Daga Peter Nyanje
Bayan fiye da shekara 50 da galibin kasashen Afirka suka samu 'yancin kansu, har yanzu nahiyar ba kai labari a kididdigar alkaluman ci gaban kasashe a fannoni daban-daban duk da cewa nahiya ce da take duk wasu abubuwa da ke kawo ci gaba da arziki.
Za a iya alakanta hakan da abubuwa da dama ciki har da rashin kyakkyawan shugabanci.
Afirka ita ce nahiya ta biyu mafi yawan al'umma a duniya kuma tana da kasar noma mai yawa da kyau – da albarkatu kamar ruwa da dazuka da kuma albarkatun kasa.
Wadannan abubuwa su ne suke taimakawa sosai wajen samar da ci gaba da bunkasa da tattalin arzikin kasa.
Amma har yanzu nahiyar tana ci gaba da kasancewa a baya-baya a fannonin ci gaba da dama a duniya. Duk kasar da take so ta amfana daga yawan al'ummarta da albarkatunta, to wajibi ne shugabanninta sai sun samar da alkiblar da ta dace da kuma daukar matakai masu kyau. Watakila wadannan aka rasa a Afirka.
Rashin amfani da damarmaki
Shugabanni masu inganci suna da muhimmanci wajen samar da tsare-tsare dimokradiyya da kuma nasarori. Rashin kyakkyawan shugabanci shi ke dakike samun nasarori a fannin tattalin arziki.
Kasashen Afirka suna da kyakkyawan yanayin samar da lantarki daga hasken rana. Hoto: Reuters
Misali, matsalar wutar lantarkin da Afirka ta Kudu ke fuskanta a yanzu. Matsalar ba za ta kai munin haka ba idan da a ce kasar Ethiopia ta yi hanzari wajen gina dam din samar da wutar lantarkin da take yi a Kogin Nilu.
Saboda da yanzu Ethiopia ta fara samar wutar lantarki fiye da bukatarta kuma kila ta fara sayarwa Afirka ta Kudu wadda take cikin matsalar wuta ta hanyar babban layin wuta da ke gabashin Afirka.
Ya kamata a tuna cewa Tanzaniya ta hada babbar layin wutarta da na Kenya, wanda shi kuma aka hada da shi na kasar Ethiopia.
Saboda haka daga sabon Dam din Ethiopia mai suna Grand Ethiopian Renaissance Dam (GERD) za ai iya tura wuta zuwa Afirka ta Kudu, inda wutar za ta wuce ta Kenya da Tanzaniya da kuma Zambiya.
Hakazalika, matsalar da take fuskantar Afirka ta Kudu da ba za ta zama wata babbar matsala ba, idan da a ce shugabanni a Tanzaniya ba su yi watsi da shirin nan na 'Gas Economy' wanda aka faro lokacin mulkin tsohon Shugaba Jakaya Kikwete.
Shugaba Kikwete ya hau mulki ne a shekarar 2005 a tsakiyar wani gagarumin fari wanda ya durkusar da tashoshin samar da wutar lantarki daga ruwa wadanda suke samar da kaso 70 cikin 100 na wutar lantarki a Tanzaniya.
Daga nan ne sai ya fara tunanin magance matsalar kuma sai ya bijiro da wani shiri na amfani da dimbin iskar din da ke kudancin Tanzaniya wajen samar da makamashi.
An shirya hakan zai mayar da Tanzaniya daga kasa da ta dogara a kan samar da wutar lantarki daga dam din ruwa zuwa wadda ta dogara daga iskar gas.
Idan da shirin ya yiwu, da yanzu Tanzaniya ta iya samarwa kanta wutar lantarkin da take bukata har ma da kari, wadda za a iya sayarwa wasu kasashen Afirka kamar Afirka ta Kudu.
Sai dai za a iya cewa wannan shirin ya mutu murus a Tanzaniya.
Kashe kai
Idan kungiyar yankin Kudancin Afirka (SADC) da takwararta ta yankin Gabashin Afirka (EAC) sun kaddamar shirinsu na hada manyan rumbunansu na lantarki, da Afirka ta Kudu ta amfana daga wutar lantarkin Ethiopia.
Babban Dam din Lantarkin Ethiopia (GERD) zai bunkasa samar da wutar lantarki Hoto: AFP
Ko da a ce dam din Ethiopia GERD ya daina aiki, da a ce Tanzaniya ta ci gaba da shirinta na samar da lantarki daga iskar gas, da zuwa yanzu ta fara samar lantarki mai yawa daga wadda za ta iya sayarwa wasu kasashen.
