Daga Edward Wanyonyi
Duk da cewa bai wuce kwana 8 ba a fafata zabukan Shugaban Kasa da majalisun tarayya na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Congo ba wato DRC, yanayin kasar bai wani sauya ba a jihohin kasar guda 26, ciki har ma da Babban Birnin kasar, Kinshasa.
Akwai ’yan takarar Shugaban Kasa guda 26 da Hukumar Zaben kasar, wato National Electoral Commission (CENI) ta tantance, wanda hakan ya sa ake cigaba da shirye-shirye, musamman ga manyan jam’iyyun kasar domin samun nasara.
Idan har akwai wani abu mai muhimmanci a zaben mai zuwa, bai fi a ce an 'yan takarar su zagaya kasar domin sauraron bukatar mutanen kasar ba, maimakon kawai neman kuri’arsu, tare da yi musu alkawarin kawo musu sauyin da suka fara cire tsammani da samu.
Ya kamata su rika sauraron kiraye-kirayen mutanen kasar na samun sauyi, da sanya tausayi da bayyana gaskiya da barin kofar maslaha a bude, da kuma neman cigaban kasar.
A duk lokutan da ake tattauna batutuwa a game da gwamnatin kasar Congo, ana yin watsi da wadannan abubuwan guda biyar.
Maimakon haka, sai ake cigaba da kwaikwayon harkar gwamnatin Turawa, wanda aka tsara a kan tafarkin dimokuradiyyar Turawan Yamma masu sassaucin ra'ayi da ke zuwa a fi yawan lokuta da mayar da hankali a kan kula da albarkatun kasa da yi wa harkar tsaro garambawul, da jin kan al’umma.
Yawaitar rikice-rikice
Kamar yadda masana da masu bincike dama suke yawan bayyanawa a kasashen Yamma, tilasta amfani da tsare-tsaren dimokuradiyyar Yamma a matsayin hanyar magance matsalolin Congo domin ta samu tsayuwa da kakafunta, taimakawa kawai yake yi wajen mayar da birnin Kinshasa kamar wata kasuwar bukatar kasashen duniya, da sunan 'sake gina kasar bayan rikice-rikice."
Sun gaza magance ainihin matsalolin da suke jawo tabarbarewar matsalolin da kasar ke fuskanta, da kuma yadda ake ganin mutanen kasar a idon duniya, musamman wajen dawo da martabarta.
Wannan matsalar ta sa Congo tana yawan sake shiga cikin rikici, da damuwa a daidai lokacin da duniya take kallon yadda za ta samu shiga ta tatsa albarkatun kasar ko dai ta hannun ’yan ta’addar kasar, ko ta wajen gwamnati kamar Primera Gold DRC.
A daidai lokacin da kasar ke shirye-shiryen zabe, ya kamata kungiyin sa-ido da kasashen duniya su mayar da hankali wajen tabbatar da cewa sahihancin zaben, sannan a tsara hanyar cigaban kasar domin samar da sabuwar Congo.
A yanzu ya kamata mutanen kasar da ’yan takarar Shugaban Kasa su gane cewa matsalolin da Congo ke fuskanta yana da alaka da halayensu, sannan duk da haka, ba zai zama uzuri ba a durkusar da kasar.
Yadda Gabashin kasar mai sama da mutum miliyan 3.8 da suke gudun hijira suke bukatar agaji, da kuma sama da kungiyoyin ’yan ta’adda guda 120 da suke kasar, musamman a Gabashin ya nuna akwai matukar bukatar neman zaman lafiya.
Game halin da ake ciki
Akwai bukatar ya kasance an tsara hanyar samar da zaman lafiya kauyuka, da jihohi ba kawai a zauna a tattauna a sama ba, a bar Hukunar MOUSCO ta Majalisar Dinkin Duniya ta dabbaka.
Akwai bukatar ’yan takarar su shige gaba wajen tsarawa da assasa Asusun Samar da Zaman Lafiya, ba wai kawai su rika aiki da daidaikun mutane da za su dauki nauyin kamfe dinsu ba, domin sanin yadda za su mayar musu da biki bayan sun samu nasara.
