Tun bayan da hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta fitar da jadawalin wasannin neman shiga gasar kwallon kafa ta duniya ne dai mutane suka fara tsokaci kan yadda fafatawar za ta kaya.
Mutane sun fi mayar da hankali kan gwabzawar da za a yi tsakanin Nijeriya da tsohon kocinta, Gernot Rhor wanda a halin yanzu shi ne mai horar da 'yan wasan Jamhuriyar Benin.
Nijeriya tana rukunin C ne tare da kasar Afirka ta Kudu da Jamhuriyar Benin da Rwanda da Lesotho da kuma Zimbabwe, kuma za ta fara wasan neman shiga gasar ne a watan Nuwamba.
Wasu manazarta na ganin Gernot Rhor zai yi amfani da wannan damar wajen daukar fansa kan Nijeriya wadda ta kore shi daga aikin koci a shekarar 2021.
Daya daga cikin masu wannan tunanin shi ne tsohon dan wasan gaban Nijeriya, Jonathan Akpoborie.
A hirarsa da jardiar Complete Sports, Akpoborie ya ce Gernot Rhor "zai kaddamar da yaki kan tawagar Nijeriya, kuma ina tsammanin hukumar kwallon kafar kasar za ta shirya tawagar don tunkarar fafatawar neman shiga gasar.
Ranar Alhamis ne dai hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta fitar da jadawalin yadda za a yi yakin neman shiga gasar kofin duniya wadda za a yi a kasashen Canada da Mexico da kuma Amurka a 2026.
Tawagar Nijeriya za ta buga wasanni goma a wasannin neman shiga gasar ta kofin duniya.
Nijeriya za ta yi wasanni biyu tsakanin 13 da 21 ga watan Nuwamban shekarar 2023, kuma za ta yi wasanni biyu tsakanin 3 da 11 ga watan Yunin shekarar 2024.
Sauran wasannin shidan kuma Nijeriya za ta fafata a cikinsu ne tsakanin watan Maris zuwa Oktoban shekarar 2025.
Wasa na 1,2 – Nuwamba 13-21 2023
Wasa na 3, 4 – Yuni 3-11 2024
Wasa na 5,6 – Maris 17-25 2025
Wasa na 7, 8 – Satumba 1-9 2025
Wasa na 9,10 – Oktoba 6-14 2025
Wasa na 10-18 2025 (Wasannin raba gardama)
Sanannun abokan hamayya
Baya ga kalubalen da Nijeriya za ta fuskanta wajen karawa da kasashe irin su Afirka ta Kudu a wannan yakin neman shiga gasar kofin duniya, tawagar Nijeriya za ta fuskanci wata matsala ta daban a wannan yakin.
Tsohon kofin Nijeriya, Gernot Rhor ne shi ne yake jagorantar tawagar kwallon kafa ta Jamhuriyar Benin.
Gernot Rhor tare da mataimakinsa, Tunde Adelakun (dan asalin Nijeriya) sun kasance jagororin tawagar ‘yan wasan Nijeriya zuwa 2021 lokacin da aka kore su.
Bayan hakan ne kasar Jamhuriyar Benin ta bas u aiki a matsayin ‘yan wasan jagororin tawagar Squirrels ta Benin.
Manazarta na ganin Gerenot Rhor da Tunde Adelakun za su yi kokarin tabbatar wa mahukuntan kwallon kafar Nijeriya cewa kuskure ne korar da aka yi musu a shekarar 2021.
San an fara yakin neman shiga gasar kafin a san irin barzanar da Gernot Rhor da tawagar Jamhuriyar Benin za su kasance ga tawagar Nijeriya.