Daga RAMZY BAROUD
“Muna godiya, sau dubu! Bakin cikinmu ya girma kana ya zama mutum. Kuma yanzu, dole ne mu yi yaƙi.''
Wannan ita ce baitin ƙarshe na wata gajeriyar waƙa ta fitaccen mawakin Falasdinu mai suna Samih Al-Qasim, mai taken, ''ya'yan Rafah.''
An sake waƙar Al-Qasim ne a shekarar 197, sama da shakaru biyar kafin Isra'ila ta fara mamaye Rafah, kololuwar nasarar sojinta da ake ganin ta samu - na kisan kare dangi- a Gaza, wanda ya soma a watan Oktobar 2023.
Waƙar ta bayyana manyan abubuwa guda biyu a tashin hankalin da Falasdinu ke ci gaba da fuskanta, tun daga bala'o'in 'Nakba' a 1948: Isra'ila, a matsayin wadda ke wakiltar yaki da kuma al'ummar Falasdinu a matsayin alamar sumud - wato tsayin daka.
Al-Qasim ya siffanta Isra’ila a matsayin “wadda ta tona hanyarta tare da raunata miliyoyin mutane,” kana “wadda tankokinta suka murkushe dukkan furannin wardi da ke cikin lambu,” sannan “wadda ta karya tagogi cikin dare” kana “ jiragenta ke jefa bama-bamai kan rayuwar kuruciya."
Na biyun kuma shi ne, an kwatanta Falasdinawa a matsayin ''ya'yan da ba su da tushe," waɗanda "ba su taɓa saƙa da ƙwanƙwasa a cikin bargo ba," ko "ba su taɓa tofa yawu kan gawarwaki ko fincike haƙoran zinarinsu ba."
Sakon Falasdinawa zuwa ga masu azabtar da su Isra'ila kuma shi ne, "Muna godiya, sau dubu! a yanzu bakin cikinmu ya girma ya zama mutum. Kuma yanzu, dole ne mu yi yaƙi.''
Radaɗin ciwo mai zafi
Na yi waiwaye kan wannan waƙar a wani tafiya da an yi mai cike da ruɗani zuwa Amsterdam don yin jawabi kan Nakba ga masu sauraro, waɗanda daga baya na fahimce cewa suna cikin baƙin ciki da tashin hankali da ɗimuwa, a wasu lokutan har ruɗewa suke yi bisa ga girman zaluncin isra'ila a Gaza.
Na yi ƙoƙari daidaita tunanina. Amma ta ya za ka iya magana kan radaɗin ciwon da ka ke ji wanɗa kuma yake dada girma, kamar wani batun siyasa ne kawai, "Yaki" tsakanin bangarori biyu, da ''maban-bantan'' labaru?
Shin kisan kiyashi ko ƙare dangi labari ne? ko kuma neman 'yanci rikici ne?
"Shin ko kun san cewa an kashe 'yan jarida Falasdinawa da yawa a Gaza cikin watanni bakwai fiye da wadanda suka mutu a yakin duniya na biyu dana Vietnam baki daya?"
Na rubuta wannan jumlar ce a cikin littafina don jaddada muhimmacin muryar Falasdinawa a cikin labarin falasdinu. Ina mai jan hankali kan kamar 'hadewa.''
Ga dukkan alamu dai sai Falasdinawa da dama sun mutu domin su iya gabatarwa kansu dalilan da ya su sa a bar su su yi magana.
"Ka ɗauki rabonka na jininmu-ka tafi." kamar yadda Mahmoud Darwish ya rubuta a cikin wata waƙarsa mai taken "Those Who Pass Between Fleeting Words."
Sama da mutane 35,000 ne suka mutu, sannan kusan mutum 80,000 sun jikkata yayin da mutum 11,000 da suka bace a ƙarƙashin baraguzan Gaza, shin a ƙarshe hakan bai isa waɗanda ke neman “rabon jininmu” su bar mu ba?
Wata tambaya mai mahimmanci ita ce: Shin wannan jini mai daraja ya isa a gyale mu, mu Falasdinawa, a cewar kalmomin Edward Said, "izinin ba da labari?"
Yawancin ƙoƙarinmu, a matsayinmu na Falasɗinawa masana, ƴan jarida, masana tarihi, masu fasaha, har ma da talakawa, ba a daukar sadaukarwa da wanzuwarmu a bakin komai ba.
Yarda da wanzuwar mu
Wanzuwarmu mu shi ne ginshikin komai. Shi ne abin da ake bukata don samun rayuwa mai mutunci. Idan babu hakan, a mafi yawan lokuta mutuwarmu da kuma shafemu za su ci gaba da faruwa ne cikin shuru.
Al’ummar ƙasashe da dama da aka zalunta sun halaka ne ta wannan hanyar, ba tare da barin komai a baya ba sai kururuwar danniya da radaɗin zafin da ba za a iya mantawa da su ba.
A matsayinmu na Falasdinawa, za mu ci gaba da yin tsayin dakar samun nasara - a gare mu, har ma da duk wasu mutane da ake zalunta a ko'ina a fadin duniya.
Isra'ila ta yi iya ƙoƙarinta don ta hana mu samun haƙƙoƙin - yarda da cewa muna wanzuwa. Hakan ya soma ne tun kafin Nakba.
