A lokacin da take ganiyarta, Jean Sseninde ta shiga layin masu tsaron baya.
Saboda lokacin da ta yarda cewa "Afirka ta ba rungumi wasan kwallon kafar mata ba tukuna," kasancewa zai dauki lokaci kafin a yi maraba da tsohuwar 'yar wasan baya ta Crested Cranes da Queens Park Rangers.
Maganar da Sseninde ta yi cewa an bar Afirka a baya wajen bunkasa wasan kwallon kafar mata a jajiberin fara Gasar Cin Kofin Kwallon Kafar Mata ta Duniya ta 2023 a Australia da New Zealand a ranar 20 ga watan Yuni.
Kasashen Afirka hudu – Maroko da Zambiya da Afirka ta Kudu da kuma Nijeriya ne za su fafata a gasar a wannan karon, sai dai tsohuwar 'yar wasan Uganda ta ce ta yi amannar cewa lamarin ba zai zo da sauki ba idan ka yi la'akari da kasashen da za su fafata da su wadanda suka yi nisa ne a fagen kwallon kafar mata, idan ka kwatanta da "tafiyar hawainiyar" da nahiyar Afirka take yi dangane da kwallon kafar mata.
Watakila Sseninde tana da gaskiya. Lokacin da ta sauka a Ingila daga Uganda tana da shekara 20, cikin sauri ta fahimci cewa wasan kwallon kafar mata wani abu ne na daban.
"Na kadu lokacin da na ga yadda aka dauki kwallon kafar mata da muhimmanci a Ingila ta samu karbuwar da ana nuna ta a talabijin a lokacin, yayin mu kuma a Uganda ba wanda yake magana kan wasan," kamar yadda ta shaida wa TRT Afrika.
"Kuma na yi mamaki sosai bayan ganin yadda yara 'yan mata 'yan shekara hudu suna atisaye da yin abubuwa masu kayartawa a fili." Ingila ta ci gaba da kasancewa abin misali a fagen ci gaban kwallon kafar mata, inda take da tsari da kuma lig-lig.
Firimiyar Lig din mata wanda shi ne na biyu a daraja a duniya bayan Lig din Kwallon Kafar Mata na Amurka wanda shi ne na daya a daraja.
Akasin haka, Sseninde ta samu koci ne kawai lokacin da take makarantar sakandare, wato shekara hudu kafin samun nasararta, inda ta kulla yarjejeniya da kungiyar Charlton Athletic WFC a shekarar 2012.
"'Yan wasa da ba su kai ni shekaru ba sun fi iya dabarun wasa, kuma haka na matsawa kaina don koyo wadannan dabaru," in ji ta.
Shekara 10 bayan haka, Sseninde ta dawo gida Uganda don ta taimaki kwallon kafar mata. Sai dai yadda abin yake tafiyar hawainiya abin yana damunta. Ba kawai a Uganda ba, hatta sauran kasashen nahiyar.
"Manyan taurarin duniya wadanda suka fara kafinmu sun fi mu yin yaba," in ji Sseninde, wadda yanzu ta samu lasisin aikin koci da hukumar UEFA kuma ta kafa gidauniyar Jean Sseninde Foundation wadda take zakulo hazikan 'yan mata 'yan wasa a Uganda.
Matsayin da Afirka take kai
Jadawalin tawagogin kasashe 32 na Gasar Kwallon Kafar Mata ta Duniya bai yi wa kasashen Afirka adalci ba, inda kasahe kamar Nijeriya da Afirka ta Kudu da kuma wadanda suke zuwa gasar a karon farko kamar Maroko da Zambiya aka kai su karamin mataki kowannensu a rukuninsu.
Kasar Afirka ta Kudu ta lashe Gasar Cin Kofin Kwallon Kafar Mata ta Afirka, inda ta taka rawar gani a wasan, sai tawagar Nijeriya Super Falcons su ne suka fi gogewa. Nijeriya ta taba kai wa matakin gab da na kusa da na karshe a gasar a shekarar 1999, kuma za su fafata a gasar ne a karo na tara, ta fara fafatawa a gasar ne a shekarar 1991.
Kodayake kwarewa da gogewa suna da muhimmanci a matakin kololuwar wasan, Nijeriya ta tana tashe a 'yan shekarun nan.
A jadawalin FIFA, Nijeriya tana mataki na 40 ne wannan babbar mataki tsakanin kasashe hudu da za su wakilci kasashen Afirka a gasar, an jefa Super Falcons ne a rukunin B, inda za su kara da Kanada (ta bakwai a duniya) da mai masaukin baki Australia (ta 20 a duniya) da kuma Ireland (ta 22 a duniya).
Super Falcons suna da 'yan wasa kamar Asisat Oshoala, 'yar wasan gaba a tawagar mata ta kulob din Barcelona kuma tana cikin manyan 'yan wasa biyar da za su ja hankali a gasar.
Haka zalika akwai Onome Ebi wanda ita ce kyaftin din tawagar kuma sau shida tana halartar gasar — fiye da kowane dan wasa na miji ko mace daga Afirka a tarihin gasar. Akwai kuma 'yar wasan gaban Atletico Madrid Rasheedat Ajibade wacce ita ma tauraruwa ce.
Ana kiran tawagar Afirka ta Kudu Banyana Banyana wadda ita ce ta doke Super Falcons a Gasar Kofin Kwallon Kafar Mata ta Afirka a bara.
Sau biyar tawagar 'yan matan Afirka ta Kudun suna zama na biyu, sai sau biyu suna zama na uku a tarihin gasar.
