Agnes Jebet Ngetich ta samu wannan nasarar a birnin Valencia na Sifaniya. / Hoto: Reuters

'Yar kasar Kenya Agnes Jebet Ngetich ta kafa tarihin tseren gudun mata na kilomita 10 da kusan rabin minti daya a Valencia a ranar Lahadi.

‘Yar gudun mai shekara 22 ta kammala gudun a cikin minti 28 da dakika 46, inda ta wuce wadda ta kafa tarihi a baya ‘yar kasar Habasha Yalemzerf Yehualaw shekara biyu da ta gabata.

Ngetich ce mace ta faro da ta kafa tarihin minti 29 a gudun mata. “Ina murna kan cewa na kafa tarihi a duniya a minti 28.

Ban taba tunanin haka ba,” in ji ta. Gudun na maza Jacob Kiplimo dan kasar Uganda ne ya ci shi a cikin minti 26:48.

AFP