An cire Tobi Amusan daga Nijeriya a zagayen kusa da ƙarshe na tseren mita 100 na mata a gasar Olympics ta kaka wadda ake yi a Faransa. / Hoto: AFP

Ministan wasanni na Nijeriya ya bayyana rashin nasarar ƙasar a gasar Olympics ɗin 2024 a matsayin "bala'in Paris" inda ya ɗora alhakin hakan kan hukumomin kula da wasanni.

"Dole ne mu yi duk mai yiwuwa domin guje wa afkuwar bala'in na Paris a nan gaba kuma idan hakan zai haifar da sake duba yadda aka zabi mutane don jagorantar kungiyoyin wasanninmu, za a yi hakan," in ji John Enoh a wata sanarwa a ranar Asabar.

Wani fitaccen abu da Nijeriya ta yi a gasar ita ce yadda aka cire ta a zagayen daf da na kusa da na ƙarshe a wasan kwando tsakaninta da Amurka bayan an ja daga.

Wadda ke riƙe da kambun tseren mita 100 ta duniya Tobi Amusan ba ta kai zagayen ƙarshe ba, inda Favour Ofili ita kuma ba ta kara a tseren mita 100 na mata ba bayan hukumomin wasanni na ƙasar ba su saka sunanta ba.

"Mun yi duk abin da muka yi a matsayin ma'aikata don shirya 'yan wasa yadda ya kamata da kuma ba su kowane tallafi na kudi amma abin takaici wasan nasu bai haifar da komai ba," kamar yadda sanarwar ministan ta bayyana.

Zaben hukumomin wasanni

Enoh ya bayyana cewa yadda aka cire 'yan Nijeriya a wurin gasar ya faru ne sakamakon "wasu abubuwa da yawa da suke buƙatar a mayar da hankali a kansu" inda kuma ya bayyana alamun yiwuwar gwamnati ta sa baki a zaɓen hukumomin wasannin.

"Zaɓen hukumar wasannin yana daf kuma zai kasance wata dama da za a samu waɗanda suka cancanta kaɗai domin jagorantar hukumomin wasannin daban-daban," a cewarsa.

Hukumomin wasanni a fadin duniya na samun ‘yancin kai daga gwamnatoci, inda a lokuta da dama tsoma bakinsu ke haifar da dakatarwa daga kasashen duniya, amma ministan na Nijeriya ya dage cewa kasarsa za ta tantance wadanda ke neman shugabancin hukumar.

Bayan shafe sama da mako biyu ana gudanar da gasar Olympics a Faransa, a ranar Lahadi za a kammala gasar.

TRT Afrika