A Gasar Kofin Kwallon Kafar Mata ta Duniya a 2019, Afirka ta Kudu ba ta wuce matakin rukuni ba. Desiree Ellis da tawagarta za su fafata ne da kasar da ta kai matakin wasan kusa da na karshe a 2019 wato Sweden, sai Argentina da kuma İtaliya a rukunin G, za a zuba ido ne a kan tauraruwar 'yar wasan Afirka ta Kudu Thembi Kgatlana a gasar.
Kuma 'yar wasan mai shekara 27 ita ce ta zura kwallo daya tilo a Gasar Kofin Duniya yayin wasansu da kasar Spain a shekarar 2019.
Maroko ce ta karbi bakuncin Gasar Kwallon Kafar Mata ta Afirka a 2022 kuma a karon farko kasar ta kai wasan karshe, inda Afirka ta Kudu ta doke su a wasan karshe.
Tawagar Marokon da ake kira The Atlas Lionesses tana samun ci gaba a kwallon kafar mata.
Tawagar 'yan matan Maroko tana matsayi na 72 ne a jadawalin FIFA kuma za su iya koyi da takwarorinsu maza wadanda suka kai wasan kusa da na karshe a Gasar Cin Kofin Duniya na Maza a 2022 a Qatar.
Amma an cika wa Maroko aiki bayan saka su a rukuni daya da Jamus wacce ta lashe kofin sau biyu ( ta biyu a duniya) da Koriya ta Kudu (ta 17 a duniya) da Colombia (ta 25 a duniya) a rukunin H.
'Yar wasan gaban Tottenham Hotspur Rosella Ayane kuma tana cikin manyan 'yan wasan gaban Maroko. Rosella wadda ta taba taka wa tagawar Ingila 'yan kasa da shekara 19 leda, kuma ta zura kwallaye bakwai a wasanni 15.
Tawagar 'yan matan Zambiya da ake kira Copper Queens ta fafata a wasannin Olympics na Tokyo a 2020, su ma ba kanwar lasa ba ne.
Barbra Banda ta jagoranci kasarta inda suka doke kasar Jamus da ci 3-2 – Jamus ta taba lashe gasar har sau biyu. Kuma wannan ya sa ana ganin Zambiya za ta iya yin wani abu a gasar.
Barbra, mai shekara 23, ta ja hankalin duniya ne lokacin da ta zama 'yar wasar da ta ci kwallaye uku-uku a wasa biyu a jere a wasannin Olympics.
Tawagar Copper Queens ita take mafi karamin mataki a duniya wato mataki na 77 kuma an saka ta ne a rukunin C tare da Spain (ta shida a duniya) da Japan (ta 11 a duniya) da kuma Costa Rica (ta 36 a duniya).
Sabon tsarin wasan
Sseninde ta shawarci kasashen Afirka da za su fafata a Gasar Kofin Duniyar da su tashi tsaye wajen yin amfani da wannan dama don bunkasa wasansu.
"Za ka iya cewa a wannan karon an fadada gasar, saboda haka za a yi da kowa. A daidai wannan lokaci dama ce da ya kamata tawagogin Afirka hudu da suke gasar su yi amfani da ita da basira," in ji tsohuwar 'yar wasan bayan.
"Za mu kalli 'yan wasan Afirka da dama da za su karfafa gwiwar 'yan mata masu son buga kwallon kafa, yayin da yawancin iyaye da masu daukar nauyi za su fahimci cewa kwallon kafar mata tana gurbi a Afirka."
Tsohuwar 'yan wasan Charlton Athletic ta kuma kira ga wadanda suka shahara a wasan daga Afirka da su koma gida don taimaka kananan 'yan mata su kai ga gaci.
Yayin da Sseninde take da kwarin gwiwa dangane da rawar da kasahen Afirka za su taka a Gasar Kofin Kwallon Kafar Mata ta Duniya, ta ce zuwa gaba za a iya samun kasar da za ta lashe gasar.
"Batun gaskiya, Afirka ba ta rungumi kwallon kafar mata ba sosai kamar yadda ya kamata, yawancin masu ruwa da tsaki suna ganin kamar alfarma suke yi wa kasar, abin da ke kawo cikas kan zuba jari a gasar."
Ta kafa misali da rikicin da ya kunna kai tsakanin Banyana Banyana da Hukumar Kwllon Kafar Afirka ta Kudu kan batun biyan kudi, abin sa ya jawo 'yan wasan suka kauracewa buga wasa da Botswana.
"Wannan abin takaici ne. Ana daukar korafin da 'yan wasa maza suke da muhimmanci, amma idan mata suka yi magana sai aka rika kallon abin da rashin da'a," in ji Sseninde.
"Ana saran mu karbi duk abin da aka ba mu, da cewa mu yi biyayya kuma mu yi tsit da bakinmu. Ina karfafa wa mata gwiwa da su ci gaba da neman hakkinsu don su samar da yanayi da tsari mai kyau ga 'yan matan Afirka da suke da burin samun nasara a fagen kwallon kafa."
Bayan matsalar nuna bambanci tsakaninsu da maza wajen biya, akwai zarge-zarge da suka dabaibaye kwallon kafar mata kamar matsalar cin zarafi, inda babban kocin tawagar Copper Queens Bruce Mwape yake fuskantar tuhume-tuhumen cin zarafi.
A watan Satumbar bara, Hukumar Kwallon Kafar Zambiya (FAZ) ta ce ta mika ragamar bincike wasu zarge-zarge cin zarafi a wasannin mata ga FIFA.
Mwape da kocin tawagar 'yan kasa da shekara 17 Kaluba Kangwa suna daga cikin mutanen da ake bincike.
Amma duk da wadannan kalubale, Afirka za ta ci gaba da nuna goyon baya ga tawagoginta na mata da za su je Australia da New Zealand da magoya bayansu daga duka kasashen nahiyar da suka zuba ido don ganin sun tabuka rawar a zo a gani a gasar.