Matakin da marigayi Shugaba John Magufuli na watsi da shirin Gas Economy ya jawo wa kasar asara.
Wata biyu da suka wuce, Tanzaniya ta fada matsalar rashin wutar lantarki saboda rashin wasu hanyoyin samar da wutar.
Da ba za a fuskanci wannan matsalar ba idan da gwamnati ta ci gaba da shirin samar da lantarki daga iskar gas kuma ta dogara da shi a matsayin babbar hanyar samar da makashi.
Gwamnatin Shugaba Kikwete ta ciyo bashin kudi don shinfida layukan iskar gas daga Mtwara zuwa Dar es Salaam saboda samar da iskar gas ga masana'antu da sauran masu bukata.
Kasar ta kashe kimanin dala biliyan 1.22 a kan wannan aiki. Amma gwamnatin da ta gaje shi sai ta yi watsi da aikin kuma ta zabi fara aikin gina tashar wutar lantarki daga ruwa ta Julius Nyerere Hydroelectric Dam a Kogin Rufiji duk da cewa masu kare muhalli da masana tattalin arziki sun bayyana damuwa.
Saboda haka aikin shinfida layukan iskar gas da ya cinye dala biliyan 1.22 yanzu yana aiki ne kaso 50 cikin 100.
An tsara shirin Gas Economy ya yi amfani da iskar gas don bunkasa ci gaba da tattalin arzikin kasar.
Har ila yau, akwai shirin mayar da iskar gas makamashin girkin da aka fi amfani da shi a Tanzaniya, wanda hakan zai sa a rage sare itatuwa a dazukan kasar wadanda masu samar gawayi suke yi. Amma haka aka jingine duka wadannan tsare-tsaren.
Akwai kuma tsare-tsaren samar da tashohin wutar lantarki daki-daki, wanda hakan zai sa Tanzaniya ta zama babbar mai samar da wutar lantarki a yankin.
An shirya za a samar da wani bangare na kudin aikin daga masu zuba jari ragowar kuma gwamnati ce ta samar, kuma an tsara sai samar da fiye da megawatts 10,000 idan aka kammala aikin.
Amma wadanda suka gaji Shugaba Kikwete sun jingine duka ayyukan da ya tsara na kara yawan wutar lantarkin da kasar ke samarwa.
Saboda haka Tanzaniya tana cikin kasashen da rashin wutar ke shafa duk
da cewa tana abubuwan da ake bukata don samar da adadin wutar lantarkin fiye da bukatarta.
Dam din Ethiopia na GERD ya jawo ce-ce-cu-ce a yankin Hoto: Reuters AFP
A yanzu haka, Tanzaniya tana samar da kasa da megawatts 1,300 na wutar lantarki ga jama'ar kasar fiye da miliyan 65.
A 'yan shekarun da suka wuce, ofishin babban mai kula da ayyukan gwamnati ya bayyana a wani rahoto na shekara-shekara cewa bashin da ake bin gwamnati daga ayyukan shinfida layukan iskar gas da aka yi watsi da shi ya ci gaba da jawo wa kasar asara.
Bunkasa kasuwanci
Tsohon Shugaban Tanzaniya Benjamin Mkapa, mutum ne da yake goyon bayan kasuwanci tsakanin kasashen Afirka.
Ya yi kokarin karfafa kasuwanci tsakanin kasashen Afirka, inda ya ce kasuwancin zai bunkasa tattalin arziki kasashe kuma kasashen za su amfana da juna idan aka kwatanta da abin da ke faruwa yanzu, inda suke sayar wa kasashen da suka ci gaba kayayyakin da ke bukatar sarrafawa don su sarrafa su.
Tashar jiragen ruwan Lagos (babban cibiyar kasuwancin Najeriya) tana taimakawa wajen kasuwancin kasa da kasa.Hoto: Reuters archive
Ya bayar da shawara a yi haka kuma ya kalubalenci masu goyon bayan kasashen Afirka su kulla yarjejeniyar kasuwanci da Kungiyar Tarayyar Turai wato Economic Partnership Agreement (EPA).
