Hankali zai koma kan 'yan Afirka da ke taka leda manyan kungiyoyin duniya yayin da aka fara gasar lig na kasashe:Hoto/Reuters

Yayin da kungiyoyin kwallon kafa a Turai da ma sauran nahiyoyi ke shirin fara yakin neman cin kofi na lig-lig da Kofin Zakarun Turai, ga wasu ‘yan wasan Afirka da za su wakilci kungiyoyinsu a filin daga:

Sadio Mane

Dan wasan Senegal din wanda bai samu ya ci gaba da nasarorin da ya yi a gasar Firimiyar Ingila a lokacin da ya koma gasar Bundeliga ta Jamus a kakar da ta gabata ba, zai fito don karyata zaton masu suka a lokacin da aka fara yakin neman cin kofin Lig din Saudiyya ranar Juma’a.

Duk da cewa ya zura kwallo bakwai a wasannin gasar Bundesliga sama da 20 da ya buga, sabon kocin Bayern Munich, Thomas Tuchel ya sauke shi.

A wani bidiyo ya yi ta yawo a shafukan sada zumunta, Mane ya ki ya yi magana da wasu ‘yan jaridar Jamus yana mai cewa: “kuna kashe ni kullum kuma kuna so in yi muku magana? Haba dai!”

Sadio Mane zai nuna wa duniya cewar shi gwarzo a fagen tamaula idan aka fara gasar lig din Saudiyya

Mane na fatan cewa zai ji dadin zama a sabon kulob dinsa na Al-Nassr, kuma zai iya yin abin da ya fi iyawa, wato zura kwallaye a raga tare samar da damarmakin zura kwallaye a raga.

Wilfred Zaha

Nesa daga Gasar Firimiyar Ingila inda ya fara taka leda, Wilfred Zaha, zai fara sabuwar tafiya a lig din Turkiyya a kakar 2023/2024.

Dan wasan Ivory Coast din ya rattaba hannu kan yarjejeniya da kungiyar Galatasaray a watan Yulin nan.

Wilfred ya shafe sama da shekara 10 yana dan wasan gaba a kungiyoyin Crystal Palace da Manchester United a Gasar Firimiyar Ingila.

Wilfred dan wasan gaba ne mai barzana ga 'yan wasan baya:Hoto/ Reuters

A lokacin da aka fara wasannin kakar bana ranar Juma’a, Zaha zai kawo kwarewarsa da ya samu a shekarun da ya yi a Ingila a yunkurin zakarun Turkiyyar na kare kambunsu tare da fafatawa a Gasar Zakarun Turai wanda aka riga aka fara.

Mohamed Salah

Dan wasan da ake yi wa lakabi da Sarkin Masar, ya ce ya ji takaicin yadda kungiyarsa ta kasa samun damar shiga Gasar Zakarun Turai ta wannan kakar.

Amma shararren dan wasan Liverpool din ya shirya mancewa da abin takaicin da ya faru a kakar bara domin neman abin da ya ce shi ne abu mafi karancin da ya kamata kungiyarsa ta samu, wato shiga Gasar Zakarun Turai.

Mohamed Salah daya ne daga cikin 'yan wasan da suka fi zura kwallaye a raga a kungiyar Liverpool: Hoto/Reuters

Kungiyar za ta dogara da kwarewarsa a lokacin da aka fara fafatawa a Gasar Firimiyar Ingila ta kakar 2023/2024 ranar Juma’a.

Taiwo Awoniyi

Daya daga cikin ‘yan wasan da Nottingham Forest ta saya domin ta tsira a Gasar Firimiyar da ta shiga a kakar da ta gabata, shi ne dan wasan Nijeriya Taiwo Awoniyi.

Kuma bai bai wa kungiyar kunya ba don ya zura mata kwallo goma a raga, ciki har da kwallon nan da ya sa kungiyarsa ta yi nasara kan Arsenal, lamarin da ya sa kungiyar ta tabbatar da ci gaba da kasancewarta a Gasar Firimiyar Ingila yayin da take da wasa dayan da za ta buga a gasar.

Taiwo Awoniyi ne ya zura kwallo a ragar Arsenal a wasan da Nottingham Forest ta doke Arsenal:Hoto/Reuters

Idan aka fara fafatawa a Gasar Firimiyar Ingila ranar Juma’a, tsohon maginin zai kasance daya daga cikin ginshikan da Nottingham Forest za ta dogara da su wajen tabbatar da cewa ta ci gaba da kasancewa a Gasar Firimiyar a sabuwar kakar tare da ganin cewa ta karkare kakar a matakin da ya fi matakinta na bara.

Zaidu Sanusi

Dan wasan bayan Nijeriya Zaidu Sanusi, ya taimaka wa FC Porto ta lashe Gasar Lig din Portugal a kakar 2021/2022 da wani kwallon da ya zura raga a karshen kakar.

Kungiyar kuma ta zo ta biyu a Gasar Lig din kakar da ke biye da ita, kakar 2022/2023, bayan Benfica ta lashe gasar.

Zaidu Sanusi dan wasan bayan tawagar Super Eagles ta Nijeriya ne:Hoto/Reuters

Dan wasan na tawagar Super Eagles din Nijeriya zai kasance daya daga cikin ‘yan wasan da za su taimaka wa Porto wajen kwato kambunsu daga hannun Benfica tare da kaddamar da yunkurinsu na taka rawar gani a Gasar Zakarun Turai a sabuwar kaka.

