Karo na farko kenan da ƙasashen yankin suka taru waje guda tun bayan taron musamman na Riyadh, babban birnin maƙociyar Bahrain a watan Nuwmaban bara wanda ya haɗa da shugabannin ƙasashe 57 na Ƙungiyar Haɗin Kan Ƙasashen Musulmi da ke da hekwata a birnin Jeddah. / Hoto: Reuters Archive

Shugabannin ƙasashen Larabawa na gudanar da taro a Bahrain wanda babban batun tattaunawa shi ne kisan kiyashin da Isra'ila ke yi a Gaza wanda ake ta yi ba tare da tsagaita wuta ba a yayin da bangaren Falasdinu ke cutuwa, taron na iya sanar da matakan uƙuba na tattalin arziki da siyasa a kan Isra'ila.

Domin halartar taron na ranar Alhamis, shugabannin kasashen a ranar Laraba sun fara sauka a Manama babban birnin Bahrain, inda aka maƙala tutocin ƙasashe mambobin Ƙungiyar Hadin Kan Ƙasashen Larabawa su 22.

Karo na farko kenan da ƙasashen yankin suka taru waje guda tun bayan taron musamman na Riyadh, babban birnin maƙwabciyar Bahrain a watan Nuwmaban bara wanda ya hada da shugabannin kasashe 57 na kungiyar Hadin Kan Kasashen Musulmai da ke da hedkwata a birnin Jeddah.

A wajen taron, shugabanni sun la'anci 'munanan' ayyukan Isra'ila a Gaza amma sun ƙi fitar da wata uƙuba ta siyasa ko tattalin arziki don kalubalantar kasar duk da karuwar bacin rai da nuna goyon baya ga Falasdinawa da ake samu a duniya baki daya.

Wannan abu na iya sauya wa a yanzu saboda yadda duniya ke goyon bayan ganin an warware rikicin ta hanyar kafa kasashe biyu wanda tun da jima wa kasashen Larabawa suka bayar da shawarar yin hakan, in ji mai nazarin dan kasar Kuwait, Zafer al Ajmi.

Ra'ayin jama'a a yammacin duniya 'ya karkakata sosai ga goyon bayan Falasdinawa da cire rashin adalcin da ake yi musu' tun bayan kirkirar Isra'ila a kasar Falasdinawa shekaru 70 da suka gabata.

A yayin da hakan ke faru wa, Isra'ila ta gaza cimma burinta na yaƙi ciki har da kakkaɓe Hamas, tana ta gwabza yakin da ya shiga wata na takwas, in ji shi.

Ya zuwa yanzu Isra'ila ta kashe Falasdinawa 35,233, mafi yawansu fararen hula, kuma mamayar ta Isra'ila ta janyo mummunan karancin abinci da barazanar yunwa.

Sauyin 'kalami'

Kusan mutum 600,000 ne suka gudu daga garin Rafah na kudancin Gaza, kamar yadda MDD ta bayyana, wajen da Isra'ila ke cear tana bibiyar gyauron Hamas ne a yankin.

Domin kalubalantar wanan mataki, tare da yadda mai shiga tsakanin Qatar ke bayyana tattaunawar sulhu da musayar fursunoni a matsayin lamarin da aka dakatar, "salon muryar kasashen Larabawa ya sauya" in ji Ajm, yana mai cewar akwai yoiwuwar matakan da za a dauka a ranar Alhamis su hada da kalubalantar Isra'ila.

Sakon da za a fitar zai yi karfi musamman yadda zia zo daga Bahrain, daya daga cikin kasashen yankin Gulf da suka sasanta alakarsu da Isra'ila a 2020, karkashin shiga tsakanin Amurka da sunan 'Abraham Accords'.

Baya ga batun mamaya da Isra'ila ta yiwa Falasdinawa, ana sa ran shugabannin Larabawan za su tattauna kan rikicin Sudan, Libiya, Yaman da Siriya, inda kuma Shugaban Siriya Bashar Al-Assad zai halarci taron bayan dawo wa kungiyar a shekarar da ta gabata.

Hare-Haren mayakan Houthi a Tekun Maliya kan jiragen ruwa na dakon kaya, wanda suka ce na da manufar nuna goyon baya ga Falasdinawa a Gaza, na iya zama wani bangare na batutuwan da za a tattauna, in ji mai nazari kuma dan jaridar kasar Bahrain Mahmeed al-Mahmeed.

Bahrain ta bi sahun ƙwancen soji na yaƙi a teku da Amurka ta shirya don ƙalubalantar hare-haren.

Mahmeed ya ce "muhimmancin wadannan hanyoyi na teku ba na kasashen yankin kadai ba ne, sun shafi tattalin arzikin duniya baki daya."

TRT World