Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya tattauna da Firaministan Ethiopia wato Habasha Abiy Ahmed ta waya game da alaƙar da ke tsakanin ƙasashen biyu, da rikicin da ake fama da shi a yankin, da kuma ci gaban duniya.
Shugabanin biyu sun tattauna muhimman fannonin haɗin gwiwa tsakanin Turkiyya da Habasha, inda suka yaba da yadda dangantakar ke ci gaba da haɓaka a tsakanin ƙasashen biyu, in ji Ofishin sadarwa na Turkiyya a cikin wata sanarwa ta X a ranar Juma'a.
A yayin wannan kiran, Erdogan ya bayyana irin ƙoƙarin da Turkiyya ke yi na sasanta rikicin Somaliya da Habasha.
Ya kuma kara da cewa, matakan da Habasha za ta ɗauka domin kawar da damuwar Somaliya game da haɗin kan ƙasarta, da ikon mallakar da take da shi da amincin yankinta, za su taimaka wajen aiwatar da wannan tsari.
An gudanar da zagayen farko na tattaunawar kai tsaye tsakanin ministocin harkokin wajen Ethiopia da Somaliya a Ankara babban birnin Turkiyya a farkon watan Yuli. Hakan ya sa ɓangarorin suka amince su sake haɗuwa a zagaye na biyu ranar 2 ga watan Satumba.
Baya ga batutuwan da suka shafi yankin, Erdogan ya yi Allah wadai da yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza na Falasdinu tare da jaddada cewa Tel Aviv na ci gaba da aiwatar da kisan kiyashi a yankin da aka yi wa ƙawanya.
Shugaban ya bayyana cewa goyon bayan da Ethiopia ke bayar wa ga Falasɗinu ta hanyar fifita tunani mai kau irin na ɗan'adam zai taimaka wajen ƙoƙarin ƙasashen duniya na samar da zaman lafiya mai ɗorewa.