Altun ya bayyana cewa tsarin da ake da shi a duniya a halin yanzu ya gaza yin komai dangane da irin kisan kiyashin da ake yi a Gaza. / Hoto: AA

Fahrettin Altun, Shugaban Sashen Watsa Labarai na Jamhuriyar Turkiyya ya yaba wa kakkarfan martanin da matasa suke mayarwa a fadin duniya, kan kisan kiyashin da Isra’ila take yi wa Falasdinawa a Gaza.

Sakon da suke aike wa duniya “ya nuna irin tausayin matasa, da hanyoyin da suke bi wajen bin gaskiya da kuma halayyarsu ta nuna adalci.

Don haka ya kamata mu amince da wannan karfin hali,” a cewar Altun a ranar Asabar lokacin da yake magana a zauren Next na TRT Word.

Ya bayyana cewa taron wata shaida ce da ke nuna cewa matasa su ne muhimman wadanda aka damawa da su kuma masu shiga a dama da su a al’amuran duniya, maimakon komawa gefe su zama ‘yan kallo.

Gazawar tsarin duniya

A duniyar da muke rayuwa a yau muna bukatar tausayi da kawaici da nuna adalci da jajircewar matasa, a cewar Altun lokacin da yake jawabi a wajen.

Da yake nuna cewa akwai matsala sosai a wajen yin adalci da gaskiya a duniya, Altun ya kara da cewa tsarin da ake bi yanzu a duniya ya gaza idan aka yi la'akari da abubuwan da ke faruwa a yanzu, kuma babu wani yunkuri da ake yi na gyara al’amura.

“Muna fuskantar wani tsarin duniya da ba zai iya daukar wani kwakkwaran mataki kan kisan kiyashin da ake yi a Gaza ba, kuma gaba daya tsarin yana goyon bayan Isra’ila ne,” a cewar shugaban sashin watsa labaran.

“Tsarin duniya ya mika wuya ga ‘ra’ayin addinin’ Yahudanci duk da cewa tsarin na duniya ba ruwansa da addini, sannan da yadda ake tattauna al’amura ido bude. Mun shaida yadda tasarin duniya yake kokarin halasta kisan kiyashi a Gaza,” a cewarsa.

TRT World