Tawagar kwallon kafar matan Nijeriya ta samu shiga mataki na gaba a gasar cin kofin duniya bayan ta tashi canjaras da tawagar matan Jamhuriyar Ireland a fafatawar da suka yi ranar Litinin.
Wannan na nufin Nijeriya ta kammala matakin rukuni da maki biyar yayin da tawagar Australia ta karkare matakin da maki shida.
Australia, wadda Nijeriya ta doke da ci 3-2 a baya, ta yi nasarar doke Canada da ci hudu da nema a wasan da su ma suka yi ranar Litinin.
Sai ranar bakwai ga watan Agusta Nijeriya za ta yi wasa a matakin sili daya kwala.
Nijeriya za ta kara da kasar da ta zo ta daya a rukunin D wanda ke kunshe da Ingila da Denmark da China da kuma Haiti.
A halin yanzu dai Ingila ce ta daya da maki 6 a rukunin, yayin da kasar Denmark da kasar China ke bin ta a mataki na biyu da uku da maki uku-uku. Ita kuwa Haiti ba ta da maki ko daya.
A ranar Talata ne dai kasar China za ta kara da Ingila inda ita kuma kasar Haiti za ta kara da kasar Denmark.
Bayan wannan wasan ne za a san kasar da ta zo ta daya a rukunin D, kuma ita kasar da ta zo ta dayar ce za ta kara da Nijeriya ranar bakwai ga watan Agusta.