Ministan Tsaron Isra'ila Yoav Gallant ya ce yanayin da ake ciki a Gaza yana haifar wahukumomin Isra'ila babban kalubale. Hoto:Reuters

Ministan Tsaron Isra'ila Yoav Gallant ya yi kira da a yi "rangwame mai radadi" don sako mutanen da aka yi garkuwa da su a Gaza.

“Ba kowace manufa ce za a iya cim ma wa ta hanyar soja kadai ba; ƙarfi ba shi ne amsar komai ba," in ji Gallant a ranar tunawa da waɗanda aka kashe a harin Hamas a bara.

Ya ƙara da cewa "Lokacin da ya dace mu cika aikinmu na dawo da waɗanda aka yi garkuwa da su gida, za a buƙaci rangwame mai raɗaɗi".

Ministan tsaron ya amince cewa yaƙin Gaza da Isra'ila ke ci gaba da yi yana da sarƙaƙiya kuma ba a taɓa ganin irinsa ba a ƙalubalen da take fuskanta.

"A wannan shekara, mun kashe abokan gabanmu kuma mun haifar da sabon yanayin tsaro a tare da mu, amma asarar da ake yi ta yi yawa," in ji shi, yana mai cewa Isra'ila ta samu "nasarar da ba a taɓa gani ba" a kowane ɓangare.

"A kudanci, Hamas ba ta aiki a matsayin rundunar soji. A arewacin ƙasar, ƙungiyar Hezbollah na ci gaba da fama da hare-hare iri-iri, tare da rugujewar tsarin shugabancinta, aka lalata mafi yawan makamanta masu linzami, an kuma kora dakarunta daga kan iyaka."

Kalaman Gallant sun zo ne a daidai lokacin da masu shiga tsakani na Isra'ila ke shirin komawa tattaunawa a Qatar domin yiwuwar ƙulla yarjejeniyar musayar fursunoni da Hamas.

Yunƙurin shiga tsakani

Isra'ila ta yi ƙiyasin cewa har yanzu akwai fursunoni 101 da kungiyar Hamas ke rike da su a Gaza, wadanda ake kyautata zaton Isra'ila ta kashe wasu daga cikinsu sakamakon hare-haren wuce gona da iri a yankin.

Yunƙurin shiga tsakani da Qatar da Masar da Amurka suka jagoranta na cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da yarjejeniyar musayar fursunoni tsakanin Isra'ila da Hamas ya ci tura, sakamakon ƙin amincewar Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu a kawo karshen yaƙin.

Sojojin Isra'ila na ci gaba da kai munanan hare-hare a Gaza, duk da wani ƙudurin Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya da ya buƙaci a tsagaita wuta cikin gaggawa.

Kusan mutane 43,000 ne aka kashe tun fara yaƙin, akasari mata da yara, yayin da wasu sama da 100,000 suka jikkata, a cewar hukumomin lafiya na yankin.

Hare-haren na Isra'ila sun raba kusan ɗaukacin al'ummar yankin da gidajensu, a daidai lokacin da ake ci gaba da killace yankin, abin da ke haifar da mumunan ƙarancin abinci da tsaftataccen ruwan sha da magunguna.

Har ila yau Isra'ila na fuskantar shari'ar kisan kiyashi a kotun kasa da kasa kan abin da ta ke aikatawa a Gaza.

TRT World