Wata nau’in gasar FIFA na gaf da zuwa, inda ake da kasa da wata guda don fara gasar ta kwallon kafa ta kasa da kasa.
Qatar 2022, gasar kwallon kafa ta duniya ta farko da za a gudanar a lokacin sanyi, za a yi gasar a tsakanin 20 ga Nuwamba da 18 ga Disamban 2022.
Yadda akasaba shi ne a gudanar da gasar FIFA a loakcin zafi, kuma tana zuwa bayan kakar wasanni a Turai.
Amma an yanke hukuncin buga gasar ta Qatar 2022 saboda tsananin zafin dake kasar a lokacin zafi. Ana gama wasan karshe a Disamba, kungiyoyin za su dawo filayen atisayensu na 2022/2023.
Kuma zai zama karo na farko da wata kasar Larabawa take karbar bakuncin gasar.
Haka zalika, Qatar 2020 za ta zama gasar FIFA ta duniya da za a yi a Asiya tun bayan wadda aka buga a South Korea da Japan da aka yi a 2002, wanda Barazil ta lashe.
Qatar na Yammacin Asiya a gabar tekun kasashen Larabawa, a yanzu. Barazil na son lashe wannan gasa a karona shida
Barazil ne suka fi kowa lashe gasar, su ne suka lashe sau 5 zuwa yanzu. Barazil na ci gaba da kwadayin sake lashe gasar a kusan shekaru 20.
Barazil da Neymar ke jagoranta za su yi gwagwaröayar sake lashewa a Qatar.
A shekarar 2002 ne Barazil ta lashe gasar a karo na biyar a Yokohama, bayan ta doke Jamus da ci 2 da 0.
Haka kuma Faransa dake da ‘yan wasa sanannu a tawagarta irin su Klian Mbappe, Paıl Pogba da Antoine Griezmann ne ke rike da kambin a yanzu haka.
Faransa ta lashe gasar ta duniya sau biyu; a 1998 da 2018, yanzu ma suna son sake lashewa don ci gaba da rike kofin.
A gasar ta 2018 da aka gudanar a Rasha, Faransa ta lashe gasar bayan doke Kuroshiya da ci 4 da 2, inda Griezmann, Pogba da Mbappe suka jefa kwallaye.
A gasar ta 2014 kuma, Jamus ta so ta kamo Barazil a lokacin da Die Mannschaff ta lashe a karo na hudu.
Italiya ma ta lashe gasar sau hudu;1934, 1938, 1982 da 2006, amma ba samu nasarar halartar gasar Qatar 2022 ba.
Qatar za ta bayyana, Wales da kanada sun dawo bayan tsawon lokaci
Kasar da za ta karbi bakuncin gasar ta Qatar dake da alaka da Tarayyar Kwallon Kafa ta Asiya, za ta yi fitar ta ta farko a watan Nuwamba.
Qatar na rukunin A, za su utnkari Ecuador, Sanagal da Holan, wadanda su ne suka zo na biyu a gasar duniya ta 2010.
Haka kuma Wales da Kanada za su buga wasanni a gasar bayan tsawon lokaci.
Wales sun samu nasarar zuwa gasar ta Qatar 2022 bayan shafe shekaru 64 ba sa samun nasara. A watan Yuni, Wales da Gare Bale ya jagoranta suka doke Yukren da ci 1 da 0 a wasan neman cancantar zuwa gasar.
Dan wasan gaba na Yukren Andriy Yarmolenko ne ya ci kansu da kansa inda ya aika da kungiyar zuwa wasar kasa da kasa.
Kanada ta samu damar zuwa gasar ta duniya a karon farko cikin shekaru 36 bayan sun zo na uku a gasar CONCACAF.
Kungiyar ta jajaye sun samu nasarar zuwa gasar bayan doke Jamaica da ci 4 da 0. Wannan ne karo na farko da Kanada za ta halarci gasar tun bayan ta Mexico 1986.
A rukunin F, Kanada za ta kece raini da Beljiyom, Morokko da Kuroshiya.
Beljiyom ce ta zo na uku a gasar 2018 da aka yi a Rasha, Kuroshiya kuma su ne na biyu a gasar ta gabata.
Har yanzu Klose ne ya fi kowa jefa kwallaye a gasar ta duniya
Tsohon dan wasan gaba na Jamus Miroslav Klose kuma wanda ya lashe gasar 2014 ne ya fi kowanne dan wasa jefa kwallaye a gasar cin kofin duniya.
Klose ya jefa kwallaye 16 a gasar cin kofin duniya hudu da ya halarta; 2002, 2006, 2010 da 2014.
Ya gota zakaran Barazil Ronaldo a gasar kwallon kafa ta 2014 inda Jamus ta doke Barazil da ci 7 da 1.
Ronaldo na da kwallaye 15 a wasanni 19, Gerd Muller ne ke biye masa baya.
Muller da ya rasu a 2021, ya jefa kwallaye 14 a 1970 da 1974 a gasar ta cin kofin duniya.
Dan wasan Jamus da Bayern Munich Thomas Muller ne dan wasan dake buga kwallo kuma ya jefa kwallaye 10 a gasar kwalloon kafa ta duniya a wasanni 16 da ya buga. Muller na bukatar kwallaye 7 don ya zama a kan gaba wajen jefa kwallaye a gasar tare da haura Klose.
Dan wasan Portugal Cristiano Ronaldo mai shekaru 37 da na Ajantina Linel Messi mai shekaru 35 ba su jefa kwallaye sun kai 10 ba, kuma watakika Qtar 2022 ne za su zama gasar cin kofin duniya ta karshe da Ronaldo da Messi za su halarta.