Turkiyya da sauran kasashen yankin Gabas ta Tsakiya ba sa son wasu kasashen waje su kawo nasu rigingimu a yankin, Ministan Harkokin Wajen Turkiyya ya yi furucin a cikin fargabar barkewar tashin hankali biyo bayan harin makami mai linzami da Iran ta kai wa Isra'ila.
Hakan Fidan ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin wani taron manema labarai tare da takwaransa na Qatar Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani a Doha, ya ce "Muna ta nanata cewa matakin na Isra'ila zai haifar da yaƙi a yankin.
"Mu a matsayinmu na kasashen yankin, ba ma son wasu ƴan ba-ni-na-iya su kawo nasu rikice-rikicen ba a wannan yanki," in ji shi.
Fidan ya jaddada cewa Firaiministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya yi ta kokarin janyo yankin cikin yaƙi domin tabbatar da kamun ludayinsa, a duk lokacin da yake samun goyon baya mara sharadi daga Ƙasashen Yammacin Duniya.
Babban jami'in diflomasiyyar, wanda kwanan nan ya tattauna da shugaban ofishin siyasa na kungiyar Hamas Ismail Haniya a Qatar, ya nanata cewa, Turkiyya na kokarin ganin an cimma matsaya guda biyu ta hanyar diflomasiyya.
Fidan ya ce "Jami'an Hamas sun gaya min cewa za su kawar da reshensu na masu dauke da makamai kuma su ci gaba da zama jam'iyyar siyasa idan aka kafa kasar Falasɗinu."
Muhimmiyar rawar da Turkiyya ke takawa
A nasa bangaren, Al-Thani ya ce Qatar na gudanar da harkokin diflomasiyya a Gaza, ya kuma jaddada cewa, rawar da Turkiyya ke takawa wajen warware rikicin na da matukar muhimmanci.
Gaza na fama da hare-haren Isra’ila tun ranar 7 ga Oktoba, 2023, lokacin da Hamas ta kashe Isra’ilawa sama da 1,200 a wani farmaki da suka kai kan iyaka.
Hare-haren na Isra'ila ya zuwa yanzu sun kashe Falasdinawa sama da 34,000 tare da jikkata wasu kusan 77,000.
Yakin da Isra'ila ke yi a Zirin Gaza na Falasdinu ya jefa kashi 85 cikin 100 na al'ummar yankin gudun hijira a cikin mawuyacin hali sakamakon karancin abinci, ruwan sha mai tsafta, da magunguna, yayin da sama da kashi 60 cikin 100 na ababen more rayuwa na yankin suka lalace, a cewar MDD.
Ana tuhumar Isra'ila da laifin kisan kiyashi a Kotun Duniya. Wani hukunci na wucin gadi da aka yanke a watan Janairu ya umarci Tel Aviv da ta dakatar da ayyukan kisan kiyashi tare da daukar matakan tabbatar da cewa ana ba da taimakon jinƙai ga fararen hula a Gaza.