Wani sharhi mai zaman kansa da wasu lauyoyin da suka ƙware a kan kare hakkokin ɗan'adam suka yi ya ce dole ne a dakatar da Isra'ila kan shiga duk wani abu da ya shafi ƙwallon ƙafa saboda take dokokin hukumar FIFA da take yi a yaƙin Gaza.
A watan Mayu ne Hukumar Kwallon Ƙafa ta Falasɗinu (PFA) ta miƙa wani ƙuduri na son a dakatar da Isra'ila, inda FIFA ta ba da umarnin gaggawa na yin duba kan lamarin, tare da yin alkawarin cewa za ta magance shi a taronta na musamman a watan Yuli.
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Asiya ta kuma ba da goyon bayanta na daukar mataki kan Isra'ila kuma shugaban PFA Jibril al Rajoub ya ce FIFA ba za ta iya ci gaba da nuna halin ko-in-kula ga "cin zarafi ko kisan kiyashi da ake yi a Falasdinu ba".
Mai shari'a Max du Plessis, wanda ke cikin batun shari'ar da Afirka ta Kudu ke zargin Isra'ila da aikata kisan kiyashi a Kotun Ƙasa da Ƙasa, yana cikin waɗanda suka rubuta sharhin tare da Sarah Pudifin-Jones, bayan da wata ƙungiya mai zaman kanta da ke fafutukar tabbatar da adalci ta tuntuɓe su.
Rahoton ya ce "Babu wata tababa cewa ba a ɗaukar halayyar da Isra'ila ke nuna wa a kan Falasdinu da muhimmanci, kuma hakan yana cin kafo da muradun FIFA."
"Isra'ila ta keta hakkokin Falasdinawa da kasashen duniya suka amince da su, sabanin sashe na 3. Tana nuna wariya tare da ci gaba da nuna wa Falasdinawa wariya bisa ƙabilanci, asalin kasa da kuma haihuwa wanda ya saɓa wa doka ta 4(1) kai tsaye.
"Lamarinta yana lalata manufofin jinƙai da aka bayyana a cikin Sashe na 5.1 (b). Abin da Isra'ila ke yi na bukatar a yi Allah wadai, daidai da matsayin da FIFA ta dauka dangane da irin wannan abu na keta manufofinta da kuma yadda kasashen duniya suka amince da su."
Kudurin na Falasdinawa ya zargi hukumar kwallon kafa ta Isra'ila (IFA) da hannu wajen keta dokokin kasa da kasa da gwamnatin Isra'ila ke yi da kuma nuna wariya ga 'yan wasan Larabawa. IFA ta ƙi amincewa da hakan.
Eko ya ce ƙorafin nasu na yin kira ga FIFA ne, da Kwamitin Gasar Olympic na Ƙasa da Ƙasa da hukumomin ƙwallon ƙafa na duniya da su dakatar da Isra'ila daga wasannin duniya, kuma ya samu sa hannun sama da mutum 380,000.
Reuters ta nemi jin ta bakin FIFA.
Lokutan da FIFA ta yi dakatarwa
A cikin 'yan shekarun nan lokacin da PFA ta kawo ƙudirin dakatar da Isra'ila, FIFA ba ta sanya takunkumi ba, a 2017 ta bayyana cewa za a rufe batun kuma ba za a ci gaba da tattaunawa ba har sai an canza tsarin doka.
Rahoton ya bayar da hujjar cewa abubuwan da suka faru tun watan Oktoba sun haifar da "sabon tsarin shari'a wanda ya tilasta wa FIFA shiga tsakani".
Al Rajoub ya bayar da misali da abin da ya faru a taron FIFA kuma bincike ya ce dakatarwar da Isra'ila ta yi za ta kasance daidai da shawarar da FIFA ta yanke a baya na dakatar ko korar kungiyoyin mambobi da suka saba wa manufofinta.
An dakatar da hukumar kwallon kafa ta Afirka ta Kudu a shekarar 1961 saboda manufofin wariyar launin fata a kasar yayin da aka dakatar da kasar Yugoslavia a shekarar 1992 sakamakon takunkumin da Majalisar Dinkin Duniya ta kakaba mata a lokacin da gwamnatin Sabiyawa ke mamaye yankunan Balkan.
A baya-bayan nan, a shekarar 2022, FIFA da takwararta ta nahiyar Turai UEFA, sun dauki matakin dakatar da kungiyoyin Rasha daga gasarsu, sakamakon harin da kasar ta kai a Ukraine.