A watan Yunin 2024 ne kwantiragin Mbappe za ta kare. Hoto/AA

Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint-Germain Nasser Al-Khelaifi ya bayyana cewa dole ne Kylian Mbappe ya saka hannu a sabuwar kwantiragi idan yana so ya ci gaba da zama a kulob din.

Tun a baya dai dan wasan gaban na Faransa mai shekara 24 ya bayyana cewa ba zai tsawaita kwantiraginsa ta wuce 2024 a kulob din ba sai dai ya nuna alamun cewa zai tsaya har kaka ta gaba.

“Matsayarmu a bayyane take. Idan Kylian na so ya tsaya, dole ya saka hannu a sabuwar kwantiragi. Ba za mu bar dan wasan da ya fi kowa iya taka leda a duniya ya tafi a kyauta ba. Ba zai yiwu ba,” in ji Khelaifi kamar yadda kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito.

“Ya ce ba zai tafi a kyauta ba, idan wani ne ya sauya masa ra’ayi wannan ba laifina ne ba.”

Wannan na nufin dole ne kulob din ya sayar da dan wasan a kasuwar hada-hadar ‘yan wasan kwallon kafa ko kuma su yi asarar shi ba tare da samun ko sisi ba idan kwantiraginsa ta kare a karshen kaka.

Mbappe ya soma taka leda a PSG inda ya taho daga Monaco a Agustan 2017 inda aka siye shi euro miliyan 180, inda a halin yanzu yana daga cikin ‘yan kwallon duniya da ake ji da su.

Dan kwallon na Faransa ya ci kwallo uku ga gasarsa a wasan karshe da kulob din ya buga na wasan cin kofin duniya duk da cewa Faransar ba ta yi nasara kan Argentina ba.

Dan wasan shi ne wanda ya fi kowa zura kwallo a raga a gasar Ligue 1 ta Faransa inda ya ci kwallo 29 da kuma saka kwallo 41 jumulla a wasanni 43 da ya buga .

AFP