Sadiq Umar

Tauraron dan wasan gaban Nijeriya Sadiq Umar, ya haskaka a Gasar Laliga Smartbank a kakar 2021-2022 a lokacin da ya taimaka wa Almeria ta samu shiga babbar gasar lig din Sifaniya wadda ake ce wa Laliga Santander.

Wannan ya ja hankalin Real Sociedad wadda dan wasan gabanta Alexandar Isak ya koma taka leda a Newcastle United a Gasar Firimiyar Ingila.

Sadiq Umar (Jololo) zai koma taka leda bayan jinyan da ya sa ya rasa buga wasa da yawa a kakar da ta gabata:Hoto/Reuters

Real Sociedad ta sayo Sadi Umar, amma ya yi jinya mai tsawo bayan ya ji ciwo, lamarin da ya sa bai samu ya taka leda a yawancin wasannin kakar da ta gabata ba.

Dan wasan da aka fi sani da Jololo a Kaduna inda ya taso, zai fito ya nuna wa jama’a cewar irin rawar da ya taka a Almeria ba sa’a kawai ba ne a lokacin da Kakar Laliga ta 2023/2024 ta fara.

Samuel Chukwueze

Dan wasan Nijeriya, Samuel Chkukwueze, ya koma babbar kungiyar kwallon kafar nan ta Italiya, AC Milan, bayan tauraronsa ya haskaka a kungiyar kwallon kafa ta Villarreal da ke Sifaniya.

Chukwueze ya yi rawar gani a lokacin da yake kungiyar Villareal ta Sifaniya: Hoto/Reuters

Ana sa ran dan wasan Super Eagles din da ya koma taka leda a AC Millan zai taka muhimiyyar rawa a fafatawar da kungiyar za ta yi a gasar Seria A da gasar Zakarun Turai a kakar bana.

Achraf Hakimi

Achraf, wanda yake daya daga cikin ‘yan tawagar Moroko da suka kafa tarihi na kasancewa kasar Afirka ta farko da ta fara kai matakin daf da na karshe a gasar kwallon kafa ta duniya, yana taka leda a kungiyar Paris Saint-Germain (PSG) a gasar Ligue 1.

Achraf Hakimi na cikin 'yan nahiyar Afirkan da za su ja hankali a gasar lig din Faransa: Hoto/Reuters

Yana daya daga cikin 'yan wasan da ke jagorancin kokarin PSG na kare kambunta bayan ta lashe gasar Ligue1 a kakar da ta gabata.

Victor Osimhen

Voctor Osimhen shi ne dan wasan gaban Nijeriya wanda ya taimaka wa Napoli lashe gasar Seria A a karon farko cikin shekara 33 bayan ya zura kwallo 26 cikin raga a kakar bara.

Duk da cewa rahotanni sun ce kulob da dama na son su saye shi, da alama dan wasan da ya lashe kyautar takalmin zinare a gasar kwallon duniya ta ‘yan kasa da shekara 17 a shekarar 2015 zai ci gaba da murza leda a Italiya a kakar 2023/2024.

Osimhen yana da farin jini a birnin Naples na Italiya sosai sakamakon rawan da ya taka a nasarar da Napoli ta yi a gasar Seria A

Ya shirya domin ya ci gaba da zura kwallaye a ragar abokan hamayyan Napoli yayin da kungiyar ta fara neman lashe gasar Seria A da kuma taka rawar gani a gasar zakarun Turai a wannan kakar.

Andre Onana

Golan tawagar Indomitable Lions ta Kamaru, Andre Onana, ya koma Manchester United bayan ya taimaka wa kungiyarsa Inter Milan, ta zo ta biyu a Gasar Zakarun Turai a kakar da ta gabata.

Bayan ya maye gurbin David de Gea, ana tsammanin golan na Kamaru ya taka rawar gani a kungiyar Red Devils.

Andre Onana ne ya maye gurbin David de Gea a Manchester United: Hoto/Reuters

Onana ya shirya domin ya yi aikin da ya ce shi ya dade yana sha’awar yi ta yadda kungiyarsa ba za ta yi kewar tsohon mai tsaron gidanta David de Gea ba.

Vincent Abubakar

Wani dan Afirka da mutane za su zura wa ido shi ne Vincent Aboubakar. Vincent ya taka rawar gani a kakar da ta gabata a kulob dinsa na Turkiyya, Besitktas.

Duk da cewar kungiyarsa ta karkare kakar da ta gabata a mataki na uku a teburin lig din Turkiyya, kasa da Galatasaray da Fernabache, zai kasance daya daga cikin ‘yan wasan da kungiyar ta Turkiyya za ta dogara a kai wajen neman cin kofin lig din kasar.

Vincent Aboubakar ya shirya tsaf don tinkarar abokan hamayyar Besiktas: Hoto/Reuters

Irin rawar da ya taka a kakar da ta gabata ta nuna cewa zai iya taimaka wa kungiyarsa wajen zura karin kwallaye a ragar abokan gaba a sabuwar kaka.

Kalidou Koulibaly

Kalidou Koulibaly daya ne daga cikin taurarin kwallon kafa da suka koma Saudiyya daga Turai.

Dan wasan bayan na Senegal wanda ya koma Al Hilal ta Saudiyya daga Chelsea zai taka rawar gani a fafatawar da kungiyar za ta yi a wannan kakar.

Khalidou Koulibaly na cikin manyan 'yan wasan da suka bar Turai domin koma taka leda a lig din Saudiyya: Hoto/Reuters

Tsohon tauraron na Chelsea zai kasance daya daga cikin taurarin da za a zura wa ido a Lig din Saudiyya a kakar da za a fara ranar Juma’a.

TRT Afrika