Taron ya hada jagororin matasa da dama wadanda suka bayar da gudunmawa daban-daban a bangarorin da suka shahara. / Photo: AA

Taron kafar watsa labarai na TRT kan matasa zalla ya magantu kan batun kalubale daban-daban da duniya ke fuskanta da kuma kara karin gwiwa kan musayar shawarwari.

Taron ya hada jagororin matasa da dama wadanda suka bayar da gudunmawa daban-daban a bangarorin da suka shahara.

Taron na NEXT karo na biyu wanda aka gudanar a ranar Talata an yi shi ne a birnin Santambul inda mahalarta taron suka gabatar da jawabai, da kara wa juna sani kan abubuwa da dama masu muhimmanci domin samun ci gaba mai dorewa.

A bara, taron ya hada kan sama da matasa dubu daya da ke fadin duniya, tare da hada muhawara 11 da taron kara wa juna sani da bakwai da kuma masu jawabai 26.

A bana, an rarraba wannan taron zuwa gida goma: NEXT leads, kimiyya, wasanni, aikin jarida, duniya, kasuwanci, ilimi, samun dama da aikin gama gari.

Akwai abubuwa da dama da kowa zai iya koya da kuma bayar da gudunmawa a ciki.

Taron ya soma ne da tattaunawa kan “Kirki zai iya ceto makomarmu: Dogaro da kai” inda wadanda suka halarci taron za su iya samar da kyakkyawan sauyi a cikin al’umma ta hanyar mayar da hankali kan kalubale daban-daban da kuma bude hanyoyi domin samun makoma mai kyau.

A bangaren Wasanni kuwa, an yi duba kan rayuwar masu wasanni guje-guje da tsallae-tsalle d airin nasarori da kalubalen da suke fuskanta. An yi duba kan labaran da ba a faye jin su ba a wadannan bangarori.

Akwai kuma tatttaunawar da aka yi a kan Sauyi Yanayi mai take "Climate Anxiety: The Youth Wants a Different Planet", inda aka yi duba kan tasirin sauyin yanayi a kan matasa musamman abin da ya shafi sanya musu tsoro da fargaba.

An gabatar da bayanai kan maudu'ai da dama a wajen taron. Hoto: TRT WORLD 

Dalilin wannan tattaunawa ita ce don a samar da wani yanayi da za a yi musayar ra'ayi da kuma taimakawa matasa yadda za su mayar da fargabarsu wajen cimma wani abu mai kyau.

Mutane da dama ne suka halarci taron na kwana guda kuma suka gabatar da jawabai don karfafa gwiwar matasa.

Matasan da suka halarci taron sun zo daga kasashe irin su Amurka da Italiya da Birtaniya da Canada da Netherlands da Sudan da Chile da Pakistan da Indiya da Jordan da Nambiya da Tanzaniya da Nijeriya da sauran wurare.

Mahalarta taron sun samu damar tattaunawa da ganawa da juna da musayar ra'ayoyi.

TRT World