Turkiyya a ranar Laraba take murnar cika 101 da nasarar da ta samu kan sojojin Girka a yakin Dumlupinar a 1922.
Shugaba Recep Tayyip Erdogan da manyan jami'an gwamnati da na soji da shugaban 'yan adawa suka dora fulawar girmamawa a Antikabir, wanda a nan aka binne Mustafa Kemal Ataturk, wanda ya kirkiro Jamhuriyyar Turkiyya.
An yi shiru na minti daya inda Taken Kasar Turkiyya ya biyo baya.
"Ya kai Ataturk, muna murnar cika shekara 101 kan wannan gagarumar nasara da ka bayyana a matsayin abin tunawa har abada na kan shawarar kafa kasar Turkiyya mai 'yancin kai.
"Yau, wadda rana ce mai muhimmanci ta sauyi a tarihnmu, muna tunawa da ku, da abokan gwagwarmayarku, da mambobin Babbar Majalisar Kasa da Shahidanmu a cikin rahama," kamar yadda Shugaba Erdogan ya rubuta a littafin tunawa da 'yan mazan jiya a Antikabir.
Haka kuma mai dakin Shugaba Erdogan Emine ita ma ta yi murnar zagayowar wannan rana inda ta ce 30 ga Agusta wata alama ce ta kaiwa gaci jajircewa na kasar Turkiyya.
"Wannan sako ne fatan alheri ga duniya baki daya daga kasa wadda zuciyarta ke bugawa domin soyayyar kasa," kamar yadda ta bayyana a shafin X, inda take tunawa da Ataturk da duka shahidai.
Mataimakin shugaban kasa Cevdet Yilmaz ya bayyana cewa Turkiyya ta kawo wata sabuwar alkibla ga tarihin duniya a ranar 30 ga watan Agustan 1992.
"Irin sadaukarwar da aka yi wurin mayar da Anatolia kasarmu, da karfin da muka samu daga tarihinmu, da karfin giwa da hangen nesa na kasarmu su ne tabbacinmu mafi girma na samun 'yancin kai," kamar yadda Yilmaz ya bayyana a shafinsa na Twitter.
Shugaban majalisa Numan Kurtulmus shi ma ya bayyana cewa 30 ga watan Agusta ranar ce da ke alamta jaruma ta musamman wurin samun 'yancin kai
"30 ga Agusta rana ce a gare mu kara son kasarmu da kuma ci gaba da zama a cikin wannan kasar har abada. Muna murna da nasara," in ji Kurtulmus a shafin X.
Ita ma ma'aikatar tsaro ta kasar ta tuna Ghazi Mustafa Kemal Ataturk, da yadda gwarzaye da shahidai suka yi gwagwarmaya.
"30 ga watan Agusta ita ce rana ta karshe ta sojojin Girka. Shugaban sojoji Mustafa Kemal Pasha (ya bayar da umarni): 'Sojoji, burinku na farko shi ne Bahar Rum!' An fatattaki sojojin Girka baki daya daga fagen daga a yakin da ya kai har dare. 30 ga watan Agusta ta kasance ranar nasara!"
Babban farmakin soji, wanda tana daga cikin nasara mafi girma ga soji a tarihi - dakarun Turkiyya ne suka kaddamar da farmakin a ranar 26 ga watan Agustan 1922, a karkashin Mustafa Kemal Ataturk, wanda shi ne ya kirkiro Turkiyya ta zamani, inda aka kammala farmakin a ranar 18 ga watan Satumabar 1922.
Daga 26 ga watan Agusta na 1992, dakarun Turkiyya sun gudanar da yakin Dumlupinar a yammacin yankin Kutahya wanda a nan ne aka ci sojojin Girka da yaki.
Zuwa karshen 1992, duka dakarun waje sun bar yankunan da daga baya suka zama karkashin sabuwar Jamhuriyyar Turkiyya bayan shekara daya.