Mkapa ya damsu lokacin da nahiyar ta amince ta kafa yarjejeniyar kasuwanci mara shinge ta Africa Continent Free Trade Area (AfCTA), babban abin da yarjejeniyar ta gaba shi ne samar da kasuwaci kwaya tal ga kasashe 55 da kuma kungiyoyin raya tattalin arzikin yankuna da yawan jama'ar da ya kai biliyan 1.3 da kuma karfin tattalin arzikin da ya kai tiriliyan 3.4.
Yarjejeniyar AfCTA, wadda ta fara aiki a watan Mayun 2019, ana ganin ita ce za ta magance duk wata matsala da ke jawo cikas ga kasuwanci tsakanin kasashen Afirka. Amma kuma duk kasashe 54 daga cukin 55 sun sanya mata hannu a wannan wata, kasuwanci tsakanin kasashen yana ci gaba da yin kasa sosai.
Mujallar Africa Renewal ta Majalisar Dinkin Duniya – wadda take nazari kan tattalin arziki da al'amuran siyasa a nahiyar Afirka – ta wallafa wasu bayanai a watan Janairun da ya wuce, inda ta ce kaso 14.4 cikin 100 kacal na kayayyakin da kasashen Afirka ke fitarwa waje suke kasuwancinsu da junansu a cikin nahiyar Afirka.
Masana sun ce yarjejeniyar AfCTA za ta taimaka wa Afirka wajen bunkasa kasuwanci zuwa gaba, samar da yarjejeniyar abu ne daban da samar da yanayin da ya dace wajen tabbatar da aiki da ita tsakanin kasashen Afirka, shi ma kuma wani abu ne daban.
Har yanzu kasashen Afirka suna fuskantar kalubale wajen bunkass tattalin arzikinsu duk da dimbin albarkatun kasa da suke da su. Hoto: Reuters
Saboda yana da wuya ka ga Rwanda, wadda ta fara kera motoci masu aiki da lantarki, dogaro kan kayayyakin hada batira daga Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo saboda shugabannin kasashen biyu ba sa ganawa ido da ido duk da cewa kasashen biyu makwabta ne.
Amfana da arzikin juna
Aiki tare don cimma muradi guda shi ne babban abin da ya kamata kasashen Afirka su yi. Misali maimakon takaddama mai zafi kan wane ne ya fi dacewa ya yi amfani da ruwan Kogin Nilu, Ethiopia da Masar da sun duba yadda aka kafa Kungiyar Ci gaban Kogin Senegal (OMVS) a matsayin hanyar warware matsalarsu.
An kafa kungiyar OMVS ne a shekarar 1972 kuma hakan ya samar da mafita kan yadda a yi amfani da ruwan da kasashe biyu suke takaddama a kai, saboda tun daga lokacin ba a kara jin takaddama tsakanin Guinea da Mali da Senegal da kuma Mauritania kan Kogin Senegal ba.
Ya dace kasashen Afirka karbi yarjejeniyar AfCTA a matsayin mafita ga matsalolin kasuwancinsu. Duk wani yunkuri na ganin gwamnatocin Afirka sun bunkasa kasuwancinsu da sauran duniya, to a rika yin hakan bisa la'akari da yadda hakan zai taimaki takwarorinta kasashen Afirka.
Wannan ne zai sa kasashen Afirka amfana daga arzikin juna da kuma samar da ayyuka ta hanyar zuba jari wanda kasuwanci tsakanin kasashen Afirka ya samar.
Za a iya samar da kasuwanci tsakanin kasashen Afirka ta hanyar samar da hanyar cinikayya tsakanin manyan cibiyoyin kasuwanci.
Misali, Kungiyar EAC ta samar da hanyar cinikayya tsakaninta da Tanzaniya, ta tekun Atlantic ta Jamhuriyar Dimokradiyyar Kongo, wadda aka a baya-bayan nan ta shiga kungiyar.
Kafin wannan, kungiyar SADC ce ta fara karfafa hanyar kasuwanci tsakanin Kalahari da Walvis Bay a kasar Namibia da kuma Pretoria a Afirka ta Kudu a shekarar 1998 kafin a kara fadadawa zuwa Maputo (a Mozambique), wato kenan an samar da hanyar cinikayya tsakanin Tekun Atlantic da Tekun Indiya.
Marubucin wannan makalar, Peter Nyanje, mai sharhi kan al'amuran siyasa da tattalin arziki da ke zaune a birnin Dar es Salaam a kasar Tanzaniya.
Matashiya: Wannan ra'ayin marubucin ne kuma ba ra'ayin kafar yada labarai ta TRT ba ne.