Rahotanni daga kasar Sifaniyan sun nuna cewa an rika zage-zagen ne kan Nnaji./Hoto/AFP

Kungiyar kwallon kwando ta Barcelona ta yi Allah wadai da zagin wariyar launin fata da aka yi wa dan Nijeriya, James Nnaji, a lokacin wasan karshe na gasar cin Kofin Sifaniya da suka kara da Real Madrid.

Lamarin da ya faru ranar Talata na zuwa ne a lokacin da fannin wasannin Sifaniya ke fama da suka daga fadin dunyiya kan wariyar launin fatar da aka nuna wa dan wasan kwallon kafar Real Madrid, Vinicius Jr.

A watan Mayu ne dan wasan Brazil, mai shekara 22, ya yi korafi kan wariyar launin fatan da ake yi masa a gasar kwallon kafar Sifaniya tun lokacin da ya koma kasar da taka leda shekara biyar da suka wuce.

A ranar Laraba irin wannan ya sake faruwa, amma a fagen kwallon kwandon Sifaniya.

“Barcelona ta yi Allah wadai da zagin wariyar launin fatar da aka yi wa dan wasa James Nnaji kafin a yi rukunin wasa na uku na wasan karshe,” in ji kungiyar a cikin wata sanarwar da ta fitar ranar Laraba.

“Kulob din na sa ran martani mai karfi daga ACB [ hukumar gasar kwallon kwandon Sifaniya] kan ko wane zagi na wariyar launin fata ko na baka.”

Hotunan isowar motar kungiyar Barcelona filin wasan WiZink centre a Madrid, inda aka yi wasan na ranar Talata , sun nuna wasu magoya bayan Madrid suna zagin 'yan wasan Barcelona.

Rahotanni daga kasar Sifaniyan sun nuna cewa an rika zage-zagen ne kan Nnaji.

“Ina son na yi magana a kan abin da ya faru a nan da James Nnaji. Ina ganin abin bakin ciki ne. Na ji abubuwa da dama game Vinicius, kuma a yanzu mu ne ya zama dole mu yi magana game da abin da ke faruwa,” a cewar kocin kungiyar kwallon kwandon Barcelona, Sarunas Jasikevicius.

TRT Afrika da abokan hulda