Guevanis DOH
Gaya Habiba ta tuna abin da ya faru ranar 13 ga watan Afrilun 2021 kamar jiya ya auku.
Matukar razanar da wata abokiyar aikinta ta yi da kuma irin kalamanta a wancan lokacin inda ta kwalla wa shugabar makaranta kira cewa — "Gobara ta tashi!" — na cikin abubuwan da ba za ta taba mantawa ba.
Har yanzu tana ci gaba da takaicin yadda ta gaza ceto dalibai kanana 21 da suka rika ihu sakamakon wutar da take ci a inda suke.
Fiye da shekara biyu kenan bayan aukuwar wannan ibtila’i, amma ji take kamar yau lamarin ya faru.
"Muna cikin azuzuwa da misalin karfe hudu na yamma, yayin da maza suka tafi yin sallah a masallaci. Dalibai suna bibiyar darusan da aka koya musu bisa sanya idanun wasu malamai.
"Kwatsam sai muka ji iface-iface," a cewar Habiba yayin da take tuna gobarar da ta tashi a makarantar Pays Bays da ke Yamai, babban birnin kasar.
Gobarar ta mamaye azuzuwan da aka yi da zana cikin kasa da minti 10. Hayaki ya turnuke azuzuwan yadda babu wanda yake iya shiga domin ya yi yunkurin ceto daliban.
"Wani mutum ya yi yunkurin shiga ciki domin ya ceto daliban, amma ya shaki hayaki ya suma kafin ya isa ajin,” a cewar daraktar makarantun firamare, Habiba, a tattaunawarta da TRT Afrika.
"Gobarar ta zama wani bangare na rayuwarmu; ba za mu manta ba. Abin da yake ba da mamaki shi ne har yanzu ba mu san tushen irin wadannan gobarar ba."
Kawo yanzu ba a kammala binciken da gwamnati ta kaddamar kan silar gobarar ba, kamar dai yadda aka kaddamar da irin wannan bincike game da tashin gobara a wasu yankuna na kasar.
Yawan tashin gobara
A Jamhuriyar Nijar, azuzuwan da aka yi da zana suna yawan kamawa da wuta.
Yara akalla 50 ne suka rasu a irin wadannan gobarar cikin shekaru biyu da suka gabata kadai.
Ta baya-bayan nan ta faru ne a ranar 6 ga Faburairu a yankin Zinder na kudancin kasar, kimanin kilomita 1,000 daga Yamai babban birnin kasar.
‘Yan makaranta uku ne suka mutu a gobarar, abin da ya sake tayar da muhawara game da gina azuzuwan zana ko bukka a kasar.
A watan Nuwamban 2021, ‘yan firamare 26, ‘yan shekara biyar zuwa shekara shida, ne suka mutu a gobara da ta tashi a makarantarsu wadda aka gina da itace, da fallen kwano da kuma kara a jihar Maradi dake kudu.
Wannan ya faru ne watanni bakwai kacal bayan bala’in Pays Bas, inda galibin mutane 21 da lamarin ya rutsa da su, yara ne kanana ‘yan kasa da shekara biyar da haihuwa.
Ko shakka babu, akwai azuzuwan zana birjik a Nijar. Suna cike gibin matsalar karancin wuraren karatu a makarantu kamar makarantar Pays Bas, wadda ke da dalibai 1,250.
Kasancewar ana ci gaba da gina irin wadannan makarantu duk da atakin gwamnati na haramta su, wani abin kaico ne a bangaren ilimi na Nijar, domin matakin tamkar ba ya yi tasiri.
Kaddamar da fafutukar yaki ‘’hana samar da makarantun zana’’ da aka yi a watan Yulin bara, tamkar somin-tabi ne.
Malaman makarantu na kan gaba
Asusun Kula da Yara na Majalisar Dinkin Duniya, UNICEF, ya yi kiyasin cewa akwai azuzuwan zana kimanin 36,000 a Nijar.
Adadin na ci gaba da karuwa domin a duk shekara yara maza da mata fiye da 500,000 ne ke fara karatun firamare, abin da ke kara takura kayan aiki da ake da su wadanda dama ba su wadatar ba.