Nakba ba wai kawai wani al'amari bane da ya kawo cikas ga wanzuwar kasar Falasdinu mai cike da tarihi- wajen maye gurbin wata ƙasa da wata, ta hanyar tashin hankali da nuna kabilanci.
An yi nuni kan wannan ɓangare na Nakba sau tari da dama a cikin littattafai da taswirori, da shirye-shiryen labarai da kuma shaidar waɗanda suka tsira daga "bala'in."
Amma akwai lamarin da ya wuce na Nakba wajen lalata ɗaruruwan ƙauyuka da kisan kiyashi ko korar mazaunansu.
Nakba ita ce hanyar da mabiya akidar Yaduwa ta Zionism suke amfani wajen sarrafa batutuwan da suka shafi tarihi.
Yahudawan sun kafa hujja da cewa "Falasdinu kasa ce da ba ta da al'umma" wannan shi ne jigon farko a kuskuren tunanin da ya mamayen Yahudawan duniya.
Duk abin da ya faru tun daga wancan lokacin, shi ne sakamakon makircin da ake ciki na adawa da tarihi.
Duk da haka shafe mu yana da matukar wuya kai tsaye ko a wuraren da ake iya gani. Yakin da ake yi kan al'adun Falasdinu da addini da abinci da kuma yare duk wani bangare ne na wannan rikici da Isara'ila ta shirya tun farko.
Yaƙin Gaza na nufin ya zama babi na ƙarshe na bala'i Nakba da ke gudana:
''Yanzu muna shirin kaddamar da Gaza Nakbar." a cewar Ministan harkokin Noma na Isra'ila Avi Dichter a watan Nuwamban bara. '' Gaza Nakba 2023. Haka za'a kare,'' in ji shi.
Bam din nukiliya ''abu ne mai yiwuwa," in ji ministan tarihi na Isra'ila Amichai Eliyahu yayin wata hira da aka yi da shi a ranar 5 ga Nuwamba.
The hateful, violent language continues.
Ana ci gaba da kalaman nuna ƙiyayya da tashin hankali.
Ba a gama ba
Sai dai Isra'ila ba za ta rubuta kalmomin ƙarshe na labarinmu ba, domin Isra'ila ba ita ce ke da ikon tsara tarihinmu ba, da kuma sarrafa harshenmu tare da hukunci kan makomar mutanenmu ba.
A yanzu ’Ya’yan talakawa, manoman da suka wuce, ‘yan gudun hijira na a yanzu, “sun girma” kuma suna mai da martanin yaki.
A yanzu al'ummar Falasdinu ba sa daga cikin tarihin da ya faru a baya, ko mutanen da ba da aka zalunta aka kuma shafe su da yi musu kisan kare dangi da mayar da su saniyar ware.
Juriyarsu yanzu ta zama abin almara, wanda ke nuna sauyin tarihi da ya kwashe sama da shekaru 75 ana nema.
Gaskiyar ta bayyana a fili domin duniya ta gani: yahudawa, da mummunan abubuwan da ke faruwa da tashin hankali da rabe-raben siyasa da talauci da al'ummar Falasdinu, matasa da masu iko suka haɗe a kai wajen yin tsayin daka .
Kwana ɗaya bayan na isa Amsterdam, ɗaruruwan ɗaliban jami'a suka fara hada zanga-zanga nuna goyon baya.
Alamominsu sun yi nuni da Nakba da sumud, sun kuma yi Allah wadai da wariyar launin fata ta yahudawa ke yi da kuma kisan kare dangi na Isra'ila.
Tutocin Falasdinawa sun kada ko'ina. Daliban sun yi ta rera waka da kururuwa ga Falasdinu da al'ummarta, kazalika sun yi ta rera wakokin dalibai a wasu sansanoni da dama a fadin yammacin kasashen duniya da dai sauransu.
A halin da ake ciki, labarai suna ta bayyana karuwar samun amincewar kasar Falasdinu. Wasu sun riga sun yi, wasu kuma sun kusa.
Sake maido da tarihin fatan Falasdinawa na samun 'yanci na da nasaba da tsayin dakarsu gaba daya. Ba tare da su ba, da Nakba ya fara kuma ya ƙare karkashin rubutun yahudawan Isra'ila.
A yanzu Nakba namu ne. Mun mallake shi, ba kawai a matsayin gwaninta na raɗaɗi da zafin ciwo da muka ji baki daya, amma a matsayin sake shari'ar adalci da aka dade da hana mu.
"Bakin ciki yanzu ya girma ya zama mutum. Yanzu kuma dole ne mu yi yaki," Al-Qasim ya rubuta.
Kuma, yanzu, dole ne mu yi nasara. A 'yancin da muka dade muna nema a ƙarshe.
Dr. Ramzy Baroud ɗan jarida ne, marubuci kuma Editan mujallar The Palestine Chronicle. Ya rubuta littattafai har guda shida. Littafinsa na baya-bayan nan, wanda ya yi haɗin gwiwa tare da Ilan Pappé, shine 'Our vision for Liberation:Engaged Palestinian Leaders and Intellectuals Speak Out'. Sauran littattafansa sun hada da ‘My Father was a Freedom Fighter’ da kuma ‘The Last Earth’. Baroud babban mai bincike ne a Cibiyar Musulunci da Harkokin Duniya ta (CIGA).
Togaciya: Ba dole ba ne ra'ayin marubucin ya yi daidai da ra'ayi ko ka'idojin aikin jarida na TRT Afrika ba.