Taron na kwana daya zai samu halartar fitattu a fannoni daban-daban daga Turkiyya da sauran kasashe. / Hoto: TRT World

Za a gudanar da taron duniya na TRT World Forum karo na biyu mai taken NEXT, wanda zai mayar da hankali wurin tattauna kalubalen da mata ke fuskanta a duniya da yadda za a shawo kansu.

Taron, wanda za a yi ranar 20 ga watan Yuni, zai samu halartar matasan 'yan jarida, malaman jami'a, shugabannin kungiyoyi masu zaman kansu da kuma 'yan kasuwa.

Za a gudanar da shi ne a cibiyar Zorlu Performing Arts Center (Zorlu PSM) da ke birnin Istanbul.

Wannan shekarar, za a tattauna kan yadda za a shawo kan matsalolin da ke addabar kafofin watsa labara, fannin fasaha, sauyin yanayi, kasuwanci, wasanni, ilimi da tafiye-tafiye.

Kazalika taron zai mayar da hankali kan bunaksa hanyoyin walwala da al'adu da fasaha domin samar da mafita.

NEXT zai zama wani dandali ga matasan shugabanni, 'yar jarida, malaman jami'a, shugabannin kungiyoyi masu zaman kansu da kuma 'yan kasuwa na samar da mafita kan abubuwan da ke yi wa duniya tarnaki.

A bara, matasa 1,000 na fannoni daban-daban ne daga ciki da wajen Turkiyya suka halarci wannan taron.

Sun tattauna kan batutuwa daban-daban da suka hada da tafiya sararin samaniya, tsarin kasuwanci mai dorewa fasahar komfuta ta immersive NFT, da makamantansu.

Baya ga wannan, an yi baje-kolin kirkirarriyar basira da fasahar kamar-da-gaske ta virtual reality sannan taron ya bayar da damar tattaunawa da baki na musamman da yin baje-koli kan soshiyal midiya.

Taron bana zai samu halartar fitattun mutane daga Turkiyya da kasashen waje, ciki har da shahararren mai girka abinci da mu'amala da intanet dan kasar Turkiya kuma Burak Ozdemir, wanda aka fi sani da CZN Burak. Zai tattauna kan maudu'i mai suna, 'Tattaunawa mai ma'ana: Hada kai don rage tasirin annoba', inda zai mayar da hankali kan girgizar kasar da aka yi a Turkiyya a watan Fabrairu wadda ta yi sanadin mutuwar fiye da mutum 45,000.

Tawagar Ozdemir ta kai kayayyaki zuwa yankunan da girgizar kasar ta shafa, ciki har da Hatay, daya daga cikin yankunan da lamarin ya fi ta'azzara.

Kazalika Asma Elbadawi, 'yar kwallon kwando kuma koci da aka haifa a Sudan amma ta girma a Birtaniya, za ta halarci taron.

Elbadawi, wadda kuma mawakiyar baka ce, ta fuskanci kalubale da dama na raini da cin zarafi a rayuwarta, don haka za ta bayar da gudunmawa kan yadda ta jajirce wajen ganin an janye haramcin da aka sanya na saka hijabi a wasa kwallon kwando a 2014.

Haka kuma taron zai karbi bakuncin tsohon dan kwallon kafa Frederic Oumar Kanoute.

A taron da aka yi a shekarar da ta wuce, NEXT ya gudanar da kananan taruka 11, tattaunawa 7, sannan manyan mutane 26 suka yi jawabi kuma fiye da mutum 1000 suka halarce shi. Fiye da mutum 2000 suka rubuta takardar neman halartar taron, kuma kusan mutum 1400 sun nemi zuwa ne daga Turkiyya yayin da sauran suka fito daga kasashen ketare.

Mutanen da suka halarce shi sun fito daga kasashen Amurka, Canada, Birtaniya, Italiya, Netherlands, Sudan, Chile, Pakistan, India, Jordan, Namibia, Tanzania, da Nijeriya.

Za ku iya yin rajitar halartar taron idan kuka danna nan https://next.trtworldforum.com/.

TRT World