Nijeriya za ta kara da Ivory Coast a ranar Laraba a matakin daf da ƙarshe na Gasar AFCON. / Hoto: Getty Images

Gwamnatin Nijeriya ta shawarci ƴan ƙasar da ke zaune a Afirka ta Kudu kan su kula da kansu kafin da kuma bayan wasan da ƙasar za ta yi da Afirka ta Kudu a Gasar AFCON.

Ofishin jakadancin Nijeriya da ke birnin Pretoria na Afirka ta Kudu ne ya fitar da wannan sanarwar inda ya ce ya kula da wasu maganganu da ake yi a shafukan sada zumunta waɗanda ka iya tayar da hargitsi bayan wasan.

“Galibin kalaman sun kunshi barazanar da ake yi wa “’ƴan Najeriya kan dafa dukar shinkafa” kafin wasan, da kuma “saka wa ƴan Nijeriya barkono idan Bafana Bafana ta sha kashi a hannun Super Eagles a ranar Laraba 7 ga watan Fabrairun 2024,” in ji sanarwar.

“Sakamakon haka, ofishin jakadancin ke bayar da shawara ga ƴan Nijeriya da su lura da abubuwan da za su furta da kuma wurin da za su je kallon wasan musamman a bainar jama’a, da kuma guje wa ɗaga murya a lokacin murna ko tayar da rikici ko murna cikin tsokana idan Super Eagles ɗin ta yi nasara a wasan.

“Haka kuma, ƴan Nijeriya su ci gaba da nuna kyakkyawar ɗabi’ar da aka san su da ita, su kuma bi doka kafin da kuma bayan wasan. Ko da an harzuƙa, kada su mayar da martani, su kai koke wurin hukumomin da suka dace,” kamar yadda sanarwar ta ƙara da cewa.

Duka wannan na zuwa ne a daidai lokacin da Nijeriya ke shirin buga wasan daf da ƙarshe da Afirka ta Kudu a Gasar AFCON a ranar Laraba.

A ɗayan ɓangaren kuwa Ivory Coast wadda ke karɓar baƙuncin gasar za ta fafata da Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo a ranar Larabar.

Duk waɗanda suka yi nasara a cikin rukunan biyu za su fafata a wasan ƙarshe a ranar Lahadi 11 ga watan Fabrairun 2024.

TRT Afrika