A baya ƙasar Armenia ta goyi bayan ƙudurin Majalisar Ɗinkin Duniya da ke kiran a tsagaita wuta nan-take a yaƙin Gaza. / Hoto: AA

Armenia ta sanar a hukumance cewa ta amince da ƙasar Falasɗinu a matsayin ƙasa mai cin gashin-kanta.

Wata sanarwa ranar Juma'a daga ma'aikatar harkokin waje ta ƙasar ta ce, "Domin jaddada ƙoƙarinta na tabbatar da bin dokar ƙasa-da-ƙasa, da daidaito, da 'yancin-kai da zaman lumana tsakanin mutane, Jumhuriyar Armenia ta amince da Ƙasar Falasɗinu".

Ma'aikatar ta ce a baya ƙasar Armenia ta goyi bayan ƙudurin Majalisar Ɗinkin Duniya da ke kiran a tsagaita wuta nan-take a yaƙin Gaza, inda Isra'ila ta kashe Falasɗinawa 37,000 tun Oktoban bara.

Armeni ta kuma soki hare-haren Isra'ila kan ababen more rayuwa na farar hula, da kuma zaluncinsu kan al'umma farar hula.

Jim kaɗan bayan ta sanar da wannan mataki, ƙasar da a baya take ƙarƙashin Tarayyar Soviet, ma'aikatar harkokin waje ta Isra'ila ta yi sammacin jakadan ƙasar.

"Sakamakon cewa Armenia ta amince da ƙasar Falasɗinu, ma'aikatar harkokin waje ta yi sammacin jakadan Armenia a Isra'ila don yin kakkausan kashedi," in ji wata sanarwa.

Wani babban jami'i daga Hukumar Falasɗinu, Hussein Al-Sheikh ya yi maraba da wannan mataki.

"Wannan nasara ce ga tsarin adalci, bin doka, da fafutukar al'ummarmu ta Falasɗinu don samun 'yanci da cin gashin-kai," Al-Sheikh ya faɗa a kafar sada zumunta.

"Mun gode da abokanmu na Armenia."

Babban mataki mai tasiri

Wannan mataki na Armenia yana zuwa ne bayan Spain, da Ireland da Norway sun amince a hukumance da ƙasar Falasɗinu.

"Amincewa da Ƙasar Falasɗinu ba wai kawai batu ne na adalci a tarihi ba. Batu ne na babban abin da muke buƙata idan muna son cim ma zaman lafiya," cewar Firaministan Spain Pedro Sanchez a watan jiya.

Ƙasashen uku na Turai sun yi imani cewa matakin nasu yana da tasiri babba a bayyane, musamman kan yadda yake ba da ƙwarin gwiwa ga sauran ƙasashe su bi sahunsu.

"Wannan ce hanya ɗaya tilo don tabbatar da warware matsalar da muka amince cewa ita ce hanyar cim ma zaman lafiya a gaba, don samun ƙasar Falasɗinu da ke rayuwa gefe da gefe da ƙasar Isra'ila cikin lumana da tsaro."

Isra'ila ta hasala kuma ta gaggauta sukar yunƙurin na ƙasashen Yamma, inda ta yi wa jakadunta da ke ƙasashen kiranye.

Wasu ƙasashen Turai bakwai na daban, ciki har da Sweden, tuni sun amince da zamowar Falasɗinu ƙasa mai 'yanci.

Ƙasashe da dama a duniya da hukumomin ƙasashen duniya sun yaba wa ƙasashen uku kan amince wa da ƙasar Falasɗinu.

TRT World