A ranar Alhamis ne Faransa ta kare wani sako da aka wallafa a shafin sada zumunta kan Armeniya wanda ya nuna alamun kasar na goyon bayan muradun 'yan yankin masu tsananin kishin kasa.
Ministar harkokin wajen kasar Catherine Colonna ta wallafa a shafinta na X a ranar Talata bayan ziyarar da ta kai Armenia a makon nan, inda ta yada hoton Tsaunin Agri da aka fi sani da Arafat a Turance - wani yanki da aka kafa a matsayin mallakin Turkiyya da ke gabashin kasar - wurin da wasu Armeniyawa ke neman zaman da shi na kasarsu.
A wani taron manema labarai na Ma'aikatar Harkokin Waje Faransa da aka yi a birnin Paris, an tambayi mai magana da yawun kasar kan ko Faransa ta yarda cewa tsaunin na Armeniya ne - ko kuma Colonna "ta yi kuskure ne" game da wannan al'amari - kuma shin ba ta san cewa irin wannan sako da ta wallafa zai iya tayar da kura da kuma harzuka Turkawa da dama ba.
"Tsaunin Agri wani wuri ne da ke nuna wata alama idan aka kalle shi daga Armeniya" - sakamakon kusancin tsaunin da iyakokin kasashen - a cewar martanin da mai magana da yawun Faransa Anna-Claire Legendre ta bayar.
An wallafa hoton ne a lokacin ziyarar Colonna a Armenia, in ji ta, ta kara da cewa Armeniya ba ta da wani muradi na mallakar yankin, kuma Faransa ta fito fili ta bayyana hakan.
Turkiyya ta soki Firaiministan Faransa
Wakilin Turkiyya na musamman da ke shiga tsakanin tattaunawa da Armeniya Serdar Kilic ya jaddada cewa tsaunin yana tsakanin iyakokin Turkiyya.
Kilic ya ce "Minista, wannan tsaunin na cikin hoton, tsaunin Ararat, wanda ke tsakanin iyakokin Turkiyya, don haka wani bangare ne na Turkiyya," in ji Kilic.
"Saboda haka, ina ganin ko dai kuna da wata manufa a ziyararku ko kuma kuna bukatar samun ilimin sanin kasa ne."
Kasashen Turkiyya da Armeniya sun dade suna takun saka, duk da cewa nadin jakadu na musamman da aka yi a watan Disambar 2021 wani mataki ne na inganta alakar kasashen biyu.
A shekarar 1921 a kafa iyaka tsakanin Jamhuriyar Turkiyya da Armeniya a karkashin yarjejeniyar Kars sama da shekaru 100 da suka gabata.