Shirin zai mayar da hankali wajen samar wa matasa 550 a fannin yada labarai da fasahar sadarwa ayyukan yi, a cewar Mehmet Fatih Kacır.
Ministan Masana'antu da Fasaha na kasar Turkiyya Mehmet Fatih Kacır, ya jaddada muhimmancin sabon shirin sanin makaman aiki na al'umma 'Istanbul Codes Project' a yayin taron karawa juna sani da aka gudanar a Jami'ar Bogazici.
“A tsarin aikin, matasanmu masu shekara 18 zuwa 35 wadanda ba su samu aikin yi ba na tsawon shekara guda su za mu fi mayar da hanakali a kansu, muna fatan za a dauki matasa 550 aiki a fannin yada labarai da fasahar sadarwa, sannan an ware dala miliyan 1.25 don aiwatar da wannan shiri, " in ji Kacir.
"Sabon shirin na sanin makamar aiki na al'umma da muka kaddamar, mun yi shi ne a matsayin gwaji na wasu shirye-shirye da za mu yi a gaba a Istanbul.
Daga wannan muke son fadada wasu ayyuka na saka hannayen jari a yankuna da sassa daban-daban bisa ga irin nasarar da muka ga an samu."
Erkam Tuzgen, Sakatare-Janar na Hukumar Ci Gaban Istanbul (ISTKA), wanda ya bayyana cewa shirin sanin makamar aiki na al’umma sakamoko ne da aka samu daga wasu tsare-tsare da ke samar da amsoshin matsalolin zamantakewa na al’umma, ya ce : "Tsarin aiki ne da hada kan jama'a da kungiyoyi da kuma kamfanoni masu zaman kansu.’’
"Babban abu na musamman da ya bambanta a tsakanin wadannan shirye-shiryen da ayyukan hukumomin na ci gaba yau da kullun shine, kamfanoni masu zaman kansu su za su dauki cikakken ikon duk wani hadari da zai biyo baya,
Akwai manyan masu ruwa da tsaki guda uku da za su aiwatar da wannan aiki, sannan duk wanda ya saka hannun zari shi zai fara biyan kudi ga kamfanin da zai yi aikin"in ji Tuzgen".
'Aiki na musamman'
Safak Muderrisgil, Shugaban Hukumar Zartaswa ta Etkiyap, ya bayyana kaddamar da shirin a matsayin wani muhimmin ci gaba ga kasar, yana mai cewa, " Muhimmacin sanin makaman aiki na al’umma ya ta'allaka ne ga yadda suke iya samar da mafita ga al'amuran da su shafi zamantakewa ta hanyar kayan aikin zuba jari."
"Ana samun hakan ne ta irin hadin gwiwa da aka samu tsakanin al’umma da yan’ kasuwa. Muna magana ne game da tsarin kudi da kowace masana'anta za ta ba da gudummawarta don gyara matsalar al'umma cikin tsarin zuba jari," in ji shi.
Mene ne manufar aikin?
Manufar aikin ‘Istanbul Code’ habaka kwarewa da iyawar matasa ta hanyar ba su horon fasahar software. Matasan da suka kammala samun horo a ilimin software za su iya samun aiki a aikin kasuwanci na software.
Ana sa ran shirin zai samarwa matasa 550 da ba su da aikin yi sana’o’in da za su iya dace wa da su a nan gaba tare da sanya su cikin ma’aikatunmu.
Su ma kamfanoni za su samu biyan bukata na horar da al’umma a fannin fasahar software.
Mutanen da ke tsakanin shekaru 18 zuwa 35, sannan a kalla sun kammala karatun matakin sakandare kuma ba su da aikin yi na akalla tsawon shekara guda kuma suna son yin aiki a kasuwar fasahar software na iya neman damar shiga shirin.