Mamane, mai barkwanci dan kasar Nijar, gwani ne wajen amfani da wasan raha wajen isar da sakonni masu muhimmanci / Hoto: AFP

Ra'ayi Daga Dan Hammett da Laura Martin da Izuu Nwankwọ

Mun manta sau nawa aka taba tambayar mu, “Me ya sa kuke bincike kan wasan raha?” Amsarmu a bayyane take, kuma guda daya ce, wato saboda annashuwa.

Waye ba ya son jin dadin aikinsa? Duka mun san amfanin dariya da ban-dariya da barkwanci. Ana wasan raha a ko ina kuma tana da tasiri, ko dai wajen bayyana kin amincewa, ko nuna iko.

Wannan shi ne manufar da muka rubuta littafinmu da ita. Wato amfani da raha wajen nuna juriya da wahalar rayuwar yau da kullum.

Ko wane dayanmu ya yi rubutu kan raha a yanayi daban-daban, lokacin wasan barkwanci a Nijeriya, ko kwatanta raha da rikici a Saliyo, ko kuma zanen barkwanci a jaridun Afirka ta Kudu.

A kowace daya daga cikin kasashen nan, da ma sauran kasashen nahiyar Afrika, mun ga yadda ake shirye-shiryen raha, da yadda ake karbar ta, da ma yadda ake jayayya kanta a hanyoyi da yawa.

Mun ga yadda ake amfani da raha wajen dorewar zaman lumana tsakanin al’ummomi, da bai wa mutane hanyoyin jure wahalhalun rayuwa.

Akwai kuma yadda rashin fahimtar raha kan iya janyo rashin jituwa, musamman tsakanin kasashe da al’ummomi. Har ma da yadda wasan raha kan haifar da rikici.

Amma kuma, muhawara kan wasan raha da siyasa a Afirka sau da yawa takan mayar da wasan raha wani fage na nuna turjiya, ko a lokuta masu yawa, nuna turjiya don tunawa ‘yan kasa iko ko zaluncin mahukunta.

Kokarinmu a wannan littafin shi ne tunani kan wasan raha a Afirka a yanayi daban-daban, domin gane cewa wasan raha yana da matukar tasiri.

Wannan ba ya nufin muna cewa wasan raha na ‘yan Afirka salo daya ne ba, ko kebantacce. Amma Afirka tana da tarihi mai fadi da salo-salo mabambanta.

Akwai wanda ake kira “imbongi” ko “wawan sarki”, wanda ake yin sa a fadar sarauta. Sai kuma wasa tsakanin al’ummomi ko kabilu.

Daga nan kuma aka samu bikin wasan raha, da kuma zane-zanen barkwancin siyasa. Kamar a sauran sassan duniya, a Afirka ma barkwanci da siyasa suna da alaka.

Ana yin raha kan batun siyasa ko ‘yan siyasa ko shugabanni, a wani salo na sukar abokan hamayya. Sannan manyan mutane kan yi raha don nuna kusanci da mutane, da bagararwa kan wahalhalun al’umma da kuma shakatawa.

A takaice dai, wasan raha dabara ce mai zaman kanta, wadda ake siyasa da ita. Ana amfani da ita a hanyar ci gaba ko wayewa, yawanci a kankanin lokaci take shigewa zance.

Ana amfani da barkwanci wajen bijirewa, ko daukaka wani ra’ayin siyasa ko zamantakewa. Wato dai, barwakanci yana da tasiri a siyasa.

A kowane irin yanayi, ana wasan raha a matsayin wata damar shiga a dama da mutum a harkar zamantakewa, da siyasa, wadda ke iya magance rashin daidaiton arziki ko na siyasa.

Hakan yakan bai wa mutane dama su fada wa mahukunta gaskiya, kuma su nemi ‘yancin shiga lamuran kasarsu. Misali suna yada zanen ‘yan siyasa na barkwanci game da gazawarsu da kurakuran gwamnati.

A irin wannan salo, akan samu su kansu ‘yan siyasan suna daukar hayar masu barkwanci don ci gaba da riki mulki, misali yayin yakin neman zabe. Haka ma yin zunde ga wata al'umma don samar da barakar da su ci gajiya.

Yayin da masu barkwanci da masu ban-dariya suke da ‘yancin taba ‘yan siyasa a kasashen Afirka, a wasu kasashen wasan raha kan sa rayuwar mutum ta shiga hadari.

A ‘yan shekarun nan mun ji rahotanni kan yadda masu zanen barkwanci, da masu ban-dariya, aka kama su, ko aka musu duka, ko aka daure su, ko aka kashe su, ko ma aka tilasta musu gudun hijira.

Wannan ya nuna tasirin raha wajen haifar da wasu matsalolin a duniya.

Tarihi ya nuna yadda ‘yan mulkin mallaka suka yi amfani da dokoki don hana wasan raha kan manyan mutane.

Bayan wucewar mulkin mallaka, an yi tunanin samun ‘yancin siyasa da zai janyo karin cigaba ga wasannin barkwanci.

Sai dai kuma, wannan mafarki bai gaskata ba saboda shugabanni bayan ‘yancin-kai sun ci gaba da fada da masu barkwanci da ban-dariya kan ‘yan siyasa.

A kwanakin nan, abubuwa sun fara sauyawa, domin kuwa an samu karin dauriya da wasu nau’in wasan raha na siyasa (musamman shirin wasan raha) a kasashe da dama.

Amma an ci gaba da muzgunawa masu barkwanci ta amfani da dokokin shari’a, da ma wadanda suka saba wa shari’a.

Yayin da ake fuskantar sauye-sauyen lamura a nahiyar Afirka, shin an taba samun lokacin da wasan raha ya ci karensa ba babbaka?

Za mu iya cewa hakan na faruwa a halin yanzu, ganin yadda masu barkwanci suke yin suna irin na manyan mawaka, ko ma manyan masu wa’azi.

Amma cewa a wannan zamani suka fi samun dama, ba zai zama gaskiya ba. A duk zamuna, ana samun wasan raha a salo daban-daban a nahiyar Afirka.

Littafin da muka rubuta yana da burin gini kan abin da yake a tarihi, da wanda aka gada, ba tare da la’akari da yunkurin hukumomi na tallafawa ko hana ra’ayin da ba su so ba.

Marubutan Ra'ayin:

Dan Hammett, babban malami a sashen nazarin kasa, Jami’ar Sheffield ta Burtaniya, kuma Babban Malami Mai Bincike a Sashen Nazarin Kasa, Muhalli da Makamashi, Jami’ar Johannesburg, Afirka ta Kudu.

Laura Martin mukaddashiyar Farfesa a Nazarin Siyasa da Lakar Kasa da Kasa, Jami’ar Nottingham; mai bincike a Jami’ar Makeni, Saliyo.

Izuu Nwankwọ Mai Bincike a Sashen Nazarin Al’adu da Afirka, Jami’ar Johannes Gutenberg University, Jamus.