Emine Erdogan ta buƙaci ƙasashen duniya su tunkari wannan tashin hankalin da ke faruwa. / Hoto: AA

Uwargidan shugaban Turkiyya Emine Erdogan ta jaddada cewa irin zaluncin da Isra'ila ke yi a Falasdinu ya zama "kisan kiyashi a zamanance," kuma wani bangare ne na aniyar da suke da ita ta shafe al'umma baki daya da al'adunsu daga tarihi.

"Abin da muke gani a Falasɗinu ba yaki ba ne, ƙoƙari ne na aiwatar da tsarin duniya wanda kawai mafi karfi da ƙwarewa a zalunci zai iya rayuwa, yayin da sauran rayuka ba su da muhimmanci," in ji Erdogan a cikin wani jawabi da ta gabatar a birnin Doha na Qatar.

Ta buƙaci ƙasashen duniya su tunkari wannan tashin hankalin da ke faruwa.

Yayin da take la’akari da cewa fararen hula 44,000, ciki har da yara 16,000, aka kashe a Gaza a lokacin hare-haren Isra'ila, kuma an lalata muhimman ababen more rayuwa daga asibitoci zuwa makarantu da gidajen marayu, Erdogan ta saka ayar tambaya kan “kare kai” da Isra’ila ke fakewa da shi.

“Wa Isra’ila ke kare kanta daga shi ta hanyar sakin fiye da tan 70,000 na bama-bamai a cikin Gaza, inda rabin jama’ar wurin suna ƙasa da shekara 18?”

TRT World