"Gobarar ta zama wani bangare na rayuwarmu; ba za mu manta ba. Abin da yake ba da mamaki shi ne har yanzu ba mu san tushen irin wadannan gobarar ba."
Wannan larura ta wajabta wa malaman makarantu zama a ankare a ko yaushe kan yiwuwar samun gobara.
Habiba da abokan aikinta a makarantar Pays Bas sun yi imanin cewa yanzu akwai ingantattun azuzuwa kuma masu karin matakan kiyayewa.
‘’Gaskiya bala’in ya yi mana illa. Alhamdulillahi, yanzu ba mu da azuzuwan zana. Asusun UNICEF ya taimaka mana muka gina wasu azuzuwan da yanzu ke daukar yara 439 ‘yan makarantar sakandare’’ a cewarta.
Bayan bala’in na watan Afirilun 2021, Habiba da abokan aikinta sun karaya, har suka yi tunanin barin aikinsu na koyarwa.
Ta ce ‘’kungiyoyi masu hada hannu da mu sun tallafa mana sosai, kuma sun shawarce mu kada mu tafi.
"Wayar da kai da kuma kwantar da hankali, sun taimaka kwarai. To amma har yau din nan, idan muka ci wata hayaniya da ba mu saba ji ba, mukan damu, kuma yaran kan firgita.
"A kullum muna ankare mussaman tun da makarantar babu katanga, kuma babu jami’an tsaro.’’
Gonda Houéla, daraktan nasiri a makarantar Pays Bas, na bukatar gwamnati ta tabbatar da makarantu a fadin kasar na bin tsarin na rashin azuzuwan zana.
Ya yi roko, yana mai cewa ‘’muna bukatar gwamnati ta cika alkawarinta na tabbatar da babu makaranzun zana, domin a kawo karshen irin wadannan hasarori da za a iya kauce masu a makarantu.’’
Rama Gouba, wata mahaifiya wadda ‘ya’yanta suka tsira a gobarar 2021, na da tafa ne tak. ‘’Dole ne gwamnati ta kare mana ‘ya’yanmu’’ a cewarta.
Samun ilimi a yanayi marar hatsari
Hukumar kula da makarantun nasiri da firamare ta fara bullo da jerin matakai na kawo karshen yawan gobara a makarantu.
A cewar darakta Abdouramane Adama Brah ‘’domin kawar da azuzuwan zana, ma’aikatar ilimi ta aiwatar da wani tsari na samar da wasu hanyoyin na daban masu dorewa, marasa tsada kuma wadanda suka kai matakin inganci ta fuskar kare muhalli da kuma samar da ilimi.’’
‘’Tare da taimakon gwamnati, muna fatan cika wannan alkawari. Ana kokarin ganin kowa da kowa ya samu ilimi.’’
To amma a ganin wasu bangarori masu ruwa da tsaki a sha’anin ilimi, gwamnatin ba ta da kyakkyawan tsari.
Mahamadou Moussa, babban sakataren kungiyar ALTEN mai fafutikar yaki da ci da gumin yara, ya yi imanin cewa ‘’ya kamata gwamnatin Nijar da sauran abokan hada gwiwarta su kara kokari.’’
Ya shaida wa TRT Afrika cewa ‘’kyakkyawar manufa ce ga gwamnati ta yi kokarin kawo karshen azuzuwan zana, to amma babu tsari ko daba a yadda ake tunkarar lamarin.
"Ana so a kawo karshen azuzuwan zana, amma yaushe? Yau ko gobe? Cikin shekaru biyar ko shekaru 10?
"Ya kamata gwamnati ta yi da gaske domin masu sha’awar zuba jari su ga an tanadar da shimfidadden tsari a kasa.’’
Ya kara da cewa ‘’idan gwmnati na son gina azuzuwa da kayan aiki masu kwari, muna so mu san nawa za a kasha, a shiyya-shiyya.’’
Kafin komai ya tabbata, a yanzu zabi daya ya rage ga malaman makarantu da iyayen yara da sauran masu ruwa da tsari a sha’anin ilimi matakin farko a Nijar: su rika sa ido domin tabbatar da tsaron lafiyar ‘ya’yansu.