Daga Johnson Kanamugire
Zai iya zama abun mamaki ga mutane da yawa, yadda bayan sama da shekaru biyu da kawo karshen rufe makarantu da cutar korona ta janyo, kasashen Afirka da dama suna kin karbar sakamakon karatuttukan da aka yi daga nesa.
Kamar yadda yake a wasu kasashen duniya, a Afirka ma jami'o'i da dama na gwamnati da masu zaman kansu sun rungumi wannan sabon tsari: Komawa ga karatu ta intanet daga gida.
Sauyin yanayin koyo da koyarwar ya kawo karshen wahalar samun damar yin karatun jami'a, yana bayar da dama ga mutanen da suke zaune a gida saboda dokar hana fita a duniya - su yi karatu a manyan makarantun da suke so.
Tsawon lokaci masu hali da sarari suke samun alfarmar ikon zuwa garuruwa da birane don yin karatuttuka a manyan makarantu.
Sai dai kuma, kadan daga cikin wadanda suka yi irin wannan karatu daga nesa ne suka san cewa ba fa a ko ina ne ake amincewa da irin sakamakon karatun da suka yi ba, da kuma irin tasirin da hakan zai yi a lokacin da suke kokarin neman ayyukan yi a yankunansu.
Da yawa sun tsinci kawunansu a yanayi na rashin jin dadi saboda yadda hukumomin da ke amincewa da takardun kammala makaranta suke shakku game da karatuttukan da aka yi ta yanar gizo daga nesa, inda suke kin amincewa da digiri irin wannan ballantana a samu aikin yi da shi.
A wajen mutane da dama, dambarwar na ci gaba har zuwa yau, kuma na nuni da babbar matsalar da ta addabi mutane da yawa, musamman matasan Afirka da suke fita kasashen da ba nasu ba don neman damarmakin ilimi don tallafawa jama'arsu.
Tsawon shekaru, wadanda suka kammala wadannan karatu na kasashen waje na ta fama da gwagwarmaya da wannan matsala. Annobar Covid-19 ta bayyana tsananin matsalar ne, kuma matsala ce da za ta shafi mutane da yawa.
Kusan shekara goma kenan tun bayan da Tarayyar Afirka, UNESCO da sauran kawayen hulda suka fara tuntubar juna, ba tare da wata nasara ba, suna neman gwamnatocin nahiyar da su amince da sakamakon karatun da aka yi a manyan makarantu.
A ranar 12 ga Disamban 2014 a Addis Ababa aka kaddamar da wani kudiri, amma sai a Disamban 2019 aka amince da shi shekaru biyar baya, inda kasashe goma suka sanya hannu.
Yadda kasashe da dama suke da tsarin tabbatar da inganci da samar da cancanta, abun yana zama kamar wani tsari na mayar da shi aikin bai daya da zai shigar da miliyoyin mutane da za su amfana da shi a yayin da suke neman ilimi a nahiyar.
Amma kuma, ba a samu wani cigaba ba tun wannan lokaci. Kawai 14 daga mambobin Tarayyar Afirka ne suka sanya hannu kan wannan doka. Yarjejeniyar ta samu karin kasashe biyu da suka amince da shi a shekaru biyun da suka gabata, Zambia da Cabo Verde a 2021 da 2022.
Idan har kasashe mambobin Tarayyar Afirka gaba daya suka amince da wannan doka, to sannan ne za a ga amincewa da manyan makarantun ko ina a dukkan sauran kasashen Afirka, ciki har da ma makarantun da ake koyo da koyarwa ta yanar gizo, wanda hakan zai baiwa mutane damar samun gurabe aiki.
Tafiyar wahainiyar da ake samu game da amincewar kasashe ga wannan tsari na nufin cewa har ma mutanen da suke kasashen da suka amince da dokar, na yin zaman jira na tsawon lokaci kafin s amfana da tsarin.
Hakan ta ci gaba da kasancewa duk da sakamakon zamantakewa da na tattalin arziki da ke biyo baya saboda cigaban rashin gasgatawar kasashe ga takardun mutum na manyan makarantu, kuma duk da kokarin da wasu kasashen ke yi na tabbatar da Yarjejeniyar AfCTA a ranar 1 ga Janairun 2021.
Wannan fage na kasuwanci na kasa da kasa da aka kirkira zai bukaci dabarun ayyuka don karfafa kasuwancin da zai kai ga samar da masana'antu, da kuma aminta da ilimin juna, inda masu ruwa da tsaki a fannin ilimi za su saukaka hanyar cimma wannan manufa, saboda yadda manyan makarantu suka zama masu muhimmanci wajen samar da kwararrun da ake bukata don kawo cigaba ga kasa.
Rashin gasgatawar har ya kai ga yin tasiri kan bukatar Afirka ta magance matsalar rashin amfana da damarmakin tattalin arziki.
Hakan ya hana zabin yin aiki ga miliyoyin matasa a tsallaken kasashensu, kuma hakan ya zama cikas ga musayar ilimi da dabaru a nahiyar, wanda duk sukda da tasiri wajen auna karfin ilimi.
Gwamnatoci a Afirka na bukatar zartar da wannan amincewa ta Addis Ababa, sannan su zartar da ita cikin gaggawa matukar kasar na son kamo sauran kasashen duniya, tare da magance bambancin inganci, kyawu da kwarewar ilimi da aka yi wa nahiyar tazara sosai.
Yadda korona ta yi kutse ga bangaren ilimi a duniya na nuni da yadda 'yan Afirka ke bukatar yanayin da zai bayar da dama gare su, su samu damarmakin ilimi mai zurfi ba tare da wani kaidi na yanki ba.
Biyan wannan bukata ya kamata ya zama a jerin batutuwan da 'yan siyasar Afirka za su sanya a gaba.
Johnson Kanamugire dan jarida ne a kasar rwanda da ya kware a bangaren labaran rayuwar jama'a.
Hattara: Ra'ayin da marubucin ya bayyana ba dole ba ne ya zo ɗaya da ra'ayin, hange da kuma manufofin tace labarai na TRT Afrika.