Akalla Falasdinawa 2,808 aka kashe yayin da 10,859 suka ji rauni sanadin lugudan wuta ta sama da Isra'ila ke yi tun daga ranar 7 ga watan Oktoba. Hoto: AA

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya yana shirin samar da wani tsari dangane da yakin Isra'ila da Falasdinawa, kuma ya jaddada muhimmancin Turkiyya na samar da shi.

Yayin da yake magana da manema labarai a ma'aikatar harkokin wajen kasar a birnin Ankara, Hakan Fidan ya jaddada bukatar ganin kasashe da dama ciki har da Turkiyya su kasance masu shiga tsakani da zarar bangarorin biyu sun cimma yarjejeniyar da niyyar tabbatar da an yi aiki da ita.

Fidan ya kuma ce yana da muhimmanci kasashen duniya su matsa lamba a kan Isra'ila ta yi amfani da tsarin samar da kasashe biyu masu cin gashin kansu wato Two State Solution, inda ya ce Turkiyya ta bayyana matsayarta da bangarorin biyu.

Tattaunawa tsakanin ministan harkokin wajen Turkiyya da Amurka ta nuna cewa Shugaba Biden yana goyon bayan mafitar samar da kasashe biyu masu cin gashin kansu.

Fidan ya ce akwai bukatar kasashen duniya su taka rawa sosai wajen magance rikicin Falasdinawa da Isra'ila. Ya kuma yi magana kan cewa babu yiwuwar samar da dakarun samar da zaman lafiya daga Turkiyya zuwa yankin, amma kuma ya kara nuna muhimmancin bin hanyoyin tabbatar da mafitar samar da kasashe biyu don samun dorewar zaman lafiya.

Akwai bukatar kasashen yankin su taka rawa kuma baki ya zo daya yayin da kowane bangare ya saba wa yarjejeniyar, a cewarsa.

A karshe ya jaddada muhimmancin amfani halin da ake ciki wajen samar da mafita kan zaman lafiya, ya ce samar da kasashe masu shiga tsakani zai taimaka wajen samun dorewar zaman lafiya a rikicin Isra'ila da Falasdinawa.

TRT Afrika