Akwai bukatar neman hadin gwiwar kasashe masu makwabtaka da Congo domin hadakar kasuwanci da daga darajar kasar, da kuma magance matsalar fasakaurin albarkatun kasa a kasashen makwabta.
Haka kuma akwai bukatar a soki lamarin kasashen duniya da suke mayar da sama da mutum miliyan100 na kasar tamkar saniyar tatsarsu.
Amma wadannan abubuwa, da kuma abubuwan da za a yi ba za su yiwu ba face an fahimci cewa akwai bukatar aikin agaji da tsara hanyoyin ciyar da kasar gaba, wadanda ya kamata a tsara bisa tausayi da sanin ya kamata da za su ciyar da kasar gaba.
Yadda ake yawan samun rikice-rikice a kasar tun samun ’yancin kai a shekarar 1964, ya taimaka wajen hana kasar cigaba.
Jean Paul Mvogo ya bayyana cewa duk da dimbin arzikin da kasar Congo ke da shi, kasar ce ta 176 a cikin kasashe 187 marasa cigaba kamar yadda sabon kididdigar Majalisar Dinkin Duniya ta nuna.
Bincike kan jami'an Kungiyar Lafiya ta Duniya wato WHO da na Hukumar MONUSCO da aka samu da saba manufofin aikinsu na jin kai shi ne matakin farko na magance yadda tsarin ba da agajin jinƙai na kasa da kasa ke da kura-kurai. Sannan, ya dace 'yan takarar Shugaban Kasar Congo da na 'yan majalisar su dauki danarar gyara tsarin jinƙai na ƙasar.
Shirin samar da zaman lafiya na cikin gida
Lokaci ya yi da kungiyoyin kawance na Jamhuriyar Dimokuradiyyar Kongo (DRC) za su ba da taimako, ba ga kungiyoyi masu ta da kayar baya ba kadai, har da kungiyoyin agaji da aka tantance wadanda kuma ke tallafa wa abubuwa daban-daban a cikin harkar jinƙai.
Kuma don cimma wannan, bai kamata lokacin zabe ne kawai ya zama lokacin da 'yan takara za su yi baje-kolin manufofinsu tare da nuna kojarinsu na kawar da duk wani kalubale da aka fuskanta a tarihi a kwanaki 100 na farkon mulkinsu ba, wani abu da zai zama mai muhimmanci shi ne fitowa da gaske don bude kofofin sulhu—ba kawai a tsakanin manyan mutane masu mulki ba, har ma da sauran al'umma.
Idan aka yi la’akari da sauye-sauyen kan iyakoki da rikidewar al'amuran tarihi, dangantaka ta dangi da dangi, babu wani wani nau'in difulomasiyya na kasa da kasa da zai iya magance takaddamar da ke tsakanin Kigali da Kinshasa. Hukumar samar da zaman lafiya ta gida ce da aka samar da ita don sulhu na gaskiya kadai za ta dawwamar da zaman lafiya.
Duk da haka, ka da a manta cewa DRC ta samu damarmaki da yawa a baya don farowa daga farko.
Matsalar dai a yanzu ita ce, ya kamata a ce tsarin zaben ya sauya matsayi wanda ya wuce kirga kuri’u kawai da bayyana wanda ya yi nasara.
Ya kamata duk wanda ya ci zabe ya kasance a tare da shi akwai himma da azamar sauya kasar. Ya kamata aniyar sauya DRC ya zama aiki ne na kowa—kama daga dukkan jam'iyyun siyasa, 'yan kasa—ba kawai na jam'iyya mai mulki ba.
Marubucin, Edward Wanyonyi, masani be kuma mai bincike a kan harkokin tsaro da abubuwan da ke kawo cigaba na duniya. Za a iya samunsa ta imel: edward.marks09@gmail.com
Togaciya: Ba dole ba ne ra’ayin marubucin ya zo daidaida ra’ayi ko ka’idojin aikin jaridar TRT Afrika.