Jiragen Turkiyya dauke da kayan agaji ga 'yan Gaza sun sauka a Masar

Jiragen Turkiyya dauke da kayan agaji ga 'yan Gaza sun sauka a Masar

Isra'ila ta yanke ruwa da lantarki da kuma yi wa yankin Falasɗinu ƙawanya.
Shugaban Turkiyya Recep Erdogan ya ce zai ci gaba da aike wa al'ummar Gaza kayan agaji ta hanyar haɗa kai da Masar. Hoto: AA

Jiragen ƙasar Turkiyya ɗauke da kayayyakin agajin da za a kai wa al'ummar Gaza sun sauka a ƙasar Masar. wacce ke maƙwabtaka da yankin da ke fama da hare-hare da takunkuman Isra'ila.

Taimakon na zuwa ne sa'o'i bayan da rundunar sojin Isra'ila ta nemi illahirin al'ummar arewacin Gaza da su tattara su bar muhallansu su koma kudancin yankin cikin awa 24.

Shugaban Turkiyya Recep Erdogan ya ce zai ci gaba da aike wa al'ummar Gaza kayan agaji ta hanyar haɗa kai da Masar.

Ofishin Ayyukan Jinƙai na Majalisar Dinkin Duniya ya ce yawan Falasɗinawan da suka rasa muhallansu a Gaza ya ƙru har fiye da 423,000.

A wani yanayi mai ban mamaki na ta'azzarar rikici a Gabas ta Tsakiya, dakarun Isra'ila sun ƙaddamar da wasu hare-hare a kan Gaza, a matsayin martani ga ƙungiyar Hamas ta Falasɗinawa a yankunan Isra'ila.

An fara rikicin ne a ranar Asabar din da ta gabata lokacin da Hamas ta ƙaddamar da wasu hare-haren roka zuwa cikin Isra'ila ta ruwa da ta sama da ta ƙasa da ta kira da Operation Al Aqsa Flood.

Hamas ta ce harin martani ne kan yawan afka wa Masallacin Ƙudus da ake yi da kuma ci gaba da mamayar Gabashin Birnin Ƙudus da Yahudawa ƴan kama wuri zauna ke yi a wani lamari da cusgunawa Falasɗinawan.

Daga nan ne rundunar sojin Isra'ila ta ƙaddamar da nata hare-haren a kan Gaza.

Martanin na Isra'ila bai tsaya kan hare-hare ba kawai, ya haɗa da yanke ruwa da lantarki da yi wa yankin Falasɗinu ƙawanya, lamarin da ya ta'azzara halin da mutane ke ciki a yankin, wanda dama yake fama da takunkumai tun shekarar 2007.

Ba za a yarda da bukatar Isra’ila ta ficewar Falasdinawa daga Gaza ba: Turkiyya

Sanarwar sojin Isra’ila ta neman Falasɗinawan da ke zaune a arewacin Gaza su fice su koma kudancin yankin cikin awa 24 abu ne da ba za a taɓa yarda da shi ba, a cewar Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya.

“Tursasawa al’ummar Gaza miliyan 2.5 waɗanda ake ta yi wa ruwan bama-bamai a kwanakin nan, da hana su samun lantarki da ruwa da abinci, kan koma wa wani yankin da aka fi killace shi, ba take hakkin dokokin ƙasa da ƙasa ba ne kawai, abu ne da ba shi da hurumi a babin tausayi da jinƙan ɗan’adam,” kamar yadda ma’aikatar ta faɗa a wata sanarwa a ranar Juma’a.

“Muna sa ran Isra’ila ta yi gaggawar gyara wannan mummunan kuskuren nata tare da tsagaita wuta na rashin tausayin da take nunawa a kan fararen hular da ke Gazan,” sanarwar ta ƙara da cewa.

AA