Daga Ahmad Ibsais
A babi na baya bayan nan na kisan kiyashin da ke gudana a Gaza, ofishin harkokin wajen Amurka ya tabbatar da abin da tuni muka sani - cewa da gangan Isra'ila ke hana kayayyakin agaji da za a kai Gaza wucewa.
USAID da Hukumar Ƙidaya, Ƴan Gudun Hijira Da Ƴan Cirani a ƙarshen watan Afrilu sun tabbatar da labarin. Amma, a wani sauyi mai abin damuwa, Sakataren harkokin waje, Antony Blinken ya bayar da sheda a zauren Majalisar Dokoki ta ƙasa a watan Mayu, yana iƙirarin akasin hakan - cewa Isra'ila ba ta taɓa hana kai kayan agajin da Amurka ke goyon baya ba.
Wannan bayyanannen ruɗanin yana da hadafin kaucewa wata muhimmiyar dokar Amurka ce da ta wajabta dena bayar da taimakon soji ga ƙasashen da suka hana a kai agajin jinƙai.
A tsakiyar wannan batun akwai Sashe na 6201 na Dokar Bayar Da Agajin A Ƙasashen Waje, wacce ta haramta bayar da agajin soji ga kowacce ƙasa da ta kawo tarnaƙi ga kai agajin jin ƙai da Amurka ta ɗauki nauyi.
Ba a cika yin amfani da wannan dokar ba, amma ya kamata a ce an yi amfani da ita watanni da dama da suka wuce lokacin da kwararrun USAID da na Ma'aikatar Harkokin Ƙasashen Waje suka bayyana tarnaƙin da Isra'ila ke kawowa.
A cewar kundin bayanai na cikin gida na USAID, isra'ila ba ta juya akalar ayarin motoci dauke da muhimman kayayyaki kamar abinci da magunguna da kayayyakin tsafta ba ne kaɗai, har ma ma'aikatan jinƙai ta kai wa hari, ta jefa bamabamai a asibitoci sannan ta lalata muhimman abubuwan rayuwa a Gaza.
Ƙara Ƙaimi
A maimakon aiwatar da dokar, gwamnatin shugaban Amurka Joe Biden ta ƙara ƙaimi ne wajen bai wa Isra'ila tallafin soji, tana aikawa da sinƙin makamai ɗaya ko biyu kowacce rana tun da ta fara yaƙi a Gaza.
Wannan ya ƙunshi wani ƙunshin makamai da kuɗinsu suka kai dala biliyan $20 da aka amince da shi watan da ya gabata, a Augusta 2024. Isra'ila, wacce ta fi kowace ƙasa samun tallafin soji daga Amurka, ta yi amfani da waɗannan makaman wajen kai hare haren da suka yi sanadiyar kashe Falasɗinawa sama da dubu 41,000, galibinsu fararen hula.
Kwararrun Ma'aikatar Harkokin Ƙasashen Waje, da kuma jami'ai daga USAID, sun yi ta nanata kashedin cewa za a fassara abin da Isra'ila ke aikatawa a matsayin haramtacce a ƙarƙashin dokokin ƙasa da ƙasa kuma ya kamata a yi amfani da dokar ta Amurka a dakatar da tallafin sojin.
Amma bahasin da Blinken ya bayar a gaban majalisar dokokin ya ƙaryata waɗannan sakamakon binciken, yana iƙirarin cewa isra'ila tana bin ƙa'idojin da duniya ta yarda da su kan aikin jinƙai.
Fitowa ƙarara a ƙaryata abin da yake zahiri bai tsaya ga katange isra'ila daga girbar abin da ta shuka ba kaɗai, har ma da ba ta damar yin luguden bamabamai a Gaza da kuma ta'azzara yanayin ayyukan jin ƙai a can.
Zuwa watan Maris na 2024, motoci ɗauke da kayan agaji fiye da 930 suke maƙale a Masar, sun kasa shiga Gaza don samar da abincin da zai ceci rayuka saboda da jan ƙafa da gangan da Isra'ila ke yi.
Furucin na Blinken ba batu ba ne na aikin gudanarwa kawai. Wata dabara ce ta ci gaba da antaya makaman, yayin da kuma ake juya baya wa taɓarɓarewar aikin jinƙai da ke wakana a Gaza.
Duk da kiraye kiraye daga ƴan majalisar Demokarat da kungiyoyin kare haƙƙin bil adama na a dena aikawa da makaman, gwamnatin Biden ta yi kunnen uwar shegu kan keta dokokin Amurka da na ƙasa da ƙasa.
Halatta Makirci
Makircin da ake kan gudanarwa ya jawo a yi wata muhimmiyar tambaya: Me ya sa Amurka ta ƙyale hakan ya faru?
Dalili ɗaya shi ne ƙwaƙƙwaran ƙawancen siyasa da na soji tsakanin ƙasashen biyu, wanda a tarihance ya muhimmantar da tsaron Isra'ila sama da rayukan Falasɗinawa.
Ƙin ɗaukar mataki da gwamnatin Amurka ta yi a kan waɗannan sakamakon binciken na nuni da girman makircin da ke cikin tsarin da ya muhimmantar da ƙarfin soji a kan haƙƙin bil adama.
Jami'ai irin su jakadan Amurka a isra'ila Jack Lew ya yi ta nuna amincewarsa kan tabbacin da Tel Aviv ke bayarwa, duk da babbar hujjar gazawarsu ta kiyaye ƙa'idojin jinƙai.
