa da mamayar da Isra'ila ke yi wa yankunan Falasdinawan.
An bayyana fashewar kokon kai, illatar kwakwalwa da fatar da ta lullube ta a matsayin musabbabin mutuwar Eygi," An kai bawon harsashin da aka samu a kanta dakin bincike don yin gwaje-gwaje. Turkiyya na ci gaba da bincike kan mutuwar ta.
A makon da ya gabata aka fara gwajin farko kan gawar a Cibiyar Kula da LAfiya ta Asibitin Jami'ar Kasa ta Najah da ke Nablus. Sakamakon binciken ya tabbatar da cewa ciwon da Eygi ta samu a kanta sakamakon harbin bindigar ne ya yi sanadiyyar rasa ranta.