An fara Gasar Cin Kofin Duniya ta Mata a kasashen Australia da New Zealand. Yayin da aka mayar da hankali kan wasannin da ake bugawa da kwallayen da ake zurawa a raga, abubuwa da yawa na faruwa a wajen filayen wasanni da abubuwan da suke daukar hankali ciki har da baje-kolin al'adu.
Nijeriya tana daga cikin kasashe hudu da ke wakiltar nahiyar Afirka a Gasar Kofin Duniyar Mata ta 2023. Tawagar Nijeriya da ake kira Super Falcons ta fafata a kowace gasar da aka yi tun daga ta shekarar 1991.
Magoya bayan Philippines sanye da tufafin al'ada a wajen filin wasa gabanin fara wasa. Kodayake Philippines ita ce ta karshe a rukunin A, kayan al'adar kasar sun ja hankalin mutane a wajen filin wasa. Kuma kasar ta samu nasararta ta farko a Gasar Kofin Duniya kan daya daga mai masaukin baki wato New Zealand.
Vietnam tana rukunin E ne tare da kasar Amurka da Portugal da kuma Netherlands.
Kasashe hudu ne suke wakiltar Afirka a gasar – Nijeriya da Zambiya da Afirka ta Kudu da kuma Maroko – kowace daga cikinsu tana da basira ta musamman.
Magoya bayan sun zo da al'adu na musamman, inda suke wakiltar nahiyar. Wannan wata goyon baya ce sanya dan kunne mai taswirar nahiyar Afirka, nahiyar da ke da kasashe 54.
Zambiya tana daga cikin kasashen da ke wakiltar Afirka a Gasar Kofin Duniya ta Mata a Australia da New Zealand kuma kasar ta baje-kolin wasu daga cikin al'adunta.
Kodayake Zambiya ba ta taka rawar a zo a gani ba musamman rashin nasarar da ta yi a hannun Spain da ci 5-0, duk da haka Zambiya na alfahari da kokarinta.
Afirka ta Kudu ba ta taka rawar gani a filin wasa, sai dai su ma sun rika baje-kolin kyawawan al'adunsu.
Afirka ta Kudu ta buga kunnen doki 2-2 da Argentina a wasan rukunin G a ranar Juma'a, hakan ya sa duka kasashen biyu za su ci gaba da kasancewa a gasar amma kuma babu tabbas ko za su matsa zuwa zagayen gaba.
Wannan ne karon farko da Maroko take halartar Gasar Kofin Mata na Duniya. Ta yi nasara a karon farko a wasansu da Koriya ta Kudu da ci 1-0.
Bayan gwiwarsu ta yi sanyi a wasan da Jamus ta doke su da ci 6-0 a wasansu na farko, yanzu tawagar Maroko da magoya bayanta suna da kwarin gwiwa zuwa matakin gaba a gasar.
Yayin da ake ci gaba da Gasar Kofin Duniya na Mata na 2023, ana ganin launika iri-iri, ana saran ganin wasu abubuwa masu daukar hankali bayan kallon wasan kwallon kafa.