A lokaci guda kuma, mun yi 'matuƙar' fahimtar muhimmancin dariya da barkwanci da nishaɗi. Hoto: Reuters

Daga Dan Hammett

Ba zan iya ƙirga sau nawa aka tambaye mu ni da abokan aikina kan cewa, 'Me ya sa muke bincike a kan barkwanci?'

Amsa ta gaskiya kuma ta haƙiƙa da muke bayarwa ita ce, kawai lamarin na da daɗi. Waye ba zai so ya ji daɗin aikinsa ba?

A lokaci guda kuma, mun yi 'matuƙar' fahimtar muhimmancin dariya da barkwanci da nishaɗi.

A ko ina ana barkwanci yana da tasiri a kowane yanayi na rayuwa - ko dai ya kasance a matsayin wani makami na jajircewa ko yin adawa - ko a matsayin wata hanya ce ta nuna iko a kan mutanen da aka yi wa danniya, ko kuma nuna juriya game da wahalhalun rayuwa.

A fadin nahiyar Afirka, mun ga yadda ake gabatar da barkwanci, ake kuma yin sa ta hanyoyi da dama - yadda ake amfani da barkwanci da raha wajen inganta zaman lafiya a tsakanin al'ummomi da samar wa mutane wata hanya da shagala da wahalhalun da suke ciki, dayadda fahimtar wasu salon arkwancin ka iya janyo rikici (musamman a tsakanin ƙasashe da al'ummomi) da kuma yadda a wasu lokutan ma yakan janyo tashin hankali.

Tasirin barkwanci

Amma duk da haka, muhawara kan barkwanci da siyasa a Afirka sau da yawa suna rage raha zuwa lamari na dagiya - ko kuma, sau tari, lokacin tsayin daka da aka samu kadan ban da tunatar da 'yan kasa ikon ƙasa.

Muna tunani game da barkwanci na Afirka ta hanyoyi da yawa kuma a lokaci guda, kuma muna yin ƙoƙari don gane yadda abin dariya da kansa yake da tasiri. Wannan ba yana nufin cewa barkwanci na Afirka yana da kamanceceniya ko ya sha bambam ba.

Maimakon haka, barkwanci a Afirka yana da dogon tarihi da kuma yadda ake kallonsa a ma'auni daban-daban - tun daga salon barkwanci irin na Wawan Sarki, har zuwa dangantakar barkwanci tsakanin al'ummomi, har ta kai ga bayyanar yin wasan barkwanci a wuraren tarukan siyasa da kuma fina-finai.

As elsewhere, humour and politics are intertwined – in poking fun at political figures or events, as a tool for politicians to undermine their opponents, as a strategy for leaders to appear approachable and in-touch with communities, as a means for citizens to reflect on and cope in times of struggle, but also simply as a means of entertainment.

Kamar a sauran wurare, barkwanci da siyasa suna tafiya kafada da kafaɗa – wajen amfani da barkwanci don yin izgili a kan ƴan siyasa ko abubuwan da suka faru, a matsayin wani makami da ‘yan siyasa ke amfani da shi don yi wa abokan hamayyarsu yarfe.

Ko kuma a matsayin dabarar da shugabanni ke bi domin su zama masu kusanci da mu’amala da al’umma, ko a matsayin hanyar da ‘yan ƙasa za su yi tunani, kan da jurewa a lokutan gwagwarmaya, amma kuma a matsayin hanyar nishaɗi kawai.

A wata fassarar kuma, barkwanci da kansa yana iya yin 'aiki na siyasa' da yawa ta hanyoyin da za su iya zama na ci gaba, sau da yawa ta hanyar tattara muhimman abubuwan da suka faru a ƙananan lokuta.

A wasu lokutan, barkwanci hanya ce mai tasiri a cikin zamantakewa da siyasa wanda za a iya amfani da shi don shawo kan rarrabuwar kawuna a lamarin siyasa don bai wa mutane damar faɗin gaskiya ga masu mulki.

Jokes can be used to resist, maintain or promote social and political influence. Photo: Reuters

Wannan na iya kasancewa ta hanyar (yaɗa) hotunan shugabannin siyasa ta hanyoyi marasa daɗi ko kuma yin barkwanci game da gazawarsu da kura-kuransu.

Yadda barkwanci ke sauya salo

A lokaci guda, duk da haka, shugabannin siyasa na iya haɗa kai da masu wasan barkwanci ta hanyar gudanar da tarukan siyasa don neman goyon baya ga manufarsu.

Tabbas, yayin da masu barkwanci da ƴan wasan barkwanci za su iya samun ƴancin yin ba'a ga shugabannin siyasa a wasu ƙasashen Afirka, a wani wuri barkwaci na iya zama batun rayuwa da mutuwa.

A ’yan shekarun nan mun ga rahotannin sace-sacen ’yan wasan barkwanci, ’inda ake yin garkuwa da su, ana daure su, ana kashe su, ko a tilasta musu yin gudun hijira.

Wannan yana nuna matuƙar tasirin barkwanci da yadda zai iya jawo abubuwa da yawa marasa dadi.

A da can, Turawan mulkin mallaka sun yi amfani da doka don murƙushe barkwanci da izgili da cin mutuncin manyan mutane.

Ana sa ran ƙarshen zamanin mulkin mallaka zai ba da damar ƴancin siyasa da yawa - don haka barkwanci ya bunƙasa.

Kazalika, a lokuta da dama ba a ganin hakan, saboda yadda shuabannin a asashen da suka samu anci ke ci gaba da murƙushe masu barkwanci.

Kwanan nan ko da yake, lamarin yana ci gaba da sauyawa. Duk da yake ana samun kawar da kai daga wasu nau'ikan barkwanci na siyasa a ƙasashe daban-daban, ana ci gaba da tsanantawa masu barkwanci da masu zanen barkwanci da sauransu.

A yayin da ake ci gaba da samun sauye-sauyen siyasa a fadin nahiyar, shin an sami wani lokaci da barkwanci ya yi wa Afirka rana?

Za a iya cewa ana ganin hakan a yanzu inda masu wasan barkwanci ke shahara.

An kasance ana gudanar da nau'ukan barkwanci daban-daban a kowane lungu na nahiyar. Ni da abokan aikina Laura Martin da Izuu Nwankwo mun rubuta wani littafi da nufin ginawa da gane abin da ke wanzuwa kuma ya ci gaba ta hanyar ayyukan siyasa na barkwanci, ba tare da la’akari da yunƙurin goyan bayan gwamnati na tallafawa ko jurewa ko murkushe adawa ba.

Marubucin, Dan Hammett, Babban Malami ne a Sashen Ilimin Ƙasa a Jami'ar Sheffield ta Birtaniya, kuma Babban Jami'in Bincike, Sashen Ilimin Ƙasa da Nazarin Muhalli da Makamashi a Jami'ar Johannesburg ta Afirka ta Kudu.

Togaciya: Ra'ayoyin da marubuciyar ta bayyana ba dole ba ne ya kasance daidai da ra'ayi, da hange da nazari da kuma manufofin editan TRT Afrika ba.

TRT Afrika