Erdogan ya kuma fayyace cewa yana da muhimmanci ga al'ummomin kasa da kasa, musamman Majalisar Dinkin Duniya su yi wani abu a kan batun Falasdinu. / Photo: AA

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya sha alwashin ci gaba da kare muradun Falasdinawa tare da kyautata rayuwarsu.

"A matsayin Turkiyya, za mu ci gaba da goyon bayan muradun Falasdinawa a hanya mafi karfi da ta fi dacewa. Mun damu kwarai kan rikicin 'yan kama wuri zauna da ke faruwa," Erdogan ya fada a yayin wani taron manema labarai lokacin da ya karbi bakuncin takwaransa Shugaban Falasdinu Mahmoud Abbas a ranar Talata a birnin Ankara.

Erdogan da Abbas sun tattauna a fadar shugaban kasa kan dangantakar kasashen biyu da batun Falasdinu da Isra'ila da kuma sauran batutuwan ci gaban yankin da na kasa da kasa.

"Ba za mu lamunci duk wani abu na kokarin sauya matsayar tarihi na tsarkakakkun wurare ba, musamman ma Masallacin Kudus. Hadin kai da sasantawar Falasdinawa su ne manyan abubuwan da ake bukata a wannan aiki," ya kara da cewa.

Shugaban Turkiyya Erdogan ya ce:

  • Za mu ci gaba da yin dukkan kokarinmu don tabbatar da tsaron al’ummar Falasdinu
  • Wata rana za a kafa kasar Falasdinu mai cin gashin kanta, wacce babban birninta zai kasance Birnin Kudus
  • Ina mika gaisuwata da dukkan al’ummar Falasdinawa.

Zaman lafiya da kwanciyar hankali

Erdogan ya kuma fayyace cewa yana da muhimmanci ga al'ummomin kasa da kasa, musamman Majalisar Dinkin Duniya su yi wani abu a kan batun Falasdinu.

"Samar da kasar Falasdinu mai cin gashin kanta da Gabashin Birnin Kudus zai zama babban birninta bisa dokokin shekarar 1967 da MDD ta sanya yana da muhimmanci ga zaman lafiya da tsaron kafatanin yankinmu," ya jaddada.

Ana sa ran shi ma Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu zai ziyarci Turkiyya a wannan makon, amma an dage tafiyar bayan da aka yi masa wata tiyatar bagatatan a karshen makon da ya wuce.

Ankara na matukar goyon bayan samar da wata kasar a matsayin hanyar warware rikicin Isra'ila da Falasdinu, ciki har da son samar da kasar Falasdinu mai cin gashin kanta da babban birninta zai kasance Gabashin Birnin Kudus.

TRT World