Daga Mubarak Aliyu
Yunkurin neman sabon Sankara ya haifar da tabarbarewar siyasa a Burkina Faso tun a shekara ta 2014, lokacin da aka hambarar da gwamnatin Compaore da ta dade tana fuskantar zanga-zanga.
Ko da yake, a wannan zamani wanzuwar wani sabon Sankara abu ne mai matukar wuya, sakamakon yadda yanayin zamantakewa da siyasa suka canza sosai tun shekarun 1980.
Thomas Sankara ya kasance shugaban al'ummar Burkina Faso wanda aka fi saninsa da rawar da ya taka wajen aiwatar da manufofin ci gaban zamantakewa da tattalin arziki da gyare-gyare wadanda suka inganta rayuwar talakawan kasar Burkina Faso.
Gagarumar Nasarar da ya samu wajen bunkasa fannin ilimi da sakamakon kiwon lafiya da kuma manufofin muhalli da daidaiton jinsi a cikin shekaru uku, sun sanya shi matsayin gaba tare da sake fayyace dama ta samun ci gaba mai inganci a fadin nahiyar Afirka.
Babban koma bayar tarihin jarumtakar Sankara ta fuska wanda dole a tattauna, shi ne yanayin da ya hau kan karagar mulki.
Tashin Sankara
Juyin mulkin shekarar1983 da abokin aikinsa Blaise Compaore da sauran sojojin da suke aiki tare suka shirya masa, ya yi sanadiyar kawar da gwamnatin Ouédraogo tare da kafa Majalisar juyin juya hali a kasar (Conseil National de la Révolution) tare da sanya Sankara a matsayin shugabanta.
Sauye-sauyen siyasar da Sankara ya yi a baya sun hada da korar shugabannin gargajiya na Burkina Faso da kuma rage yawan kudaden da gwamnati ke kashewa wanda ya yi la'akari da hakan a matsayin almubazzaranci.
Da lokaci da 'dan ja, wata kungiyar manyan jami'ai ciki har da Compaoré, ba su goyi bayan manufofinsa na kawo ci gaba ba.
Bambancin ra'ayin ya kai ga rabuwar sojin kasar zuwa manyan bangarori biyu, inda daya bangaren ke goyon bayan Sankara, yayin da dayan kuma ke mara wa Compaore baya.
An kashe Sankara biyo bayan wani gagarumin goyon baya daga kasashen waje da kuma karfin sojin Burkina Faso a wani juyin mulkin da Compaoré ya jagoranta a 1987.
Magoya bayan Sankara da Compaore
A wannan zamanin, yanayin siyasar Burkina Faso na fuskantar rarruwar kawuna tsakanin magoya bayan Sankara da Cpmpaore, inda ake yi wa 'yan sankara kallon masu ra'ayin son ci gaba yayin da 'yan Compaore ke da ra'ayin mazan jiya.
Wannan tahiri na jarumtakar ya yi matukar yin tasiri kan gwagwarmayar mulki a kasar tun 1987 bayan kashe Sankara.
A shekarar 2003, an kama akalla sojoji 16 a birnin Ouagadougou, bayan wani yunkurin juyin mulki.
Daga cikin wadanda aka kama har da Michel Norbert Tiendrebéogo, shugaban jam'iyyar Sankalist da aka fi sani da sojoji da ke kan gaba a ra'ayin gurguzu.
Zargin yunkurin juyin mulkin 2003 ne ya bude kofar tabarbarewar siyasa da ta kunno kai tsakanin magoya bayan Sankara da Compaore a shekarun 2020.
Faduwar Compaore
An hambarar da Compaore daga kan mulkinsa na shekaru 27 bayan wata gagarumar zanga-zangar da aka yi a shekarar 2014.
An kaddamar da bincike game da hannunsa a kisan Sankara a shekarar 2021 kuma an yanke wa Compaore hukuncin daurin rai da rai tare da wasu manyan abokan aikinsa guda biyu.
Sai dai a watan Janairun 2022 ne wasu sojoji suka hambarar da gwamnatin farar hula, kana kasar ta koma karkashin wani tsari na mulkin soja karkashin jagorancin Paul-Henri Sandaogo Damiba.
