Karel ya ce kamfaninsa na aiki a ko inna a  faɗin duniya yayin da motocinsu ke aiki a cikin ƙasashe sama da 22 a nahiyoyi huɗu daban-daban. / Hoto: AA  

Kamfanin tsaro na Turkiyya Nurol Makina ya ƙera motoci 400 masu sulke don ba da gudunmawar tsaro ga Qatar.

Babban kamfanin da ke ƙera motoci masu sulke ya samu halartar taron Doha kan baje kolin fasahohin tsaron ruwa na duniya karo na takwas (DIMDEX 2024) a Qatar, inda ya nuna sabuwar motarsa mai suna ‘Ejder Yalcin,’ wacce Sojojin Qatar ke amfani da irinsa.

Anil Karel mataimakin babban manajan Kamfanin Nurol Makina ya shaida wa kamfanin dillacin labaran Turkiyya Anadolu Agency cewa sun fara kwangilar samar da ababen hawan ne don biyan bukatun sassan tsaro da sojoji da daban-daban a Qatar a shekarar 2017.

Ya ce sun hada kai da kamfanin tsaro na Qatar Barzan Holdings, kuma a halin yanzu, akwai motoci sama da 400 da ke aiki a sassa daban-daban a Qatar.

Karel ya ƙara da cewa, ba motoci kadai suke ƙerawa ba har da tsarin samar da mafita, saboda an ƙera motocin ne har da makamai da kuma tsarin da suka hada gwiwa da wani kamfanin tsaro na Turkiyya Aselsan.

Yana mai cewa: “Sun gamsu da motocin Ejder TOMA (Intervention Vehicle Against Social Incidents), sun sayi motocin ne musamman don Ggasar Cin Kofin Duniya, saboda yana da matukar amfani wajen tabbatar da tsaro.

"Baya ga wannan, sauran bangarorin rundunar sojojin ma sun gamsu da motocin da suke amfani da su."

A shekarar 2023 ne kamfanin ya bude cibiyar kula da gyara, wanda ya kunshi kerawa d ayyuka da horarwa da kuma tsarin mika wa mai amfani, in ji shi.

Ya bayyana cewa, wannan aiki shi ne mafi girma da Turkiyya ta rattaba hannu a bangaren kasafin kudi da lambobi, kuma har yanzu akwai wasu motoci da ake jira a kai su nan gaba.

Karel ya ce kamfaninsa na aiki a ko ina a faɗin duniya yayin da motocinsu ke aiki a cikin ƙasashe sama da 22 na nahiyoyi huɗu daban-daban.

TRT Afrika