Ɗan takarar nan mai ra'ayin kawo sauyi Masoud Pezeshkian ya kai zagaye na biyu na zaɓen da ƙuri'u 10,415,991, inda mai tsatsauran ra'ayi na 'yan mazan jiya Saeed Jalili ya samu ƙuri'u 9,473,298.

Ɗan siyasar nan na Iran wanda asalin ɗan Turkiyya ne kuma mai ra'ayin kawo sauyi zai fafata a zagaye na biyu na zaben shugaban kasa a Iran, inda a zagayen farko na kada kuri'a aka kasa fitar da wanda ya yi nasara.

Zaɓe a ƙasar wadda mabiya aƙidar Shi'a ne suka fi yawa, ya zama tilas ne bayan mutuwar shugaban Iran Ebrahim Raisi a wani hatsarin helikwafta a ranar 19 ga watan Mayu.

A ranar 5 ga watan Yuli, 'yan Iran za su je rumfunan zaɓe domin gudanar da zaɓe a tsakanin Masoud Pezeshkian da Saeed Jalili - kusan kwanaki kaɗan bayan ƙasar ta fuskanci zaɓe wanda mutane da dama ba su fito ba, inda waɗanda suka fita ba su wuce kashi 40 cikin 100 ba.

Sakamakon yadda ƙasar ke fuskantar sauyi, tambaya ta farko ta take buƙatar amsa ita ce: wane irin tasiri sakamakon zaɓen na farko yake da shi ga siyasar Iran?

Shin har yanzu akwai batun sahihancin gwamnati?

Tsarin siyasar Iran yana da nufin samar da fassarar Shi'a game da Shari'ar Musulunci, tare da jaddada goyon bayan ubangiji da na mutane. Bangaren tsarin siyasar Iran yana cikin tafsirin Velayat-e Faqih na mazhabar Usuli ta Shi'anci ta manyan limanan shi'a 12.

Ra'ayin Velayat-e Faqih, wanda Khomeini ya tattara a lokacin da yake gudun hijira a Najaf, ya zama ginshikin ka'idojin kafuwar Iran bayan juyin juya halin 1979.

Wannan ra'ayin ya jawo sauyi matuƙa ga aƙidar malamai 12 na Shi'a.

Yayin da kalmar Velayat-e Faqih tana nufin hurumin hukunce-hukuncen faqih a cikin tsarin siyasa, haka nan kuma ta qunshi hurumin gudanar da mulki na faqih, da kuma matsayinsa na shugaban kasa.

Sabanin haka, bangaren siyasar faranta wa al'umma tana bayyana a zabukan wuraren irin su shugaban kasa, majalisa, da majalisar amintattu.

A cikin tsarin juyin juya hali na Iran, an gabatar da fitowar masu jefa kuri'a a zabuka a matsayin ma'auni na auna mizanin hallacin gwamnati. Hakika jami'an Iran ciki har da Jagoran Addini na Iran Ali Khamenei, suna amfani da adadin fitowar jama'a wurin zaɓe wajen tabbatar da halaccin tsarin siyasar jamhuriyar.

A cikin jawabin da ya yi a ranar 24 ga watan Yuni, Khamenei ya jaddada muhimmancin fitowar masu kada kuri'a a zaben shugaban kasa, yana mai mayar da martani kan cewa, halartar gagarumin taron zai kara daukaka darajar Iran.

Sai dai sakamakon zaben zagaye na farko na nuni da cewa burin Khamenei na samun fitowar jama'a da yawa bai kai ga samuwa ba.

Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta Iran ta bayar da rahoton cewa, adadin wadanda suka kada kuri'a a zagayen farko ya kai kashi 39.96 a duk fadin kasar, inda babban birnin Tehran ya kasance daya daga cikin mafi karancin waɗanda jama'a suka fito da kashi 23 cikin dari.

Hakan na nufin kashi 60 cikin 100 na masu kada kuri’a sun kaurace wa zaben, lamarin da ke nuni da cewa batun sahihancin gwamnati yana nan.

Tsirar da masu sassaucin ra'ayin mazan jiya

Sakamako na biyu muhimmi a zagayen farko na zaben shugaban kasar Iran shi ne kawar da masu sassaucin ra'ayin 'yan mazan jiya da kuma fifita 'yan takara masu tsatsauran ra'ayin mazan jiya.

A zagayen farko, Mohammad Bagher Ghalibaf ya wakilci masu sassaucin ra'ayin mazan jiya, yayin da Saeed Jalili ya wakilci masu ra'ayin rikau.

A cewar sanarwar da ma'aikatar harkokin cikin gidan Iran ta fitar na sakamakon zaben, dan takarar neman sauyi Masoud Pezeshkian ya tsallake zuwa zagaye na biyu da kuri'u miliyan 10,415,991, yayin da dan takarar masu ra'ayin rikau Saeed Jalili ya samu kuri'u 9,473,298.

Daga cikin wadannan akidun siyasa guda biyu, Jam'iyyar Juyin Juya Halin Musulunci tana wakiltar tsattsauran ra'ayin mazan jiya a siyasar Iran. Ta kunshi mabiya Muhammad Taqi Misbah Yazdi, daya daga cikin malaman Shi'a masu tsatsauran ra'ayi a Iran cikin shekaru arba'in da suka gabata.

Ana kuma kiransu 'yan 'Evangilika na Shi'a', inda ake ganin mambobinsu na daga cikin ƙungiyar Hojjatiyeh, ɗaya daga cikin ƙungiyoyin sirri a tarihin ƙasar. Masu sassaucin ra'ayi da masu ra'ayin kawo sauyi sun sha Allah wadai da su inda suke kiransu a matsayin Salafan Shi'a da kuma 'yan Taliban na Iran.

