Lokacin da Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bukaci a bude sabon babi a dangantaka da Tarayyar Turai – hakan ya kasance wani tukuici bayan amincewa da bukatar Sweden ta shiga kungiyar kawance ta NATO – kawayen Turkiyya na Yammacin Duniya sun yaba wa haka.
Jim kadan bayan haka ne aka dawo da batun tattaunawa kan bukatar Turkiyya ta zama mamba a Kungiyar Tarayyar Turai da kuma Kungiyar Kwastam.
Bayan tattaunawa da Shugaba Erdogan yayin taron kungiyar NATO a Lithuania a makon jiya, Shugaban Hukumar Tarayyar Turai Charles Michel ya ce "muna duba damarmaki kafin dawo da hulda tsakanin Tarayyar Turai da Turkiyya da kuma kara karfafa dangantarmu."
Ya kuma ce hukumar ta bukaci babban jakadanta Josep Borell da Majalisar Tarayyar Turai da su mika rahoton "nazari kan tsare-tsare" yiwuwar shigar Turkiyya Tarayyar Turai.
Shugabannin kasashen yammacin duniya ciki har da Shugaban Amurka Joe Biden da Shugaban Kungiyar NATO Jens Stoltenberg da Firaiministan Sweden Ulf Kristersson cikin hanzari suka nuna goyon bayansu ga zaman Turkiyya mamba a Tarayyar Turai, wanda ta fara neman hakan tun a ranar 31 ga watan Yulin shekarar 1959.
Shin Turkiyya ta fara sauya manufofinta na hulda da kasashen waje?
Biyo bayan amincewar Erdogan na tura kudirin neman yardar majalisar Turkiyya da kuma dawo da dangataka da Tarayyar Turai da kuma Amurka, masu sharhi kan al'amura suna ganin cewa Turkiyya ta "sauya matsayarta a siyasance", inda ta fara yin nesa-nesa da Rasha kuma tana kara jingina da "kasashen yamma."
Amma akwai abubuwa da yawa na manufofin wajen Turkiyya fiye da abin da ake gani a zahiri.
“Masu sharhin ba su san Shubaga Erdogan ba sam. Ga mu, duka matsayar da ya dauka daidai ce. Tunani ne irin na masu sharhi kawai a ce Turkiyya ta karkata zuwa kasashen Yammaci ko na Gabashin duniya," in ji mai magana da yawun Jam'iyyar AK Omer Celik, ya ce masu wannan kalamai ba su fahimci sarkakiyar manufofin kasashen wajen Turkiyya ba.
Yayin da ake ganin shigar Sweden kungiyar NATO ba abu ba ne da zai yi wa kasar Rasha dadi ba, sanarwar da fadar gwamnatin Rasha ta fitar ta ce ta fahimci matakin da Turkiyya ta dauka.
"Turkiyya tana da wani nauyin NATO a wuyanta, kuma muna sane da haka," in ji mai magana da yawun gwamnatin Rasha Dmitry Peskov.
Erdogan yana cikin shugabannin duniya 'yan kalilan da suke da kyakkyawar alaka da Rasha da Ukraine, inda ta ki goyon bayan kowane bangare a rikicin wanda ya raba duniya zuwa bangare biyu.
Peskov ya ce Turkiyya da Rasha suna da muradu, yayin da kasahen biyu suke da bambance-bambancensu haka zalika suna da wasu bukatu iri guda wadanda suka tilasta wa kasashen biyu yin aiki da juna.
Kodayake batun gaskiya Tarayyar Turai da Turkiyya suna da wasu muradu iri guda, misali a tekun Bahar Aswad da yankin Mena da yankin Balkans da batun tsaron Gabashin Nahar Rum da yaki da kwararowar 'yan gudun hijira ba bisa ka'ida ba da batun yaki da ayyukan ta'addanci da sauransu," in ji malamin jami'a Talha Kose na Jami'ar Ibn Haldun.
Sai dai ba za a iya kawar da kai daga wadannan muradu idan ana nazari kan huldar Turkiyya da Rasha.
Batun dangantaka da Amurka
Biyo bayan ganawarsa da Shugaban Amurka, Erdogan ya ce Turkiyya ta fara sabuwar hulda da Amurka.
Turkiyya tana kuskantar matsin lamba daga kawayenta na kasashen Yammacin Duniya, musamman daga Amurka, kan ta sanya wa Rasha takunkumi saboda yakin Ukraine. Amma duk da haka Turkiyya ta ci gaba da kasance 'yar ba ruwanmu a yakin.
Turkiyya ta zabar wa kanta matsayi dangane da rikicin, inda ta zama mai shiga tsakanin Ukraine da Rasha.
Turkiyya ba ta dauki wannan matsayar don ta rusa alakarta da Amurka da kuma kungiyar NATO ba, kamar yadda aka bayyana bayan babban taron da aka yi a birnin Vilnius na kasar Lithuania.
Duka shugabannin suna murmushi yayin da Erdogan ya yi Biden fatan samun nasara a zaben kasar Amurka mai zuwa. Biden ya mayar da martani da cewa yana fatan yin aiki da Shugaba Erdogan a shekaru biyar masu zuwa.
Ya gode wa Erdogan kan salon shugabancinsa da kuma daukar matsayar diflomasiyya dangane da amincewa da shigar Sweden kungiyar NATO.
Dangantaka tsakanin kasashen Yamma da Turkiyya tana nuni da yadda Turkiyya take ci gaba da kare matsayinta a tsakanin kawayenta, kuma duka kasashen Yamma suna mata kallo mai kyau, ita kuma tana kara karfafa matsayarta a kawancen.
Ko da yake yana da kyau a fahimci cewa matsayar Turkiyya ba domin ta rusa alakarta da Rasha ko kuma Yammacin duniya ba ne, Turkiyya tana tafiyar da manufofinta ne saboda cimma muradunta.
Kuma Erdogan zai ci gaba da kasancewa shugaba daya a kungiyar NATO wanda zai iya kawo Rasha da Ukraine a teburin tattaunawa.