Fernandez, wanda shi ne ɗan wasa mafi tsada a tarihin Gasar Premier, ya nemi afuwa. / Hoto: Reuters      

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Duniya, FIFA ta ce za ta buɗe bincike kan waƙoƙin wariyar launin fata da 'yan wasan Argentina suka rera bayan sun lashe kofin Copa America.

''FIFA na sane da wani bidiyo da ya karaɗe shafukan intanet kuma tana kan duba kan lamarin.

FIFA tana Allah- wadai da duk wani nau'in nuna wariya daga ko waye ciki har da 'yan wasa da magoya baya da kuma sauran jami'ai,'' in ji mai magana da yawun hukumar a ranar Laraba.

An dai ji waƙokƙn ne a wani bidiyo da ɗan wasan tsakiya na Chelsea da Argentina Enzo Fernandez ya wallafa kai tsaye a cikin motar tawagarsa bayan nasarar da suka samu kan Colombia a gasar Copa aka yi a Miami a ranar Lahadi.

Wasu 'yan wasa ciki har da Fernandez, sun taɓa rera waƙa ta nuna wariya tun a Gasar Cin Kofin duniya ta 2022 da Argentina ta doke Faransa.

Wakar ta mayar da hankali ne kan tauraron ɗan wasan Faransa Kylian Mbappe wacce ta haɗa har da zagi.

Ba a yarda da hakan ba kwata-kwata

Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Faransa ta miƙa ƙorafinta ga FIFA game da waƙoƙin.

A baya dai Chelsea ta sanar da cewa ta ƙaddamar wani tsarin ladabtarwa na cikin gida kan Fernandez kan lamarin.

Fernandez, wanda shi ne ɗan wasa mafi tsada a tarihin asar Premier, ya nemi afuwa kan hakan.

Ƙungiyar, a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce, "Kungiyar Ƙwallon Ƙafa ta Chelsea ba za ta ɗauki duk wani nau'in nuna wariya ba kwata-kwata.''

''Mun amince kuma mun yaba da uzurin da 'yan wasanmu suka bai wa jama'a kuma za mu yi amfani da wannan a matsayin wata dama don ilimantarwa.

Ƙungiyar ta bullo da tsarin ladabtarwa na cikin gida," in ji sanarwar.

AFP