Turkiyya ta yaba da kokarin shiga tsakani na Masar, Qatar da Amurka don ganin an samar da dawwamammen zaman lafiya a yankin Gaza na Falasdin, wanda a cikin sama da kwanaki 300 ke karkashin ruwan hare-hare daga Isra'ila.
"Muna goyon bayan aiwatar da matakan da shugabannin wadannan kasashe suka dauka wanda suka sanar a yau," in ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya a ranar Juma'a.
Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta nuna muhimmancin aiwatar da matakan da aka tanada a Matakin Kwamitin Tsaro na Majalisar DInkin Duniya mai lamba 2735, tana mai jaddada cewa wannan shiri ya samar da tushe samar zaman lafiya mai dorewa.
Ma'aikatar ta kuma yi kira ga Isra'ila da amsa irin tayin zaman lafiya da Falasdinu ta nuna na a tsagaita wutar rikicin.
Gwamnatin Turkiyya ta kuma bukaci kasashen duniya da su matsa lamba yadda ya kamata kan gwamnatin Isra'ila da Benjamin Netanyahu ke wa jagoranci da ta tabbatar an tsagaita wuta, sanna a ci gaba da tattaunawar wanzar da zaman lafiya.
Labanan ta goyi bayan kiran tsagaita wuta a Gaza da Amurka-Masar-Qatar suka yi
Labanan ma ta bayyana goyon bayanta ga matakain na hadin gwiwa da Amurka, Masar da Qatar suka dauka.
A yayin wani taron manema labarai a Beirut babban birnin Labanan, Ministan Harkokin Wajen Kasar Abdallah Bou Habib ya ce "gwamnatinsu na goyon bayan sanarwar hadin gwiwa da shugaban kasar Amurka Joe Biden, shugaban kasar Masar Abdul Fattah Al Sisi da Sarkin Qatar Tamim bin Hamad Al Thani.
Ministan ya yaba kokarin shugabannin uku da kasashensu saboda samar da 'fasalin yarjejeniya'.
Habib ya ce "Gwamnatin Labanan na bayar da muhimmanci ga kammala cimma yarjejeniyar tsagaita wuta da sakin fursunonin yaki kan doron ka'idojin da Shugaban Kasar Amurka Biden da Matakin Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya mai lamba 2735 suka tanada."
Yakin Isra'ila a Gaza da aka fara bayan harin kan iyaka da Hamas ta kai a 7 ga Oktoba, ya yi ajalin a kalla Falasdinawa 39,699 - mafi yawan su mata da yara kanana.