Duniya
Rahotanni na cewa masu shiga tsakani sun samu ci-gaba a tattaunawar tsagaita wuta a Gaza, amma har yanzu ba a cim ma matsaya ba
Qatar da Amurka da Masar suna wani gagrumin yunƙuri na ganin an cim ma matsaya don dakatar da yaƙin da Isra’ila take yi a Gaza da kuma sakin ragowar mutanen da aka yi garkuwa da su kafin Joe Biden ya bar ofis.Duniya
Isra'ila ta kai samame ofishin Aljazeera a Ramallah, ta ba da umarnin a rufe shi.
Umarnin ya biyo bayan wani irinsa da ba a saba gani ba da aka bayar a Mayu, inda 'yan sanda suka mamaye inda tashar ke aiki a Gabashin Birnin Kudus, suka ƙwace kayayyaki, suka hana watsa shirye-shiryenta a Isra'ila suka toshe shafukanta naa intanet.Duniya
Sojojin Isra'ila sun ce an yi musayar wuta da dakarun Masar
Yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza, ya shiga rana ta 234 inda aka kashe akalla mutum 35,984 - kashi 70 jarirai ne da yara da mata - an raunata sama da 80,643 yayin da ake fargabar sama da mutum 10,000 na karkashin baraguzan gine-ginen da aka rusa.Duniya
Taron Bahrain na iya bayar da damar ƙalubalantar afka wa Gaza da Isra'ila ta yi
Salon kalaman ƙasashen Larabawa ya sauya tun watan Nuwamban bara, in ji mai nazari ɗan ƙasar Kuwait, Zafer al-Ajmi, yana mai cewa akwai yiwuwar bayanin bayan Taron Larabawa da za a fitar ya haɗa da matakan da za a ɗauka kan yaƙin Isra'ila a Gaza.Türkiye
Bai kamata ƴan ba-ni-na-iya su shigo da matsalolinsu Gabas ta Tsakiya ba: Turkiyya
Babban jami'in diflomasiyyar Turkiyya Hakan Fidan a wata ganawa da manema labarai tare da takwaransa na Qatar Sheikh Abdulrahman Al Thani, ya yi gargadin yiwuwar rikici ya mamaye yankin Gabas ta Tsakiya, wanda ya taso sakamakon yakin Isra'ila a Gaza.
Shahararru
Mashahuran makaloli