Zaben shugaban kasa da ‘yan majalisar dokoki na 2023 na Turkiyya zai kafa tarihi saboda yadda ake da yawaitar mata da suka tsaya takarar majalisar dokoki. Kazalika za a samu ‘yan majalisa mafiya karancin shekaru.
Nisa Alptekin, mai shekara 18 kuma ‘yar takarar majalisar dokoki daga lardin Izmir karkashin jam’iyyar AKP, ta zama wata alama ta muhimmancin shigar mata siyasa da tsayawa takara.
Tare da ‘yan takara da yawa irin Alptekin da ke tsayawa takara a zabuka, fagen siyasar Turkiyya zai sauya ta fuskar samar da wakilci.
Mun yi nazari kan yadda ake damawa da mata a siyasar Turkiyya
Mata a majalisar dokoki
A ko da yaushe mata suna taka muhimmiyar rawa a siyasar Turkiyya.
A zabukan da suka gabata, mata ‘yan majalisar dokoki sun kai kashi 18 na mambobi 600 a majalisar dokokin Turkiyya. Ana sa ran wannan adadi zai karu saboda an samun yawaitar mata ‘yan takara.
Jerin ‘yan takarar jam’iyyar AKP na da mata 113 daga cikin ‘yan takara 600, kuma mata ne a sahun gaba a yankunan Agri, Duzce da Osmaniye.
Tun bayan hawa karagar mulki, jam’iyyar AKP karkashin Shugaba Recep Tayyip Erdogan ta nada mata a mukamai da dama, da suka hada da Minista da ta fi kowacce dadewa a kan kujerarta, Nimet Bas, wadda ta yi sama da shekara shida a matsayin minista.
Bayan da jam’iyyar AKP mai mulki ta yi wata doka a 2013 kwaskwarima, an bayar da karin dama ga mata su tsaya takara sannan su yi aiki a ofisoshin gwamnati a Turkiyya.
Jam’iyyar MHP na da mata ‘yan takara su 90 daga cikin 600 da suke neman kujerun majalisar dokokin Turkiyya. Matan na jerin ‘yan takara uku na farko a larduna 18.
Jam’iyyar CHP kuma na da mata 147 da suke takara a wannan karon, mata 7 ne suke a sahun farko na ‘yan takarar kujeru 600 na majalisar dokokin kasar. Amma ‘yan takara daga jam’iyyun Saadet, DP, DEVA da Gelecek na takara ne a cikin ‘yan jam’iyyar CHP a dukkan fadin kasar karkashin kawancen kasa.
Jam’iyyar IYI na da mata ‘yan takara152 daga cikin 600, inda jam’iyyar HDP da ke da alaka da ‘yan ta’addar PKK take da mata 193 daga ‘yan takara 490 da ta fitar wadanda suke takara karkashin jam’yyar YSP.
Matasa da ke neman shiga ofis
Alkaluman Hukumar Kididdiga ta Turkiyya sun bayyana daga 2021, masu shekaru 15 zuwa 24 sun kai yawan kaso 16 na adadin jama’ar Turkiyya. Matasa na shiga siyasa sosai a dama da su, inda jam’iyyu daban-daban suka tsayar da matasa da yawa takara. Shekaru matsakaita na ‘yan takarar a wannan zaben na kasa da na zabukan da suka gabata, inda a yanzu ake da matasa da dama da ke yin takara.
Alkaluman da aka samu daga Hukumar Zabe ta Koli ta Turkiyya sun nuna an samu kari sosai na adadin matasa da ke shiga siyasa a Turkiyya. Misali a zaben ‘yan majalisar dokoki na 2018, kaso 24.5 na ‘yan takara ‘yan kasa da shekaru 40 ne. Haka kuma ‘yan takara 143 na da shekaru kasa da 30.
A wannan zaben na 2023 kuma, adadi mai yawa na matasa sun bayyana aniyarsu ta tsaya wa takara.
A zabukan gama-gari na 2019, matasa masu karancin shekaru sama da 2,300 ne suka tsaya takarar neman kujeru daban-daban.
Dadin dadawa, jam’iyyun siyasa a Turkiyya sun gano amfanin matasa a tafiyarsu wanda hakan ya sa suke ba su dama sosai. Misali, jam’iyyu da yawa na amfani da shafukan sada zumunta wajen isar da sakonninsu ga matasa masu jefa kuri’a.
Tarihin shigar mata siyasa
Tarihin shigar mata siyasa a Turkiyya na koma wa ga farkon karni na 20, a lokacin da mata suka shiga gwagwarmayar neman ’yancin kai.
A 1934 ne mata a Turkiyya suka samu ‘yancin jefa kuri’a da tsaya wa takara, inda aka zabi mata 18 a shekarar da ta biyo baya a matsayin ‘yan majalisar dokoki.
Amma kuma, shigar tasu siyasa ya samu tsaiko har sai a baya-bayan nan.
Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya dauki matakan baiwa mata damar shiga harkokin siyasa. Daya daga cikin matakan shi ne yadda a 2013 ya shardanta dole jam’iyyarsa ta AKP ta ware kaso 30 na ‘yan takararta ga mata a zabukan ‘yan majalisar dokoki, wanda hakan ya sanya dukkan sauran jam’iyyu suka tsayar da mata su ma.
Wannan doka da ya kawo na da matukar muhimmanci wajen wakilcin mata a siyasar Turkiyya. Ya nada mata a manyan mukamai da suka hada da ministoci, gwamnoni da jakadu.