Isra'ila ta daɗe tana rashin jituwa tsakaninta da Al Jazeera, inda ta zarge ta da nuna son kai ga al'ummar kasar. / Hoto: Reuters

Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu a ranar Lahadi ya bayyana cewa gwamnatinsa ta yi ƙuri’a inda ta amince ta rufe duka ofisoshin kafar watsa labarai ta Al Jazeera a ƙasar.

Netanyahu ne ya sanar da hakan a wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na X, sai dai bai bayyana sauran bayanai da suka ƙunshi ko yaushe dokar za ta soma aiki ba haka kuma babu bayani kan rufewar ta har abada ce ko da wucin-gadi ce.

Har ila yau, Isra'ilar ta yi barazanar saka ƙafar wando ɗaya da Qatar, wadda ke da tashar, a daidai lokacin da gwamnatin ta Doha ke taka muhimmiyar rawa a kokarin shiga tsakani domin dakatar da yakin Gaza.

Isra'ila ta daɗe tana rashin jituwa tsakaninta da Al Jazeera, inda ta zarge ta da nuna son kai ga al'ummar kasar.

Al Jazeera na daya daga cikin kafafen yada labarai na kasa da kasa da ke ci gaba da zama a Gaza a tsawon yakin da ake yi, inda suke yada hotunan zubar da jini na hare-hare ta sama da cunkoson asibitoci tare da zargin Isra'ila da kisan kiyashi.

Haka kuma Isra’ilar na zargin Al Jazeerar da haɗa kai da abokiyar gabarta wato Hamas.

AA