Fidan ya bayyana cewa Turkiyya za ta iya karɓar wasu daga cikin fursunoni Falasɗinawa da Isra'ila ta saki bayan cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas. / Hoto: AA

Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya bayyana cewa Ankara na "adawa baki ɗaya" da shawarar da Shugaban Amurka Donald Trump ya bayar na korar Falasɗinawa daga Gaza domin su koma wasu ƙasashen.

Ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a yayin wani taron manema labarai na haɗin gwiwa shi da takwaransa na Qatar Mohammed bin Abdulrahman Al Thani a Doha, inda Fidan ya bayyana cewa wannan shawarar ta saɓa wa dokokin bil'adama.

Ya kuma jaddada cewa ya kamata kowa ya nuna ƙin goyon baya game da wannan shawarar inda kuma ya ƙara da cewa Ankara na goyon bayan abin da aka ayyana a 'yan kwanakin nan game da Falasɗinaw a birnin Alkahira na Masar.

Fidan ya bayyana cewa Turkiyya za ta iya karɓar wasu daga cikin fursunoni Falasɗinawa da Isra'ila ta saki bayan cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra'ila da Hamas.

"Shugaban ƙasarmu ya bayyana cewa a shirye muku mu karɓi wasu daga cikin Falasɗinawan da aka saki... domin goyon bayan wannan yarjejeniyar. Turkiyya tare da wasu ƙasashe za ta ci gaba da yin iya ƙoƙarinta ta yadda wannan yarjejeniyar tsagaita wutar za ta ɗore," kamar yadda ya bayyana a yayin wani taron manema labarai wanda aka gudanar a birnin Doha.

Fidan na gudanar da wata ziyara ta kwana biyu a Qatar wadda ya fara a ranar Lahadi.

TRT World