Har adawa Lew ya yi da nuna damuwa da hana wucewar kayayyakin jin ƙai da Ma'aikatar Harkokin Ƙasashen Waje ta yi, yana bayyana isra'ila a matsayin wata mashahuriyar mai aikin jin ƙai - abin da za a ce ya yi banbaraƙwai idan aka yi la'akari da halaka ma'aikatan agaji da ɓarnar dukiya a Gaza.
Bugu da ƙari, taƙaddamar da Isra'ila ke yi kan cewa kayayyaki irin su kayan wanka da wanki da fitilu masu aiki da hasken rana da kuma kayan tace ruwan gishiri da Hamas za ta iya sarrafa su ta wata hanya, an yi amfani da su domin halatta wannan haramcin. Amma wannan tsaikon ya saɓawa doka sannan kuma yana ƙara ƙuncin da fararen hular Gaza ke ciki.
Ƙin ɗaukar mataki da gwamnatin Amurka ta yi a kan waɗannan sakamakon binciken na nuni da girman makircin da ke cikin tsarin da ya muhimmantar da ƙarfin soji a kan haƙƙin bil adama.
Ban da ƙin bin dokokin jin ƙan bil adama na ƙasa da ƙasa, akwai kuma mara wa ƙarerayin da Isra'ila baya don ta samu goyon bayan jama'a kan wannan kisan kiyashin.
Alal misali, Biden ya ce ya ga jirajirai babu kawuna bayan 7 ga watan Oktoba (bai gani ba), yayin da wasu ƴan siyasar Amurka ke yaɗa (ƙarairayi da iƙirarin da aka musanta) kan yi wa ɗimbin mata fyaɗe.
Waɗannan labaran sun fito ne daga wajen gwamnatin isra'ila don ta halatta kisan kiyashin nata, amma daga ƙarshe an tabbatar da dukkansu karya ne. Duk da haka Amurka ta ci gaba da goyon bayan irin wannan iƙirarin babu wata hujja, a ƙoƙarin nema wa Isra'ila goyon bayan jama'a.
Yayin da yanayi a Gaza ke ƙara dagulewa, dole Amurka ta yi nazarin rawar da take takawa a wannan ta'addacin. Dokar a bayyane take: Idan ƙasa ta hana shiga da kayayyakin jin ƙai, dole Amurka ta daina ba ta tallafin soji.
Amma a maimakon aiwatar da waɗannan halattattun kariyar, Amurka ta ci gaba da rura wutar rikicin.
Murɗe gaskiya da ƙarfin tsiya domin kauce wa matakin Shari'a yana nuni da rashin ɗaukar ran Falasɗinawa da wata kima sannan ya ƙara disashe kwarjinin Amurka a matsayin jagorar duniya wajen ayyukan jin ƙai.
Ranar Talata, Biden ya yi jawabi a Babban Taron Majalisar Ɗinkin Duniya, jawabinsa na farko a can tun da aka fara gwabza yaƙin a Gaza.
A jawabinsa, Biden har wa yau ya jaddada ƙaryar da Isra'ila ta shirga game da keta haddin mata da yawa ranar 7 ga watan Oktoba kuma ya ci gaba da nuna dacewar kisan kiyashin da ake kan yi saboda da ƴan isra'ila da aka yi garkuwa da su da har yanzu ba a gan su ba - kamar isra'ila ba ta kashe galibin waɗanda aka yi garkuwar da su ɗin ba, kuma ta ƙi amincewa da yarjeniyoyin tsagaita wuta da dama ba.
Biden har wa yau ya bayyana shugaban ƙasar Russia, Vladimir Putin a matsayin tarnaƙi ga zaman lafiya, duk da dai shi shugaban Amurkan shi ne ke ci gaba da bayar da kuɗaɗe da goyon bayan yi wa Falasɗinawa kisan ƙare dangi.
Duniya na kallo kuma tarihi zai bayyana inda Amurka ta kasance a wannan lokaci na rikici.
Idan Biden na son zaman lafiya kamar yadda ya ambata, dole ya tsame hannayensa daga jini sannan ya buƙaci a aiwatar da cikakken takunkumin makamai da dokar ƙasa da ƙasa a kan firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu.
Ba za mu taɓa manta goyon bayan kisan kiyashin da gwamnatin Biden ta yi ba, kuma shi Biden ɗin ba zai taɓa iya wanke kansa ba kan abin assha da ya aikata na kashe dubban fararen hula da ba su ji ba ba su gani ba da sunan mamaya.
Amurka ba za ta iya ci gaba da fakewa da daɗin bakin diflomasiyya ba. Akwai doka da za ta iya dakatar da irin wannan makircin, amma ba a amfani da ita.
Har sai idan gwamnatin Amurka ta fahimta kuma ta yi wani abu a kan rawar da ta taka a kisan kiyashin da Isra'ila ke yi a Gaza, za ta ci gaba da zama wadda aka haɗa makirci da ita wajen halaka al'umma gabaɗayanta.
Duniya na kallo kuma tarihi zai bayyana inda Amurka ta kasance a wannan lokaci na rikici.
Marubucin, Ahmad Ibsais Bafalasɗine ɗan Amurka na farko farko ne kuma ɗalibin karatun lauya wanda ya rubuta muƙalar State of Siege.
Togaciya: Ra'ayoyin da marubucin ya bayyana ba dole ba ne ya zo daidai da ra'ayi, fahimta da manufofin editan TRT Afrika ba.