Duk da cewa juyin mulkin bai fito fili ya mayar da martani ga hukuncin ba, amma akwai wasu fitattun ‘yan Compaore da ke da hannu a ciki, duk da cewa da farko Damiba ya bayyana cewa tsarin Sankara ne ya janyo ra'ayin manufofinsa a matsayin wani gagarumin mataki da ya sa shi ya kwace mulki.
Watanni bayan juyin mulkin, gwamnatin Damiba ta gayyaci Compaore don halartar taron sulhu na tsoffin shugabannin kasar a Ouagadougou babban birnin kasar, yanayin da ya bai wa tsohon shugaban kasar da aka yanke wa hukunci kuma mai gudun hijira damar komawa Burkina Faso na tsawon kwanaki kuma daga karshe ya fice ba tare da kama shi ba.
Zuwan Ibrahim Traore
Rashin hukunta Compaoré daga gudun hijira a Cote d'Ivoire da gwamnatin Damiba ta yi, ya ba da damar sake yin juyin mulki watanni biyu bayan haka, a wannan karon daga 'yan Sankara karkashin jagorancin Ibrahim Traore, wanda ya karbi mulki a watan Satumban 2022.
Juyin mulkin Traore shi ne na baya bayan nan a takardamar neman mulki tsakanin 'yan Sankara da 'yan Compaore, wanda ke nuna irin tasirin siyasar da Sankara ya kafa a fagen siyasar Burkina Faso.
Idan aka yi la’akari da tsarin manufofin mulkin mallaka na Ibrahim Traoré, bai wani zo da mamaki ba lokacin da gwamnatin mulkin sojin kasar ta sanar da yunkurin juyin mulki da aka yi a watan Satumban 2023, wanda ke nuna yiwuwar kara kwace madafun iko.
Ana iya danganta wannan gagarumar gibi da aka samu na rashin zaman lafiya da tabarbarewar siyasa kisan da aka yi wa Sankara, wanda wasu manyan kasashen waje suka shirya shi ta hanyar amfani da tasirin Compaoré.
Sankara mai ra'ayin gurguzu
Kamar yadda aka abin yake a wannan zamani, tarihin jarumtakar Sankara yana da nasaba da yakin siyasa, inda muradun siyasar kasa ke tasiri sosai a fagen siyasar Afirka.
A matsayinsa na mai ra'ayin gurguzu, ya yi barazana ga muradun kasashen yammacin duniya wadanda suke ganin manufofinsa a matsayin barazana ga tasirinsu a Afirka.
A 'yan shekarun nan, an sake farfado da gwagwarmayar neman ikon kasa a nahiyar, inda mutane iri daya ke taka wannan rawa yayin da aka dada samun wasu sabbin mutane a cikinsu.
Daga tutocin Rasha a Burkina Faso a yayin zanga-zangar nuna goyon baya ga gwamnatin mulkin sojin kasar na nuni da yanayin da ake ciki na maye gurbin tasirin wani kasar Turai da wani, wanda a zahiri ya sabawa tahirin abin da Sankara ya bayar.
Dole ne a fahimci tsarin mulkin mallaka na ''anti-imperialism'' a matsayin gwagwarmayar neman 'yancin kai, maimakon dogara kan wani bangare da ke iko na rabewar mulki a duniya.
Hakki ne da ya rataya akan wuyan shugabannin Burkina Faso su samar da wata hanya da jama'a za su jagoranci kafar gudanar da mulki.
Wanda tsarinsa ke biye da tarihi da kuma sanya al'umma a kan gaba.
Wani sabon Sankara
Kazalika, hakkin al'ummar Burkina Faso ne da daukacin 'yan Afirka su dauki kyawawan ra'ayoyi daga tarihin jarumtar Sankara su sanya su a gaba; don samar da sabbin hanyoyin gudanar da shugabanci nagari sabanin goyon bayan juyin mulkin soji da makauniyar fatar samun sabon Sankara.
Daga karshe dai, jarumtakarsa ba ya daya daga cikin wadannan sauye-sauye, inda aka watsar da tsofaffin dabaru wasu sababbi.
Mubarak Aliyu, manazarci ne kan harkokin siyasa da tsaro wanda ya fi kwarewa a yammacin Afirka da yankin Sahel
Togaciya: Ba dole ba ne ya zama ra'ayin marubucin ya yi daidai da ra'ayi da ka'idojin aikin jarida na TRT Afrika.