Ƙungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas da Isra'ila sun cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta da nufin dakatar da yaƙin da Isra'ila ke yi a Gaza tare da musayar fursunoni, in ji Sheikh Mohammed bin Abdulrahman Al Thani, mai shiga tsakani na Qatar kuma Ministan Harkokin Wajen ƙasar.
Ya faɗa a ranar Laraba cewa matakin farko na tsagaita wuta na kwanaki 42 zai fara aiki ne daga ranar 19 ga watan Janairu.
Yarjejeniyar dai ta zo ne bayan shafe makonni ana tattaunawa a babban birnin Qatar, an yi alƙawarin kawo ƙarshen yaƙin kisan ƙare dangi da Isra'ila ke yi a Gaza, da sakin Isra'ilawan da aka yi garkuwa da su a matakai, da sakin ɗaruruwan Falasdinawa daga gidajen yarin Isra'ila tare da bai wa dubban ɗaruruwan mutanen da suka rasa matsugunansu a Gaza damar komawa abin da ya yi saura na gidajensu.
Har ila yau, za a ba da damar shigar da taimakon jin ƙai da ake buƙata yankunan Falasɗinawa da aka ɗaiɗaita.
A halin yanzu dai Isra’ila na tsare da fursunonin Falasdinawa sama da 11,000, yayin da aka yi ƙiyasin cewa ana tsare da Isra’ilawa 98 a Gaza.
Isra'ila ta dakatar da yakin Gaza na wani ɗan lokaci tsawon kwanaki 6 a watan Nuwamban 2023, wanda ya kai ga sakin fursunonin Isra'ila 50 da aka yi garkuwa da su a Gaza da kuma fursunoni 150 na Falasɗinawa da aka tsare a Isra'ila.
Sai dai ba a iya tsawaita wa'adin tsagaita wutar ba, saboda Isra'ila ta ci gaba da yaƙin da take yi kan yankin da aka yi wa ƙawanya, kuma Netanyahu ya ci gaba da yin kalaman yaƙi.
Hatta waɗanda suka san abin da ke faruwa na Isra'ila sun zargi Firaminista Benjamin Netanyahu da murƙushe ƙoƙarin da aka yi na cim ma cikakkiyar yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza, a daidai lokacin da yake shirin janye sojoji daga yankin da aka yi wa ƙawanya.
Da dada daga 'yan siyasa da shugabannin soja a Isra'ila sun nuna cewa Netanyahu yana tsawaita yaƙin ne don ci gaba da riƙe matsayinsa na siyasa.
Isra'ila ta kashe sama da mutane 46,700 a ci gaba da kai hare-hare na kisan kiyashi a Gaza, a cewar jami'an kiwon lafiya na Falasɗinu, tare da lalata mafi yawancin yankin, sannnan aka tilasta wa akasarin mutanenta yankin barin gidajensu.
A watan Nuwamba 2024, Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta ƙasa da ƙasa ta ba da sammacin kama Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu da tsohon Ministan Tsaro Yoav Gallant kan laifukan yaƙi da cin zarafin bil'adama a Gaza.
Har ila yau Isra’ila na fuskantar shari’ar kisan kiyashi a kotun ƙasa da ƙasa kan yaƙin da take yi a yankin.