Shugaban Turkiyya ya yi nasara a zaben shugaban kasa da ‘yan majalisar dokoki da aka gudanar, inda bayanansa a yayin gangamin zabe suka mayar da hankali kan neman hadin kai tare da watsi da rarrabuwar kawuna, in ji Daraktan Sadarwa Fahrettin Altun.
“Shugaba @RTErdogan ya rungumi dattako da aiki da lura a matsayin manyan jiga-jigai a siyasa. Sabanin haka kuma abokin hamayyarsa (Kemal Kilizcdaroglu) bai damu da dattako ba.
"Bai kuma damu da fadin gaskiya ba. Yana fadar abin da ya ga dama a lokacin da ya ga damar fada,” in ji Altun a wani sako da ya fitar ta shafinsa na Twitter a ranar Litinin din nan.
Altun ya ce zaben Shugaban kasa da ‘yan majalisar dokokin Turkiyya da aka kammala ya nuna bambanci tsakanin dabarun yakin neman zabe na Erdogan da na abokin hamayyarsa.
"Ya kara da cewar a lokacin da Erdogan ya mayar da hankali kan dattako, aiki d alura tare da tabo batutuwan da suka shafi zamantakewar al’umma da cigabansu, abokin hamayyarsa kuma ya mayar da hankali wajen “Wuce gona da iri kan yana tare da jama’a da fadin abubuwan da babu su”.
Ya ce an gudanar da gangamin zaben cikin ingantacce yanayi na adalci, kuma Shugaba Erdogan da ya fuskanci kawance masu ra’ayin rikau da masu saukin ra’ayi, ya gudanar da gangami cikin gaskiya, bai yi alkawarin karya ba, kuma ya yi watsi da yada bayanan karya da za su cutar.
Ya ce “Ba masu amfani da kafafan sada zumunta na yanar gizo da suka boye fuskokinsu ne kawai suka shiga ayyukan yada labaran karya ba, har ma da manyan kafafen yada labarai na kasa da kasa.
"Abin bakin ciki, abokin hamayyar shugaban kasar ya zama shi ne mai yada wadannan labarai na karya da kansa.”
Rarrabuwar kai a siyasa
Haka kuma, duk da kokarin shugaba Erdogan na magance afkuwar “rarrabuwar kai a siyasa ya janyo rarrabuwar kai a zamantakewa, abokin hamayyarsa ya yi duk abin da zai iya don canja rarrabuwar kai a siyasa ya koma rarrabuwar kan al’umma a yanayin zamantakewar su. Har ta kai ga suna kalaman nuna kyama.”
Daraktan ya ambaci irin yadda masu adawa da Erdogan suka dinga amfani da bayanan karya bayyana manufofin rarraba kan al’umma a yayin yakin neman zabe.
Ya ce “Shugaban kasar ya gina yakin neman zaben sa kan tushen ka’dojin nazarin zamantakewa wanda yake tare da gaskiyar yadda al’amura suke a siyasance: ‘al’umma ta fi daidaikun mutane.’ Wannan ka’ida tare da kokarinsa na kare hakkokin ‘yan kasa, wanda ya yi masa jagora don magance matsalolin al’umma.”
Altun ya kuma bayyana cewa shugaba Erdogan ya fito da “Karnin Turkiyya” a cikin manufofin jam’iyyarsa na zabe… Kuma shugaban ya fitar da littafi mai shafuka da yawa da aka bai wa sunan “Kyawawan Matakan Isa ga Karnin Turkiyya’.
Ya kuma tabo batun kyawawan ayyuka, wadanda bangare ne ne wannan shiri da ya so kaddamarwa, a tattaunawar talabijin da wuraren gangamin zabe.
Ya kara da cewa “Ba za a tafi ba tare da fadin jama’ar Turkiyya na goyon bayan Shugaba Erdogan saboda sun san kyawawan halayensa.”
Sama da ‘yan kasar Turkiyya miliyan 64.1 ne suka cananci jefa kuri’a a zagaye na biyu na zaben da aka gudanar a ranar Lahadin nan, masu zaben sun hada da mutum miliyan 1.92 da suka fara jefa kuri’a a kasashen waje da kan iyakokin Turkiyya.
Kusan akwatunan zabe dubu 192,000 aka ajje a cikin Turkiyya.
Sakamakon zaben da ba a bayyana ahukumance ba, ya bayyana Erdogan a matsayin wanda ya yi nasara da kaso 52.14, inda Kilicdaroglu ya samu kaso 47.86 na kuri’un da aka jefa.
Ya zuwa yanzu an bude kaso 999.43 na akwatunan zabe.