Erdogan ya ce Turkiye ba za ta dauki bangare a yakin da ake yi tsakanin Rasha da Yukren ba Photo: AA

Shugaban Kasar Turkiye Recep Tayyip Erdogan ya anar da cewa dukkan duniya na tattauna nasarar da kasarsa ta amu wajen kubutar da duniyar aga rikicin karancin abinci da hatarin da ahkaan ka iya janyowa.

Erdogan ya bayyana hakan yayin sanar da kara wa’adin yarjejeniyar fitar da hatsi zuwa kasashen waje da Yukren da Rasha suka sanya hannu a kai.

Shugaba Erdogan y ace duniya na yabawa kokarin shiga tsakanin Turkiye don sasanta Rasha da Yukren.

Ya ce ”Duniya ta riga ta san da mu. A dukkan duniya ana tattauna nasarar da Turkiye ta samu.”

Shugaban ya kuma tunatar da cewa Putin ya mika bukatar zai dinga tura hatsi kyau zuwa ga kasashe matalauta.

Ya kara da cewa Turkiye na shirye-shiryen sayen alkama tare da mayar da ita garin fulawa don turawa zuwa kasashen matalauta.

Erdogan ya kuma kara da cewa suna yunkurin fitar da takin zamanin da Rasha ke samarwa zuwa kasashe masu tasowa.

“Akwai bukatar takin zamani. Za mu kai musu. Za mu aika da takin zamanin zuwa kasuwannin duniya da kasashen da ba su ci gaba ba sannan mu yi kokarin rage musu radadin da suke ji.”

Shugaban ya kuma jaddada cewa Turkiye ba za ta dauki wani bangare a yakin da ake yi ba, kuma a koyaushe za ta kasance a bangaren zaman lafiya.

Ya ce “Magana ta gaskiya wannan ne matakin da muka dauka a rikin Rasha da Yukren.”

AA