Kasar Afirka ta Kudu ta kafa tarihi a karo na farko bayan da ta tsallake zuwa zagayen sili-daya-kwale na gasar cin kofin duniya ta mata bayan da ta doke Italiya da ci 3 da 2 a ranar Laraba.
'Yar wasar Banyana-Banyana Thembi Kgatlana ce ta zura wa Afirka ta Kudu kwallo ta uku a minti na 92 lamarin da ya bai wa kungiyarta damar kai wa wannan mataki.
Italiya ce ta fara zura kwallo a ragar Afirka ta Kudu ta hanyar fenareti minti 11 da fara wasa.
Kana 'yar wasar Italiya Benedetta Orsi ta mayar da wasan 1-1 yayin da ta zura kwallo a ragar kasarta bisa kuskure a minti 32 da fara wasa.
Hakan bai sa 'yan Afirka ta Kudu sun daina kai wa Italiya hari ba, kuma sun yi nasarar zura kwallo a ragar Italiya minti 67 da fara wasa ta hannun Magaia.
Kasancewar wasan 2-1 ya zaburar da 'yan Italiya inda suka yi ta kokarin daukar fansa.
A minti 74 na hakarsu ta cimma ruwa inda Arianna Caruso ta tura kwallo ragar Afirka ta Kudu da kai, kuma wasan ya koma 2-2.
Mutane sun fara tunanin za a tashi canjaras a wasan har zuwa minti 92 lokacin da Thembi Kgatlana ta zura kwallo a ragar Italiya.
Wannan sakamakon ya sa Afirka ta Kudu ta karkare matakin rukuni a mataki na biyu da maki hudu.
Ranar Lahadi ne Afirka ta Kudu za ta kara da kasar Netherlands a matakin sili-daya-kwale a gasar cin kofin duniyar.