A aƙidar juyin juya hali na Iran, masu ra'ayin 'yan mazan jiya na wakilar ra'ayin Velayat-e Faqih a mazhabar Usuli ta limaman shi'a 12, inda masu ra'ayin kawo sauyi ke kira kan a tsaya kan tsarin zaɓe wadda ke magana kan ra'ayin.

Wannan ra'ayin, wanda kuma aka fi sani da Theory of Absolute Velayat-e Faqih, ya nuna cewa ya kamata ikon siyasa ya kasance tare da malaman addini, waɗanda ake ɗauka a matsayin magadan ruhaniya na limaman shi'a.

A cikin shi’ar Imamiyya, imani da limaman shi'a yana daya daga cikin shika-shikan imani. Wannan imani ya qunshi ra'ayin cewa matsayin limaman kamar annabci ne.

Masu ra'ayin riƙau na mazan jiya, a daya bangaren, sun amince da ra'ayin Makarantar Tafqiqi. Ma'ana Saeed Jalili a siyasance yana wakiltar kungiyar Paydari ne kuma a akida ya yi daidai da makarantar Tafqiqi.

Akwai Turkawa da dama a cikin 'yan Iran. Hukumomin Iran a 2014 sun tabbatar da cewa Farisawa da ke zaune a Iran ba su kai rabin adadin jama'ar Iran ba.

Fiye da rabin al'ummar kasar sun ƙunshi kabilun da ba Farisa ba ko kuma waɗanda ba sa jin harshen Farisa, inda ƙabilar Turkiyya ta kasance ta biyu mafi girma bayan ƙabilar Farisa.

A ziyarar da ya kai Turkiyya a shekarar 2014, Tsohon Ministan Harkokin Wajen Iran Ali Akbar Salehi ya bayyana cewa "kashi 40 na al'ummar Iran Turkawa ne".

Ya kara da cewa, akalla Turkawa miliyan 30 ne ke zaune a Iran, yana mai cewa wannan adadi na al'umma wani muhimmin al'amari ne da zai iya inganta dangantakar da ke tsakanin kasashen biyu.

Binciken da aka yi kan muhawara da yakin neman zabe a zagayen farko na zaben shugaban kasar Iran ya nuna cewa, a karon farko batun Turkiya a Iran ya yi fice a babban zaben kasar.

Ana iya danganta wannan shaharar ta musamman ga dan takarar neman sauyi Masoud Pezeshkian wanda asalin Baturke ne da kuma ba da muhimmanci ga bukatun kabilar Turkawa.

Dangane da sakamakon zagayen farko, Masoud Pezeshkian ya mayar da hankali ne a yankunan da ke da dumbin al'ummar Turkawa, inda ya bai wa wanda ya zo na biyu tazara sosai.

Goyon baya da Pezeshkian ke samu ba wai ya ta'allaƙa ne kawai kan ga Turkawan Azerbaijan ba da ke arewa maso yammacin Iran, amma har ga wasu Turkawan na Qashqai da ke tsakiyar Iran.

Ɗan takara mai rajin kawo sauyi da ke jan hankalin Ahlus Sunna na Iran

'Yan Ahlus Sunna sun kasance wani rukuni na musamman a cikin al'ummar Iran. A iƙirarin da shugabanninsu suka yi, su ne kashi 20 cikin 100 na al'ummar ƙasar.

Al'ummar Ahlus Sunna a ƙasar sun fi yawa a arewa maso yammacin ƙasar da kuma arewa maso gabas, musamman a lardunan Sistan da Baluchestan.

'Yan Ahlus Sunna na Iran sun yi zargin cewa suna fuskantar wariya haka kuma ana hana su 'yancinsu da dama da suke da shi a ƙasar wadda masu bin aƙidar limamai 12 na shi'a su ne suka fi yawa.

A lokacin yakin neman zabe, Pezeshkian ya ci gaba da yin tir da wannan wariya da ake nuna wa ‘yan Sunna tare da nuna adawa da rashin adalcin da gwamnatin Tehran ke yi musu a gidan talabijin na kasar.

Wannan matsayar da ya ɗauka ta ja hankalin 'yan Ahlus Sunna matuƙa a Iran inda har wasu suka soma nuna goyon baya a gare shi.

Wannan goyon bayan ya bayyana ƙarara a sakamakon zaben, inda Pezeshkian ya zo na ɗaya a lardin Sistan da Baluchestan da kuri'u 443,226.

A taƙaice, Saeed Jalili ya jagoranci yankuna masu yawan jama'ar Farisa, yayin da Masoud Pezeshkian ya yi rinjaye a yankunan da 'yan tsiraru suka fi zama.

A ranar 28 ga watan Yuni kashi 60 cikin 100 na masu jefa kuri'a sun kaurace wa kaɗa ƙuri'a a zaɓen da za a gudanar don zaɓen shugaban ƙasar Iran na tara, lamarin da ke nuni da cewa yunkurin kaurace wa zaɓen na da goyon bayan zamantakewa.

Akasin haka, sama da masu jefa ƙuri'a miliyan 10 sun goyi bayan ɗan takarar neman sauyi Pezeshkian, waɗanda ke nuna rashin gamsuwarsu da halin da ake ciki da kuma buƙatar yin garambawul a ƙasar.

Ganin cewa duk wani zabe da aka yi a Iran cikin shekaru arba'in da suka gabata ya haifar da sauye-sauyen siyasa masu ma'ana, da alama kasar na kan hanyar sake samun wani gagarumin sauyi.

Kuma ranar 5 ga watan Yuli na iya zama sabuwar duniya ga Iran da Iraniyawa.

TRT World